Genesis 24

Genesis 24:1

Menene Ibrahim ya sa baransa, wanda ya fi daɗewa ya rantse cewa zai yi?

Ibrahim ya sa baransa, wanda ya fi daɗewa ya rantse cewa zai sama wa Ishaku mata daga dangin Ibrahim.

Genesis 24:5

Menene Ibrahim ya nace cewa kada bawansa yayi wa Ishaku?

Ibrahim ya nace cewa kada bawansa ya komar da Ishaku ƙasar da ya fito.

Genesis 24:12

Menene bawan Ibrahim ya roke Allah yayi domin ya nuna masa wane mace ne ya zaɓa wa Ishaku?

Bawan ya roka cewa matan da ya ce mata ta saukar da abin ɗiban ruwanta domin ya sha za ta haka ta kuma ba wa raƙumansa ma.

Genesis 24:15

Wane dangantaka ne Rebeka take wa Ibrahim?

Rebeka jikan Nahor ne, ɗan'uwan Ibrahim.

Genesis 24:17

Menene Rebeka ta yi a lokacin da bawan Ibrahim ya roka ruwan sha?

Rebeka ta ba wa bawan ruwan sha.

Genesis 24:19

Menene Rebeka ta faɗa bayan ta gama ba wa bawan ruwan sha?

Bayan Rebeka ta gama ba bawan ruwan sha, ta ce "Zan ɗebowa raƙumanka ma su sha har sai sun kammala sha."

Genesis 24:26

Menene bawan yayi a lokacin da ya ji cewa Rebeka dangin Ibrahim ne kuma cewa zai iya kwana a gidansu?

Bawan ya yi sujada ga Yahweh.

Genesis 24:31

Menene Laban yayi a lokacin da ya hadu da bawan Ibrahim?

Laban ya gayyaci bawan Ibrahim ya zauna a gidansa.

Genesis 24:33

Menene bawan Ibrahim ya nace yi kafin ya ci abinci?

Bawan Ibrahim ya nace faɗi dalilin zuwansa kafin cin abinci.

Genesis 24:39

Ya ya ne Ibrahim ya faɗa cewa Yahweh zai ba wa bawan nasara?

Ibrahim ya faɗa cewa Yahweh zai aika mala'ikansa ya kasance tare da shi ya kuma ba shi nasara bisa tafiyarsa.

Genesis 24:47

Menene bawan ya ba wa Rebeka a lokacin da ya ji cewa ita dangin Ibrahim ne?

Bawan Ibrahim ya ba wa Rebeka zoben zinariya a hancinta da ƙarau a damtsenta.

Genesis 24:50

Yaya ne Laban da Betuwel suka amsa bawan Ibrahim a lokacin da ya tambaye su abinda suke so su yi game da Rebeka?

Laban da Betuwel suka amsa cewa bawan ya ɗauke Rebeka ya tafi da ita, domin ta zama matar ɗan Ibrahim.

Genesis 24:52

Menene bawan Ibrahim yayi a lokacin da ya ji amsar daga Laban da Betuwel?

Bawan ya durkusa ƙasa ga Yahweh, ya kuma ba wa Rebeka ƙyautai da kuma ɗan'uwanta da mahaifiyarta.

Genesis 24:54

Sa'adda suka tashi da safe, menene ɗan'uwan Rebeka da mahaifiyarta suke son bawan yayi?

Sa'adda suka tashi da safe, sun so bawan Ibrahim yayi waɗansu 'yan kwanaki goma tukuna.

Genesis 24:56

Sa'adda bawan Ibrahim ya ce ya na so ya tafi nan da nan, menene Rahila ta ce ta na so ta yi?

Rahila ta ce ta na so ta tafi da bawan.

Genesis 24:59

Menene albarkar da iyalin Rebeka suka ba ta sa'adda ta tafi da bawan Ibrahim?

Iyalin Rebeka sun suka albarkace ta cewa za ta zama uwar dubun dubbai goma, kuma zuriyarta zasu mallaki ƙofar maƙiyansu.

Genesis 24:63

Menene Ishaku yake yi a lokacin da Rebeka ta isa gida?

Ishaku na nazari a waje.

Menene Rebeka ta yi a lokacin da ta gan Ishaku?

Sa'adda ta gan Ishaku, Rebeka ta diro daga kan raƙumin sai ta rufe kanta da lulluɓi.

Genesis 24:66

Menene Ishaku yayi bayan bawan Ibrahim ya zaiyana masa dukkan abubuwan da yayi?

Ishaku ya kawo ta rumfar mahaifiyarsa Saratu ya ɗauki Rebeka ta zama matarsa.