Genesis 25

Genesis 25:1

Menene Ibrahim yayi bayan matar Saratu ta mutu?

Ibrahim ya aure wata mata mai suna Ketura.

Genesis 25:5

Ya ya ne Ibrahim ya raɓa dukiyarsa?

Ibrahim ya ba da kyautai ga 'ya'yan ƙwaraƙwaransa, ya kuma mallaka duk abinda ya ke da shi ga Ishaku.

Genesis 25:7

Ibrahim ya yi shekaru nawa ne?

Ibrahim yayi rayuwa shekaru saba'in da biyar.

Genesis 25:9

Wanene ya bizne Ibrahim?

Ishaku da Isma'ila, suka bizne Ibrahim.

Genesis 25:17

Yaya ne 'ya'yan Isma'ila gomasha biyu suka yi zama da juna?

'Ya'yan Isma'ila gomasha biyu sun yi zaman tankiya da juna.

Genesis 25:21

Menene Ishaku yayi domin Rebeka ba ta da ɗa?

Ishaku ya yi addu'a ga Yahweh domin matarsa sabo da ba ta da ɗa, Yahweh kuma ya amsa addu'arsa, Rebeka matarsa kuma ta yi junabiyu.

Genesis 25:23

Menene Yahweh ya faɗa game da 'ya'ya biyu da suke fafitika a cikin Rebeka?

Yahweh ya faɗa cewa al'umma biyu ne a mahaifarta,ɗaya jama'ar za ta fi ɗayar ƙarfi, babban kuma zai bauta wa ƙaramin.

Genesis 25:24

Wanene aka haifa a farko, kuma ya yi kama da menene?

An haife Isuwa a farko, kuma ya fito da gargasa a ko'ina kamar tufafin gashi.

Wanene aka haifa na biyu, kuma menene yake yi sa'adda aka haife shi?

An haife Yakubu na biyu kuma ya fito hannuwansa na‌ riƙ‌e da diddigen Isuwa.

Genesis 25:27

Wane irin mutum ne Isuwa?

Isuwa shahararren mafarauci ne mai yawo a saura.

Wane irin mutum ne Yakubu?

Yakubu mai shiru-shiru ne, wanda ya kwashe lokacinsa cikin runfofi.

Wanene Ishaku ke ƙauna, kuma wanene Rebeka take ƙauna?

Ishaku na ƙaunar Isuwa kuma Rebeka ta na ƙaunar Yakubu.

Genesis 25:29

Menene wani suna na Isuwa?

Edom ne wani suna na Isuwa.

Genesis 25:31

Akan menene Yakubu ya roka a maimakon dage-dagen da Isuwa ya so ya ci domin ya na jin yinwa?

Yakubu ya roka Isuwa matsayin ɗan fari a maimakon dage-dagen.

Menene amsar Isuwa ga maganar Yakubu?

Isuwa yi rantsuwa ya kuma sayar da matsayin ɗan fari wa Yakubu.

Yaya ne Isuwa ya ɗauki matsayin ɗan farinsa a lokacin da ya amsa a wannan hanya ga tayin Yakubu?

Isuwa ya banzantar da matsayinsa na ɗan fari ga tayin Yakubu a haka.