Genesis 23

Genesis 23:1

Menene farkon abin da Ibrahim yayi a lokacin da Saratu ta mutu?

A lokacin da Saratu ta mutu, Ibrahim ya yi makoki da kuka dominta.

Genesis 23:3

Menene rokon da Ibrahim yayi wa 'ya'yan Het?

Ibrahim ya roka mallakar wurin maƙabarta.

Genesis 23:5

Yaya ne 'ya'yan Het suka amsa rokon Ibrahim?

'Ya'yan Het sun ba wa Ibrahim maƙabartar da ya zaɓa.

Genesis 23:10

A lokacin da Ibrahim ya roka Efron Bahitte maƙabarta a kogon, yaya ne Efron ya amsa?

Efron ya yarda ya ba wa Ibrahim kogon fili kusa da shi.

Genesis 23:12

Ya ya ne Ibrahim ya amsa wa Efron?

Ibrahim ya yarda zai biya kuɗin fili da kuma kogon.

Genesis 23:14

Ya ya ne Ifron ya amsa wa Ibrahim?

Ifron ya roki shekel ɗari huɗu na zinariya don fili da kuma kogon.

Yaya ne aka karasa magana sakanin Ibrahim da Ifron?

Ibrahim ya biya Ifron shekel ɗari huɗu na zinariya don filin.

Genesis 23:17

Menene aka kara a cikin sayan filin Ifron wanda ke Makfelah?

Filin da kogon da ke cikinsa, da duk itatuwan da ke cikin filin akan iyakarsa aka hada a sayar wa Ibrahim filin Ifron.

Genesis 23:19

Menene Ibrahim ya yi da kogon?

Sai Ibrahim ya binne Saratu a kogon.