Genesis 22

Genesis 22:1

Wane jarabawa ne Allah yayi wa Ibrahim?

Allah ya faɗa wa Ibrahim ya tafi ƙasar Moriyah ya kuma miƙa Ishaku a matsayin baiko na ƙonawa.

Ya ya ne Ibrahim ya amsa umarnin Allah?

Ibrahim ya tashi da asuba ya kama hanyarsa zuwa inda Allah ya faɗa masa.

Genesis 22:4

Menene Ibrahim ya faɗa wa samarinsa biyu cewa shi da Ishaku zasu je su yi?

Ibrahim ya faɗa wa samarinsa biyu cewa shi da Ishaku zasu je su yi sujada sai su kuma dawo

Genesis 22:7

Wane tambaya ne Ishaku ya yi wa Ibrahim sa'adda suke tafiya tare?

Ishaku ya tambaye Ibrahim cewa, "Ina ɗan ragon baikon ƙonawa?"

Ya ya ne Ibrahim ya amsa tambayar Ishaku?

Ibrahim ya faɗa cewa Allah da kansa zai tanada ɗan rago domin baikon ƙonawa.

Genesis 22:9

Sa'adda suka kai wurin, menene Ibrahim ya shirya a matsayin hadayan kuma yaya ne ya yi ta?

Ibrahim ya shirya Ishaku a matsayin hadaya ta ɗora shi akan bagadin bisa itacen.

Genesis 22:11

Sa'adda Ibrahim ya ɗauke wuka a hannunsa, menene mala'ikar Yahweh ya faɗa masa?

Mala'ikar Yahweh ya ce wa Ibrahim kada ya cutar da Ishaku.

Menene mala'ikar ya ce ya sani game da Ibrahim?

Mala'ikar ya faɗa cewa ya san Ibrahim na tsoron Allah

Genesis 22:13

Menene Allah ya tanada wa Ibrahim don hadayar ƙonawa?

Akwai ɗan ragon da an kama a cikin jeji a bayan Ibrahim wanda ya yi amfani don hadayar ƙonawa.

Menene Ibrahim ya kira wurin hadayar ƙonawa?

Ibrahim ya kira wurin "Yahweh zai tanada."

Genesis 22:15

Menene dalilin da mala'ikar Yahweh ya bayar don albarkace Ibrahim?

Mala'ikar Yahweh ya faɗa cewa zai albarkace Ibrahim domin bai hana ɗan ɗansa.

Genesis 22:18

Ta wurin wanene kuma don menene al'umman duniya za su sami albarka?

Ta wurin hadayar Ibrahim, dukka al'umman duniya za su sami albarka domin Ibrahim yayi biyayya da muryar mala'ikar Yahweh.