Sura 34

1 Sai Dinah, ɗiyar Liya wadda ta haifawa Yakubu, ta fita ta tafi wurin 'yanmatan ƙasar. 2 Shekem ɗan Hamo Bahibiye, yariman ƙasar, ya ganta ya kuma cafke ta, ya ɓata ta, ya kuma kwana da ita. 3 Ya shaƙu da Dinah, ɗiyar Yakubu. Ya ƙaunaci yarinyar, ya kuma yi mata magana mai taushi. 4 Shekem ya yi magana da mahaifinsa, cewa, "Ka samo mani wannan yarinyar a matsayin mata." 5 Yanzu Yakubu ya ji cewa ya lalata ɗiyarsa Dina. 'Ya'yansa kuma na tare da dabbobinsa a saura, sai Yakubu ya kame bakinsa har sai da su ka zo. 6 Hamo mahaifin Shekem ya tafi wurin Yakubu domin ya yi magana da shi. 7 'Ya'yan Yakubu suka dawo daga saura sa'ad da suka ji batun al'amarin. Mutanen ransu ya ɓaci. Suka fusata sosai saboda ya kunyatar da Isra'ila ta wurin tilasta kansa bisa ɗiyar Yakubu, domin bai kamata a aiwatar da irin haka ba. 8 Hamo ya yi magana da shi, cewa, "‌Ɗana Shekem na ƙaunar ɗiyarka. Ina roƙon ka. ka bayar da ita a gare shi a matsayin mata. 9 Ku yi auratayya da mu, ku bayar da 'ya'yanku mata a gare mu, ku kuma ɗauki 'ya'yanmu mata domin kanku. 10 Zaku zauna tare da mu, za a buɗe ƙasar kuma a gare ku domin ku zauna ku kuma yi sana'a a ciki, ku kuma mallaki kaddarori." 11 Shekem yace wa mahaifinta da 'yan'uwanta maza, "Bari in sami tagomashi a idanunku, duk kuma abin da kuka ce mani zan bayar. 12 Ku tambaye ni komai yawan sadakin da kyautar da kuke so, kuma zan bayar da duk abin da kuka ce, amma dai ku bani yarinyar a matsayin mata." 13 'Ya'yan Yakubu suka amsa wa Shekem da Hamo mahaifinsa tare da zamba, saboda Shekem ya ɓata Dina 'yar'uwarsu. 14 Suka ce masu, "Ba za mu iya yin wannan abu ba, mu bayar da 'yar'uwarmu ga duk wani wanda ba shi da kaciya; domin zai zama abin kunya a gare mu. 15 Sai dai a kan wannan matakin kaɗai za mu yarda da ku: Idan zaku zama masu kaciya kamar mu, idan kowanne namiji a cikin ku an yi masa kaciya. 16 Daga nan ne za mu bayar da 'ya'yanmu mata a gare ku, mu kuma zamu ɗauki 'ya'yanku mata a gare mu, mu kuma zauna daku mu zama mutane ɗaya. 17 Amma idan baku saurare mu ba kuka zama masu kaciya, daga nan zamu ɗauki 'yar'uwarmu kuma za mu tashi." 18 Maganganunsu suka gamshi Hamo da ɗansa Shekem. 19 Saurayin bai ɓata lokaci ba wurin yin abin da suka ce, saboda yana jin daɗin ɗiyar Yakubu, saboda kuma shi ne taliki mafi daraja a dukkan gidan mahaifinsa. 20 Hamo da ɗansa Shekem suka tafi ƙofar birninsu suka kuma yi magana da mutanen birninsu, cewa, 21 "Mutanen nan suna zaman salama da mu, bari su zauna cikin ƙasar su kuma yi sana'a a ciki domin, tabbas, ƙasar na da isasshen girma domin su. Bari mu ɗauki 'ya'yansu mata a matsayin matayen aure, bari kuma mu bayar da 'ya'yanmu mata a gare su. 22 A wannan matakin kaɗai mutanen za su yarda su zauna da mu kuma mu zama mutane ɗaya. Idan a ka yi wa kowanne namiji a cikin mu kaciya, kamar yarda suke da kaciya. 23 Ba dukkan dabbobinsu da kaddarorinsu - dukkan dabbobinsu zasu zama namu ba? Don haka mu yarda da su, zasu kuma zauna a cikinmu." 24 Dukkan mutanen birnin suka saurari Hamo da Shekem, ɗansa. Kowanne namiji a ka yi masa kaciya. 25 A rana ta uku, sa'ad da suke cikin zafi tukuna, 'ya'yan Yakubu biyu (Simiyon da Lebi 'yan'uwan Dina), kowannen su ya ɗauki takobinsa suka kuma kai hari ga birnin dake da tabbacin tsaro, suka kuma kashe dukkan mazajen. 26 Suka kashe Hamo da ɗansa Shekem ta kaifin takobi. Suka ɗauke Dina daga gidan Shekem suka yi tafiyar su. 27 Sauran 'ya'yan Yakubu suka zo wurin gawawwakin suka washe birnin, saboda mutanen sun ɓata 'yar'uwarsu. 28 Suka ɗauki garkunan tumakinsu dana awaki, da garkunan shanunsu, da jakkansu, da duk wani abu dake cikin birnin da gonakin dake kewaye tare da 29 dukkan dukiyarsu. Dukkan 'ya'yayensu da matayensu, suka kame. Suka ma ɗauke kowanne abu dake cikin gidajen. 30 Yakubu ya cewa Simiyon da Lebi, "Kun kawo mani matsala, domin kun sa in yi ɗoyi ga mazaunan ƙasar, da Kan'aniyawa da Feriziyawa. Ni kima ne a lissafi. Idan suka tattara kansu tare gãba da ni, su kuma kawo ma ni hari, daga nan zan hallaka, ni da gidana." 31 Amma Simiyon da Lebi suka ce, "Ya kamata Shekem ya yi da 'yar'uwarmu kamar karuwa?"