Genesis 48

Genesis 48:1

Wane sako ne Yosef ya ji game da mahaifinsa kuma menene yayi?

Yosef ya ji cewa mahaifinsa bai da lafiya sai ya ɗauki 'ya'yansa maza biyu tare da shi.

Genesis 48:3

Wane alkawari ne daga Allah Yakubu ya tunawa Yosef?

Yakubu ya tuna cewa Allah ya yi masa alkawari cewa zai hayayyafa ya kuma ruɓanɓanya, za a kuma maida shi taron al'ummai, kuma za a bayar da wannan ƙasar ga zuriyarsa a matsayin madawwamiyar mallaka.

Genesis 48:5

Yaya ne Yakubu ya ce zai duba 'ya'ya biyu na Yosef a gadon?

Yakubu ya faɗa cewa zai ɗauke 'ya'ya biyun Yosef a matsayin nashi.

Genesis 48:8

Don menene Isra'ila bai iya gane 'ya'ya biyu na Yosef ba?

Isra'ila bai iya gane 'ya'yan Yosef ba domin idanunsa na kasawa saboda shekarunsa.

Genesis 48:14

Wanene ɗan fãrin 'ya'yan Yosef?

Manasse ne ɗan fãrin Yosef.

Akan wanene Isra'ila ya miƙa hannunsa na dama, kuma akan wanene ya miƙa hannunsa na hagu?

Isra'ila ya miƙa hannunsa na dama bisa kan Ifraimu, hannun hagunsa kuma bisa kan Manasse.

Genesis 48:17

Don menene Yosef ya so ya canza inda hannun Isra'ila yake?

Yosef ya so hannun daman Isra'ila ya zauna bisa kan Manasse domin shi ne ɗan fãri?

Genesis 48:19

Don menene Isra'ila ya ƙi canza inda hannunsa yake akan 'ya'yan Yosef?

Isra'ila ya ƙi domin ƙaramin zai fi babban.

Wane albarka ne Isra'ila ya ce mutanensa zasu furta?

Isra'ila ya ce mutanensa zasu furta albarkan, "Bari Allah ya mai da ku kamar Ifraimu kamar kuma Manasse."

Genesis 48:21

Menene Isra'ila ya ce zai faru da Yosef?

Isra'ila ya faɗa cewa za a maida Yosef zuwa ƙasar ubannunsa.