Genesis 47

Genesis 47:3

Menene 'yan'uwan Yosef guda biyar suka faɗa wa Fir'auna cewa sana'arsu?

'Yan'uwan Yosef guda biyar sun faɗa wa Fir'auna cewa su makiyaya ne.

Wane irin mazauni ne 'yan'uwan suka ce suke a ƙasar Masar?

'Yan'uwan sun faɗa cewa suv zo ɗan zama ne a ƙasar Masar.

Genesis 47:5

Menene Fir'auna ya gaya wa Yosef yayi da iyalinsa?

Fir'auna ya ce wa Yosef ya zaunar da iyalinsa a lardi mafi kyau, ƙasar Goshen.

Genesis 47:7

Menene Yakubu yayi wa Fir'auna sa'adda ya hadu da shi da kuma sa'adda ya fita daga gabansa?

Yakubu ya albarkaci Fir'auna sa'adda ya hadu da shi da kuma sa'adda ya kuma fita daga gabansa.

Menene shekarun Yakubu a lokacin da ya hadu da Fir'auna?

Yakubu yayi rayuwa ɗari da talatin.

Yaya ne kwatancin tsawon rayuwar Yakubu da kakanninsa?

Yakubu ya ce shekarun rayuwarsa kima ne kuma cike da zafi.

Genesis 47:13

Menene Yosef ya iya yi ta wurin sayar da hatsi?

Yosef ya tattara dukkan kuɗaɗen da ke ƙasar Masar da ƙasar Kan'ana.

Genesis 47:15

Menene Yosef ya iya yi ta wurin canjin abinci da Masarawa?

Yosef ya ba su abinci misanya domin garkunan tumakin Masarawa.

Genesis 47:18

Bayan da aka ba Fir'auna dukka kuɗaɗen da garkunansu a musanya domin abinci, menene mutanen Masar sun mika masa a maimakon abinci?

Mutanen Masar sun mika wa Fir'auna ƙasarsu da kuma kansu a matsayin baya a musanya domin abinci.

Genesis 47:23

Wane sashin duka girbin ne Yosef ya bukaci a ba wa Fir'auna?

Yosef ya bukaci kaso biyar ga Fir'auna.

Genesis 47:27

A wane hanyoyi ne mutanen Isra'ila suka ci nasar a ƙasar Masar?

Mutanen Isra'ila sun sami mallakar ƙasar Masar, kuma sun hayayyafa suka ruɓanɓanya sosai.

A wane shekara ne Yakubu ya mutu?

Yakubu ya mutu a shakara ɗari da arba'in da bakwai.

Genesis 47:29

Menene Isra'ila ya faɗa wa Yosef ya rantse cewa zai yi?

Isra'ila ya faɗa wa Yosef ya rantse cewa zai bizne shi a maƙabartar kakanninsa.