Genesis 49

Genesis 49:1

Don wane dalili ne Yakubu ya tara 'ya'yansu tare?

Yakubu ya kirawo 'ya'yansa maza domin ya gaya masu abin da zai faru da su da zuriyarsu nan gaba.

Genesis 49:3

Menene hali mai kyau da Ruben yake da shi?

Ruben ya fice wajen jamali da iko.

Don menene Ruben ba zai zama da muhimmanci ba, ko dashike shi ne ɗan fãri?

Ruben ba zai zama da muhimmanci ba domin ya hau bisa gadon mahaifinsa.

Genesis 49:7

Menene Yakubu ya la'anta game da Simiyon da Lebi?

Yakubu ya la'anta zafin fushin Simiyon da Lebi.

Genesis 49:8

Menene Yakubu ya ce sauran 'ya'ya mazan zasu yi a gaban Yahuda?

Yakubu ya ce sauran 'ya'ya mazan zasu rusuna a gaban Yahuda.

Genesis 49:10

Wane alkawari ne aka yi wa Yahuda nan gaba?

An yi wa Yahuda alkawarin cewa sandan sarauta ba za ta rabu da shi ba, kuma al'ummai za su yi masa biyayya.

Genesis 49:13

Ina ne Yakubu ya ce zuriyar Zebulun zasu zauna?

Yakubu ya ce zuriyar Zebulun zasu zauna a gaɓar teku.

Genesis 49:16

Wane dabba ne Yakubu ya ce Dan zai zama kaman?

Yakubu ya ce Dan zai zama kamar maciji a gefen hanya.

Genesis 49:19

Akan menene Yakubu ya ce za a san Asha?

Yakubu ya ce za a san Asha ta wurin bayar da girke-girken sarauta.

Genesis 49:22

Wane irin itace ne Yakubu ya ce Yosef zai zama kaman?

Yakubu ya ce Yosef zai zama kamar itace mai bayar da 'ya'ya dake gefen ƙorama wanda rassansa ke hawan katanga.

Genesis 49:24

Wanene Yakubu ya ce zai riƙe bakan Yosef da kuma hannayensa da kyau?

Yakubu ya ce hannayen Mai Iko na Yakubu, Dutsen Isra'ila zai zai riƙe bakan Yosef da kuma hannayensa da kyau.

Genesis 49:31

Wanene aka bizne a inda Yakubu ya so a bizne shi?

an riga an bizne Ibrahim, Saratu, Ishaku, Rebekka, da kuma Liya.

Menene Yakubu yayi bayan da ya bada albarku da kuma umarnensa ga 'ya'yan shi?

Yakubu ya ja lumfashinsa na ƙarshe, sai ya tafi wurin mutanensa.