Genesis 36

Genesis 36:1

Amma wane suna ne akae kiran zuriyar Isuwa kuma?

Ana kiran zuriyar Isuwa Edom.

Daga ina ne Isuwa ya sami matarsa?

Esuwa ya ɗauki matayensa daga Kan'aniyawa.

Genesis 36:6

Don menene Isuwa ya tafi daga ɗan'uwansa Yakubu?

Isuwa yayi haka saboda mallakarsu ta yi yawan da ba za su iya zama tare ba. ‌Ƙasar da su ka zauna ba za ta iya ɗaukar su ba saboda yawan dabbobinsu.

Ina ne Isuwa ya zauna?

Isuwa ya zauna a ƙasar tudu ta Seyir.

Genesis 36:9

Menene sunar ɗan da Timna ta haifa, ƙwarƙwarar Elifaz, ɗan Esuwa, ta fari?

Sunar ɗan da Timna ta haifa shi ne Amalek.

Genesis 36:20

Wanene mahaifin mazaunan ƙasar da Edom ya zauna?

Seyir bahoritiye ne mahaifin mazauna ƙasar da Edom ya zauna.

Genesis 36:31

Menene mutanen Edom suke da shi kafin Isra'ila ta ɗauke su?

Mutanen Edom suna da sarakunan da suka yi mulki kafin wani sarki ya yi mulki a bisa Isra'ilawa

Genesis 36:40

Wanene mahaifin Edomawa?

Esuwa ne mahaifin Edomawa.