Genesis 35

Genesis 35:1

Menene Allah ya faɗa wa Yakubu ya je yayi?

Allah ya ce wa Yakubu ya tafi Betel ya je ya gina masa bagadi.

Menene Yakubu ya ce wa mutanen gidansu yi?

Yakubu ya fada masu cewa su fitar da bãƙin alloli da ke a tsakaninsu, su tsarkake kansu, su kuma canza suturarsu.

Genesis 35:4

Sa'adda suke tafiya, don menene mutanen biranen dake kewaye da Yakubu da iyalinsa basu runtume su ba?

Mutanen biranen dake kewaye dasu basu runtume su ba domin suna tsoron Allah.

Genesis 35:6

Don menene Yakubu ya kira wurin da suka isa "Elbetel"?

Yakubu ya kira wurin da suka isa "Elbetel" domin wurin ne Allah ya bayyana kansa ga Yakubu a lokacin da yake gudu daga ɗan'uwansa.

Genesis 35:9

Wane sabon suna ne Allah ya ba wa Yakubu?

Allah ya ba wa Yakubu sabon suna Isra'ila.

Genesis 35:11

Wane alkawari ne Allah ya tabbatar wa Yakubu?

Allah ya tabbatar da alkawarin cewa Yakubu zai zama ƙungiyar ƙasashe kuma sarakuna zasu kasance cikin zuriyarsa, kuma ‌ƙasar da ya yi alkawari ga Ibrahim da Ishaku, zai ba shi.

Genesis 35:16

Menene ya faru da Rahila a lokacin naƙudanta da Benyamin?

Rahila ta mutu a lokacin naƙudanta da Benyamin.

Genesis 35:21

Isra'ila ya ji game da wane abu ne da Ruben yayi?

Isra'ila ya ji cewa Ruben ya kwana da Bilha ƙwarƙwarar sa.

'Ya'ya maza nawa ne Yakubu yake da shi?

Yakubu na da 'ya'ya maza sha biyu.

Genesis 35:23

Wane 'ya'ya maza ne na Yakubu Rahila ta haifa?

Ya'yansa maza daga Rahila sune Yosef da Benyamin.

Genesis 35:28

Ishaku ya yi rayuwa shekaru nawa ne?

Ishaku ya rayu shekaru ɗari da tamanin.

Wanene ya bizne Ishaku?

Esuwa da Yakubu, 'ya'yansa, suka bizne shi.