Genesis 37

Genesis 37:1

Ina ne Yakubu ya zauna?

Yakubu ya zauna ƙasar Kan'ana.

Menene Yosef ya kawo wa mahaifinsa Yakubu sa'adda yake kiwon tumakai da 'yan'uwansa?

Yosef yana kawo labarai marasa daɗi game da su wurin mahaifinsu.

Genesis 37:3

Yaya ne Isra'ila ya nuna cewa yana ƙaunar Yosef fiye da sauran 'ya'yan?

Isra'ila yayi wa Yosef wata riga mai kyau.

Menene 'yan'uwan Yosef suke tunani game da shi?

'Yan'uwan Yosef sun ƙi jininsa kuma ba su maganar alheri da shi.

Genesis 37:7

Menene Yosef ya gani a mafarkinsa na farko?

Yosef ya gan daminsa ya tashi ya kuma tsaya a tsaye, dammunan 'yan'uwansa kuma suka zo a kewaye suka rusuna wa daminsa.

Menene 'yan'uwan Yosef suka yi tunani game shi bayan da ya faɗa masu game da mafarkin?

'Yan'uwan Yosef suka ƙara ƙin jininsa.

Genesis 37:9

Menene Yosef ya gani a mafarkinsa na biyu?

Yosef ya gan rana da wata da taurari sha ɗaya sun rusuna mashi.

A mafarkin Yosef na biyu, menene rana da wata da taurari suke wakilci?

Rana da wata da taurari suna wakilcin mahaifin Yosef, mahaifiyarsa da kuma 'yan'uwansa.

Genesis 37:12

Menene Yakubu ya aike Yosef zuwa kwarin Hebron ya je yayi?

Yakubu ya aike Yosef zuwa kwarin Hebron don ya duba ko 'yan'uwansa na lafiya sai ya kawo ma shi magana.

Genesis 37:18

Menene 'yan'uwan Yosef suka yi shirin aikatawa sa'adda suka gan shi zuwa?

'Yan'uwan Yosef suka yi shirin ƙashe shi su kuma jefa shi cikin ɗaya daga cikin ramukan.

Genesis 37:21

Wane shawara ne Ruben yayi wa 'yan'uwansa, kuma don menene?

Ruban ya ba da shawarar cewa 'yan'uwan su jefa Yosef a cikin rami, domin ya ceto shi.

Genesis 37:27

Su wanene 'yan'uwan Yosef suka sayar masu da Yosef kuma a nawa?

'Yan'uwan Yosef sun sayar da Yosef ga Isma'ilawa a kan azurfa ashirin.

Zuwa ina ne aka kai Yosef?

An kai Yosef Masar.

Genesis 37:31

Ya ya ne 'yan'uwan Yosef suka yi don su nuna cewa ya mutu?

'Yan'uwan Yosef sun ƙashe akuya suka ɗauki rigarsa suka tsoma a cikin jini sai suka ba Yakubu rigan.

Genesis 37:34

Menene Yakubu yayi bayan ya amince cewa Yosef ya mutu?

Yakubu ya yayyage tufafinsa ya sanya tsummokara a kwankwasonsa, yayi makokin ɗansa kwanaki da yawa.

Ga wanene akan sayar da Yosef a Masar?

An sayar da Yosef wa Fotifa wani maƙaddashin Fir'auna, a Masar.