Genesis 31

Genesis 31:1

Daga ina ne Laban da 'ya'yansa suka amince cewa Yakubu ya sami dukka dukiyarsa?

Laban da 'ya'yansa suka amince cewa Yakubu ya sami dukka dukiyarsa daga mallakarsa.

Wane umarne ne Yahweh ya ba wa Yakubu?

Yahweh ya ba wa Yakubu umarne cewa ya koma ƙasar ubanninsa da danginsa.

Genesis 31:7

Ya ya ne Allah ya ɗauke tumakan Laban ya ba wa Yakubu?

Allah ya sa dabbobin suka haifi 'ya'ya kyalloli, da kuma 'ya'ya masu zãne ne ladan Yakubu.

Genesis 31:14

Wane ra'ayi ne Rahila da Liya suke da shi ga mahaifinsu?

Rahila da Liya suka amsa suka ce ya maida dasu kamar bãre ya kuma ya lanƙwame kuɗinmu gabaɗaya.

Genesis 31:19

Menene Rahila ta yi kafin tafiya da Yakubu?

Rahila ta ɗauke allolin gidan mahaifinta.

Yaya ne Yakubu ya ruɗe Laban a wannan lokacin?

Yakubu ya ruɗe Laban ta wurin ƙin gaya masa cewa zai tashi.

Genesis 31:22

Menene Laban yayi a lokacin da aka faɗa mashi cewa Yakubu ya gudu?

Laban ya ɗauki danginsa ya kuma bi shi na tsawon tafiyar kwana bakwai.

Genesis 31:24

Menene Allah ya faɗa wa Laban a mafarki?

Allah ya faɗa wa Laban a mafarki cewa yayi hankali kada kayi magana da Yakubu mai kyau ko marar kyau.

Genesis 31:31

Don menene Yakubu ya faɗa cewa ya gudu daga Laban a ɓoye?

Yakubu ya faɗa cewa ya gudu daga Laban a ɓoye domin ya ji tsoron cewa Laban zai kwace 'ya'yan shi.

Menene Yakubu ya faɗa a lokacin da Laban ya yi masa zargin sata allolin gidansa?

Yakubu ya faɗa cewa duk wanda ya sace allolin gidan Laban ba zai ci gaba da rayuwa ba.

Genesis 31:34

Don menene Laban bai sami allonin gidansa a cikin mallakar Yakubu ba?

Laban bai sami allonin gidansa a cikin mallakar Yakubu ba domin Rahila ta zauna akansu kuma ta ce baza ta iya tashi ba domin tana cikin al'adarta.

Genesis 31:41

Menen tsawon lokacin da Yakubu yayi wa Laban aiki, kuma so nawa ne Laban ya canza masi hakinsa?

Yakubu yayi wa Laban aiki na shekaru ashirin kuma Laban ya canza masa hakinsa so goma.

Genesis 31:43

Yaya ne Laban ya nuna cewa yayi tunanin mallakar Yakubu a matsayin nasa?

Laban ya faɗa cewa dukka abin da ya gani na Yakubu nashi ne.

Genesis 31:45

Yaya ne Yakubu da Laban suka sa alama a wurin alkawarinsu?

Yakubu da Laban suka sa alama a wurin alkawarinsu ta wurin tara duwatsu a wurin.

Genesis 31:48

Wanene aka ayyana a matsayin shaidar sakanin Yakubu da Laban domin a tabatar cewa za a kiyaye alkawarin?

An ayyana Allah a matsayin shaidar sakanin Yakubu da Laban domin a tabatar cewa za a kiyaye alkawarin

Genesis 31:51

Menene amfanin tarin da ginshiƙin?

Tarin da ginshiƙin dukka shaidu ne na alkawarin da ta ce Laban Ko Yabuku ba za su wuce tarin da ginshiƙin don su cutar da juna ba.

Wane alkawari ne Yakubu da Laban suka yi?

Yakubu da Laban sun amince cewa baza su haye tarin duwatsun don cutar da juna ba.

Menene Yakubu yayi domin ya nuna cewa ya amince da alkawarin?

Domin ya nuna cewa ya amince da Laban game da alkawarin, Yakubu yayi rantsuwa da Allah da mahaifinsa Ishaku ya ji tsoro.

Genesis 31:54

Menene Laban yayi a washegari?

Laban ya tashi ya, ya sumbaci jikokinsa da 'ya'yansa mata ya kuma albarkace su sai ya koma gida.