Genesis 32

Genesis 32:3

Ga wanene Yakubu ya aika da sako a hanyarsa zuwa Kanaan

Yakubu ya aika da sako wa ɗan'uwansa Isuwa a hanyarsa zuwa Kanaan.

Akan wane dalili ne Yakubu ya aika wannan sakon?

Yakubu ya so ya sami tagomashi a idanun Isuwa.

Genesis 32:6

Menene Yakubu yayi sa'adda ya ji cewa Isuwa na zuwa da mutane ɗari huɗu?

Yakubu ya ji tsoro, sai ya raba mutanen dake tare da shi yayi sansani biyu domin idan Isuwa ya zo ga sansani ɗaya ya kawo ma na hari, ɗaya zasu kuɓuce.

Genesis 32:11

Menene bukatar Yakubu ga Yahweh?

Yakubu ya roƙi Yahweh ya cece shi daga hannun Isuwa.

Akan wane alkawari ne Yakubu ya tunawa Yahweh?

Yakubu ya Yahweh ya faɗa cewa zai sa ya wadata, zai maida zuriyarsa kamar rairayin teku.

Genesis 32:19

Menene Yakubu ya zata cewa zai yi ta wurin aika da kyaututtuka wa ɗan'uwansa Isuwa?

Yakubu ya zata cewa zai tausar da Isuwa da kyaututtukan da yake aikawa da su a gabansa domin daga baya, sa'adda zai gan shi, wataƙila zai karɓe shi.

Genesis 32:22

Ya ya ne Yakubu ya kasance shi kadai a wannan ɗare?

Ya ɗauki matayensa, da matayensa barori, da 'ya'yansa zuwa ƙetaren kududdufin Yabbok.

Genesis 32:24

Menene Yakubu yayi a wannan ɗaren har wayewar gari?

Yakubu yayi kokawa da wani mutum har wayewar gari.

Menene mutumin yayi a lokacin da ya ga cewa ba zai iya kayar da Yakubu ba?

Mutumin ya mazge Yakubu a kwankwasonsa.

Menene Yakubu ya bukaci kafin ya bar mutumin ya tafi?

Yakubu ya bukaci cewa mutumin ya albarkace shi.

Genesis 32:27

Menene mutumin ya faɗa cewa za a fara kiran Yakubu?

Mutumin ya faɗa cewa sunar Yakubu yanzu zai zama Isra'ila.

Genesis 32:29

Wanene Yakubu ya ce ya gani fuska da fuska a wannan ɗare?

Yakubu ya ce ya ga Allah fuska da fuska a wannan ɗaren.

Genesis 32:31

Wane damuwa ne Yakubu ya cigaba da shi bayan wannan ɗaren?

Yakubu yana ɗangyashi saboda kwankwasonsa.