Genesis 30

Genesis 30:1

Bisa ga Yakubu, don menene Rahila ba ta da 'ya'ya?

Bisa ga Yakubu, Allah ne ya hana ta samun 'ya'ya.

Genesis 30:3

Menene Rahila ta yi domin ta samu 'ya'ya?

Rahila ta ba wa Yakubu Bilha baiwanta domin ta samu 'ya'ya a madadin ta.

Genesis 30:7

Don menene Rahila ta faɗa cewa ta ci nasara akan 'yar'uwanta Liya?

Rahila ta faɗa cewa ta ci nasara domin Bilha baiwar ta ta haifi 'ya'ya biyu wa Yakubu.

Genesis 30:9

Menene Liya ta yi bayan ta gan cewa ta daina haihuwa?

Liya ta ba wa Yakubu Zilfa baiwarta domin ta haifa 'ya'ya a madadin ta.

Menene ya sa Liya t ce "Wannan rabo ne."?

Liya ta faɗa cewa, "Wannan rabo ne." domin Zilfa baiwarta ta haifa wa Yakubu ɗa.

Genesis 30:14

Menene Rahila ta ba wa Liya a maimakon 'ya'yan itacen manta'uwar ɗanta?

A maimakon 'ya'yan itacen manta'uwar Ruben, Rahila ta yarda wa Liya ta kwana da Yakubu a ɗaren.

Genesis 30:19

'Ya'ya maza nawa ne Liya ta haifa wa Yakubu?

Liya ta haifa wa Yakubu 'ya'ya maza shidda.

Genesis 30:22

Menene ya sa Rahila ta faɗa cewa an ɗauke kunyarta?

Sa'adda Rahila ta haifa wa Yakubu ɗa, ta faɗa cewa an ɗauke kunyarta.

Genesis 30:25

Wane roko ne Yakubu yayi wa Laban bayan da an haifi Yosef?

Yakubu ya roka cewa Laban ya bar shi ya tafi da iyalinsa zuwa gidansa da kuma ƙasarsa.

Genesis 30:27

Don menene Laban ba ya so ya bar Yakubu ya tafi?

Laban ya gane cewa Yahweh ya albarkace shi ta dalilin Yakubu ne.

Genesis 30:31

Wane lada ne Yakubu ya ƙarba a wurin Laban don aikinsa?

Yakubu ya ɗauke tumaki dabbare-dabbare da masu ɗigo, da waɗanda ke baƙaƙe daga cikin tumakin, da masu ɗigo da kyalloli daga cikin awakin.

Genesis 30:35

Ya ya ne Laban ya cutar da Yakubu game da hakinsa?

Da farko, Laban ya cire dabbobin da ya kamata Yakubu ya ɗauka kafin ya ba bashi tumakan ya yi kiwon.

Genesis 30:37

Wane irin ƙirare ne Yakubu ya fera fararen zãne a kai?

Yakubu ya fera fararen zãne a da rassan itacen almon da rassan itacen durumi.

Menene Yakubu yayi da fararen zãnen?

Yakubu ya sa fararen zãnen da yayi a gaban dabbobin, a gaban kwamamen ruwa in da suke zuwa su sha.

Genesis 30:39

Menene na faruwa a lokacin da dabbobin suna barbara a gaban ƙiraren?

A lokacin da dabbobin suna barbara a gaban ƙiraren suna haihuwar 'ya'yai masu zãne, da kyalloli, da masu ɗigo.

Genesis 30:41

Menene sakamakon Yakubu a kiwon dabbobin?

Sakamakon shi ne tumakin Laban suna da rashin ƙarfi kuma ƙarfafan kuma na Yakubu ne.