Genesis 29

Genesis 29:4

Daga ina mutanen da Yakubu yayi magana da su suke?

Mutanen daga Haran suke.

Wanene ya kuma zo rijiyan da garken tumakai?

Rahila, ɗiyar Laban, ta kuma zo rijiyan da garken tumakai.

Genesis 29:9

Menene Yakubu yayi wa tumakin Laban?

Yakubu ya gangarar da dutsen daga bakin rijiyar, ya kuma yi wa garken banruwa.

Genesis 29:11

Menene Yakubu ya faɗa wa Rahila kuma menene ta yi?

Yakubu ya gaya wa Rahila cewa shi dangin mahaifinta ne,sai Rahila ta ruga ta gaya wa mahaifinta.

Genesis 29:13

Yaya ne Laban yayi a lokacin da ya ji game da zuwan Yakubu?

Laban ya ruga domin ya same Yakubu, ya rungume shi, ya sumbace shi, ya kuma kawo shi cikin gidansa.

Genesis 29:15

Kwatanta 'ya'ya mata biyu na Laban.

Liya ce babbar kuma idanunta tausasa ne amma Rahila na da kyakkyawar siffa kuma ita ne ƙaramar.

Wane shiri ne Laban da Yakubu suka yi game da aikin Yakubu?

Sun amince cewa Yakubu zai bauta wa Laban na shekaru bakwai domin Rahila.

Genesis 29:19

Don menene shekaru bakwai na aikin Yakubu ya zama kamar ɗan kwanaki a wurinsa?

Shekaru bakwai na aiki sun zama masa kamar kwanaki kaɗan, domin ƙaunar da yake da ita wa Rahila.

Genesis 29:23

Ya ya ne Laban ya yaudare Yakubu?

Laban ya ba Yakubu Liya a maimakon Rahila, a daren bikin auren.

Wanene Laban ya ba wa Liya don ta zama baiwarta?

Laban ya ɗauki baiwarsa Zilfa ya ba ɗiyarsa Liya, ta zama baiwarta.

Genesis 29:26

Don menene Laban ya ce ya yaudare Yakubu?

Laban ya ce ba al'adarsu ba ce su bayar da ƙaramar ɗiya kafin ta fãrin a aure ba.

Wane shiri ne Laban da Yakubu suka yi game da aikin Yakubu?

Sun amince cewa Yakubu zai bauta wa Laban na wasu shekaru bakwai kuma a maimakon Rahila.

Genesis 29:28

Wanene Laban ya ba wa Rahila don ta zama baiwarta?

Laban ya bayar da Bilha ga ɗiyarsa Rahila, ta zama baiwarta.

Genesis 29:31

Menene Yahweh yayi a lokacin da ya gan cewa Yakubu ba ya ƙaunar Liya?

Yahweh ya sa Liya ta yi juna biyu, amma Rahila ba ta da ɗa.

Menene Liya ta yi begen zai faru idan ta haifi 'ya'ya wa Yakubu?

Liya ta yi begen cewa Yakubu zai ƙaunace ta idan ta haifa masa 'ya'ya.

Menene sunar ɗan fari na Liya?

Sunar ɗan farin Liya shine Ruben.

Genesis 29:35

Menene Liya ta faɗa bayan da ta haifi Yahuda?

Bayan da ta haifi Yahuda ta ce, "Wannan lokacin zan yabi Yahweh."