Genesis 28

Genesis 28:1

Wane umarni ne Ishaku ya ba wa Yakubu kafin ya tafi?

Ishaku ya umarce Yakubu kada ya auri 'yar Kanaan.

Ina ne Ishaku ya fada wa Yakubu cewa ya je ya samu mata?

Ishaku ya ce ma Yakubu ya je samo mata daga Laban, ɗan'uwan mahaifiyarsa.

Genesis 28:3

Albarkar wanene Ishaku ya roke Allah ya ba wa Yakubu?

shaku ya roke Allah ya ba wa Yakubu albarkar Ibrahim.

Genesis 28:8

Daga ina ne Isuwa ya sami daya daga cikin matansa sa'adda ya gan cewa matan Kanaan basu gamshi Ishaku ba?

Isuwa ya ɗauko mata daga 'ya'ya mata na Isma'ila, ɗan Ibrahim.

Genesis 28:12

Menene Yakubu ya gani a cikin mafarkinsa a hanya zuwa Haran?

Yakubu ya gan hawan bene an kafa bisa ƙasa zuwa sama da mala'iku suna hawa suna kuma sauka a kansa, kuma Yahweh ya na tsaya a bisansa.

Menene Yahweh ya fada game da kasar da Yakubu ke kwance akai?

Yahweh ya fada cewa za a ba Yakubu da zuriyarsa kasar da yake kwance akai.

Albarkar wanene Yahweh ya ba wa Yakubu?

Yahweh ya ba wa Yakubu albarkar Ibrahim.

Genesis 28:16

Menene Yakubu ya faɗa game da wurin da yayi mafarki?

Yakubu ya faɗa cewa wurin gidan Allah ne da kuma kofan sama.

Genesis 28:18

Wane suna ne Yakubu ya ba wa wurin da yayi mafarkin?

Yakubu ya sa wa wurin suna Betel.

Genesis 28:20

Menene Yakubu ya faɗa cewa Yahweh yayi domin ya zama Allahnsa?

Yakubu faɗa cewa ɗole Yahweh ya kasance tare da shi ya kuma kiyaye shi a cikin wannan hanya da yake tafiya, domin ya dawo lafiya zuwa gidan mahaifinsa.

Menene Yakubu yayi alkawari cewa zai ba wa Yahweh idan yayi masa waɗannan abubuwan?

Yakubu yayi alkawarin ba Yahweh bayar da kashi ɗaya cikin goma a gare shi.