Genesis 20

Genesis 20:1

Menene Ibrahim ya faɗa game da Saratu sa'adda yake zama a Gerar?

Ibrahim ya faɗa cewa Saratu 'yar'uwarta ce.

Menene Allah ya faɗa wa Abimelek bayan ya ɗauki Saratu?

Allah ya zo wurin Abimelek a mafarki, ya faɗa masa cewa shi mataccen mutum ne saboda ya ɗauke matar mutumin ce.

Genesis 20:4

Menene Abimelek ya faɗa wa Allah cewa an gaya mashi game da Ibrahim da Saratu?

Abimelek ya faɗa wa Allah cewa Ibrahim ya ce masa Saratu 'ya'uwarsa ce, kuma Saratu ta faɗa masa cewa Ibrahim ɗan'uwansa ne.

Genesis 20:6

Menene Allaha ya ce wa Abimelek ya yi, kuma menene Allah ya ce zai faru idan bai aikata ba?

Allaha ya ce wa Abimelek ya mayar da Saratu wa Ibrahim; ko kuma, shi da dukka mutanensa su mutu.

Genesis 20:8

Ya ya ne Mazajen Abimelek suka amsa sa'adda sun ji abin da Allah ya faɗa wa Abimelek?

Mazajen Abimelek sun tsorata sa'adda suka ji abin da Allah ya faɗa mashi.

Genesis 20:10

Don menene Ibrahim ya ce ya faɗa wa Abimelek cewa Saratu 'yar'uwarsa ce?

Ibrahim ya faɗa cewa ya ji tsoro Abimelek zai kashe shi saboda saratu.

A wane hanya ne Saratu 'yar'uwar Ibrahim?

Saratu 'yar mahaifinsa ne amma ba na mahaifiyarsa ba.

Genesis 20:15

Wane dabbobi da mutane ne Abimelek ya ba wa Ibrahim?

Abimelek ya ba wa Ibrahim tumaki da takarkari, bayi maza da mata.

Wane dalili ne Abimelek ya ba wa Saratu akan dalilin da ya ba wa ɗan'uwarsa azurfa dubu?

Abimelek ya faɗa wa Saratu cewa ya ba wa ɗan'uwanta azurfa dubu domin ya rufe duk wani laifin da yayi wa Saratu a fuskar duk wanda ke tare da Saratu da gaban kowa.

Genesis 20:17

Menene ya faru sa'adda Abrahim yayi addu'a ga Allah don Abimelek da mutanensa?

Allah ya warkar da Abimelek, matarsa, da bayinsa mata domin su iya haifa 'ya'ya.