Genesis 19

Genesis 19:1

Sa'adda Lutu ya gan mala'iku biyun suna shiga cikin Saduma, menene ya basu?

Lutu ya roƙe su da su kwana a gidansa sai su tafi washegari.

Menene amsar mala'ikun ga Lutu?

Mala'ikun sun faɗa cewa za su kwana a kwararo.

A roƙon Lutu, ina ne mala'ikun suka kwana a karshe?

A karshe, mala'ikun sun je sun kwana a gidan Lutu.

Genesis 19:4

Menene mutanen garin da suka ƙewaye gidan Lutu suke son Lutu yayi?

Mutanen sun so Lutu ya fitar masu da bãƙi biyun domin su kwana da su.

Genesis 19:6

Menene Lutu ya ba wa mutanen garin a maimako?

Lutu ya ba mutanen garin 'ya'yansa mata biyu a maimakon bãƙin.

Genesis 19:9

Yaya ne mtanen suka amsa wa Lutu?

Mutanen sun ce wa Lutu ya tsaya a can har sun kusa su ɓarke ƙofar.

Genesis 19:10

Menene mala'ikun suka yi?

Mala'ikun suka miƙa hannuwansu suka shigo da Lutu cikin gidan sai suka bugi mutanen da makanta.

Genesis 19:12

Menene mala'ikun sun ce Yahweh ya aike su su yi?

Mala'ikun sun ce an aike su su hallaka garin.

Genesis 19:14

Yaya ne surukan Lutu suka yi sa'adda ya ce masu su sauri su bar Saduma domin an yi kusa a hallaka ta?

Surukansa su ka ɗauka wasa ya ke yi.

Da safiya ta yi, menene mala'ikun suka ce wa Lutu yayi?

Mala'ikun sun faɗa wa Lutu cewa ya ɗauke matarsa da ''ya'yansa mata su fita daga garin.

Genesis 19:16

Don menene, da duk jinkirin Lutu mala'ikun suka kama hannuwan Lutu suka fitar da shi da iyalinsa wajen gari?

Mala'ikun sun fitar da su wajen garin domin Yahweh ya yi masa jinƙai.

Wane umarne ne mala'ikun suka ba wa Lutu sa'adda suka wajen garin?

Mala'ikun sun ce wa Lutu da iyalinsa su tserar da rayukansu, Kada su waiga baya.

Genesis 19:21

Ina ne mala'ikar ya bar Lutu da iyalinsa su ruga zuwa?

An bar Lutu da iyalinsa su ruga zuwa wata ƙaramar birnin da ake kira Zowar.

Genesis 19:23

Menene Yahweh yayi sa'adda Lot ya kai Zowar?

Yahweh ya saukar da ruwan wuta da matsanancin zafi bisa Soduma da Gamora.

Genesis 19:26

Menene matar Lutu ta yi kuma menene ya faru da ita?

Matar Lutu ta waiwaya baya, sai ta zama umudin gishiri.

Menene Ibrahim ya gani da sassafe sa'add a ya duba gangaren dukkan filayen?

Ibrahim ya ga hayaƙi na tashi daga filin kamar na hayaƙin matoya.

Genesis 19:30

Zauna ina Lutu ya tafi kuma don menene?

Lutu ya tafi zuwa duwatsu domin yana jin tsoron zama a Zowar.

Genesis 19:31

Wane shiri ne 'ya'ya mata na Lutu suka yi akan mahaifinsu?

'Ya'ya mata na Lutu sun shirya sa mahaifinsu ya bugu, sai su kwana da su domin su samu 'ya'ya.

Genesis 19:36

Wane kabilu ne suka zo daga 'ya'ya matan Lutu?

Mutanen Mowobawa da Ammoniyawa sun fita daga 'ya'ya matan Lutu.