Genesis 21

Genesis 21:1

Menene Yahweh yayi wa Saratu?

Yahweh ya ziyarci Saratu sai ta haifi Ibrahim kamar a lokacin da aka alkawarta.

Sa'adda Ishaku na kwana takwas, menene Ibrahim yayi?

Sa'adda Ishaku na kwana takwas, Ibrahim yayi masa kaciya.

Genesis 21:5

Menene Saratu ta faɗa cewa Allah ya sa ta yi?

Saratu ta faɗa cewa Allah ya sa ta dariya.

Genesis 21:8

A ranar da aka yaye Ishaku, menene Saratu ta gani?

Saratu ta gan ɗan Hajara na ba'a.

Genesis 21:10

Menene Saratu ta ce wa Ibrahim yayi da Hajara da ɗanta, kuma don menene?

Saratu ta ce wa Ibrahim ya kori Hajara da ɗanta domin ɗan Hajara ba zai ci gãdo, tare da Ishaku ba.

Menene amsar Ibrahim ga bukatar Saratu?

Ibrahim yayi baƙin ciki da bukatar Saratu.

Genesis 21:12

Menene Allah ya ce wa Ibrahim ya yi?

Allah ya ce wa Ibrahim ya saurare Saratu.

Genesis 21:14

Ina ne Hajara da ɗanta suka tafi bayan Ibrahim ya kore su?

Hajara da ɗanta sun tafi cikin jeji.

Genesis 21:17

Menene Allah ya faɗa wa Hajara cewa zai yi wa ɗanta?

Allah ya ce zai maishe ɗan Hajara babbar al'umma.

Genesis 21:19

Ya ya ne Hajara da ɗanta suka tsira?

Allaha ya buɗe idanun Hajara sai ta ga rijiyar ruwa.

Menene ya faru da ɗan Hajara sa'adda ya yi girma?

Ɗan hajara ya zama mafarauci sai mahaifiyarsa ta aura masa mata daga ƙasar Masar.

Genesis 21:22

Menene Abimelek ya so Ibrahim ya rantse ya yi masa?

Abimelek ya so Ibrahim ya rantse cewa ba zai yi masa ƙarya ba, ko 'ya'yansa, ko da zuriyarsa. Abimelek ya ce wa Ibrahim ya nuna masa irin wannan alƙawari mai aminci da ya nuna wa Ibrahim.

Genesis 21:25

Menene Ibrahim ya koke game da Abimelek?

Ibrahim ya koke game da Abimelek game da rijiyar ruwa da bayin Abimelek suka ƙwace daga wurinsa.

Genesis 21:28

Done menene Ibrahim ya aika da matan tumakin guda bakwai wa Abimelek?

Ibrahim ya aika da matan tumakin guda bakwai domin su zama shaida cewa shi ne ya haƙa wannan rijiya.

Genesis 21:31

Zuwa cikin wane ƙasa ne Abimelek ya koma?

Abimelek ya koma zuwa ƙasar Filistiyawa.

Genesis 21:33

Menene Ibrahim yayi a itacen sabara a Biyersheba?

Abrahim yayi wa Yahweh sujada, Allah madawwami.

Ina ne Ibrahim ya zauna a kwanaki masu yawa?

Ibrahim ya zauna a ƙasar filistiyawa na kwanaki masu yawa.