Genesis 15

Genesis 15:1

Sa'adda Yahweh ya bayyana ga Ibram, wane karfafawa ne Yahweh ya yi masa?

Yahweh ya ce wa Ibram kada ya ji tsoro kuma shine garkuwarsa da kuma babban ladansa.

Game da menene Ibram ya damu?

Ibram ya damu domin ba shi da ɗa kuma ma'aikacin shi ne magajinsa.

Genesis 15:4

Wanene Yahweh ya ce zai zama magajin Ibram?

Yahweh ya faɗa cewa wanda zai zo daga jikin Ibram ne zai zama magajinsa.

Zuriya nawa ne Yahweh ya ce Ibram zai samu?

Yahweh ya faɗa cewa Ibram zai samu zuriya masu yawa kamar tauraru.

Genesis 15:6

Yaya ne Ibram ya amsa alkawarin Yahweh kuma menene Yahweh yayi?

Ibram ya gaskanta Yahweh kuma Yahweh lisafta masa shi a kan adalci.

Wane tambaya ne Ibram yayi wa Yahweh game da ƙasar?

Ibram ya tambaye Yahweh cewa, "Ta yaya zan sani cewa zan gãje ta?"

Genesis 15:9

Menene Ibram yayi da dabbobin da aka ce ya kawo?

Ibram ya datsa su biyu biyu ya kuma ajiye kowanne tsagi a gefen ɗayan.

Genesis 15:12

Menene ya faru da Ibram sa'adda rana na faɗuwa?

Sa'adda rana na faɗuwa Ibram ya yi barci mai nauyi sai ga wani babban abin razana da kuma duhu sun lullluɓe shi.

Menene tsawon lokacin da Yaweh ya ce zuriyarsa zasu yi bauta a kuma tsananta masu?

Yahweh ya faɗa wa Ibram cewa za a bautar da zuriyarsa, a kuma tsananta musu har tsawon shekaru ɗari huɗu.

Genesis 15:14

Menene Yahweh ya ce zai faru da al'umma da ta azabantar da zuriyar Ibram?

Yahwe ya ce zai hukunta wannan al'umma.

Yaya ne Yahweh ya ce ran Ibram zai kare?

Yahweh ya ce Ibram zai mutu a cikin salama a shekara mai kyau.

Menene zai kai iyaka kafin zuriyar Ibrahim su dawo ƙasar da aka yi masu alkawari?

laifofin Amoriyawa za ta kai matsayinsa kafin zuriyar Ibram su dawo.

Genesis 15:17

A wannan ɗaren, menene ya faru a tsakanin yankin nama

Hayaƙin wuta da kuma harshen wutar tukunya da tartsatsi sun wuce a tsakanin yankin nama.

Wane alkawari ne Yahweh yayi da Ibram a wannan rana?

Yahweh yayi alkawari da Ibram cewa zai ba zuriyar shi wannan ƙasar.