Genesis 14

Genesis 14:10

Menene ya faru a Saduma a sakamakon faɗan sarakuna a kwarin Siddim?

An kwace dukka mallakar Saduma kuma an ɗauke Lot da dukka mallakarsa.

Genesis 14:13

Menene Abram yayi a lokacin da aka ce masa an ɗauke Lot?

Abram ya jagoranci horarrun mazajensa guda 318 su bi su.

Genesis 14:15

Kusa da wane babbar birni ne Abram suka yaki sarakunan, kuma menene sakamakon faɗan?

Abram ya yaki sarakunan arewa da Dimashku, ya kuma dawo da mallakan, Lot da kuma sauran mutane.

Genesis 14:17

Wane sarakuna biyu ne suka sadu da Abram a lokacin da suka dawo?

Sarkin Saduma da Melkizedik, Sarkin Salem suka sadu da Abram da suka dawo.

Menene zumuncin Melkizedik da Allah?

Melkizedik firist ne na Allah Mafi Ɗaukaka.

Menene Melkizedik ya kawo a lokacin da ya sadu Abram?

Melkizedik ya kawo gurasa da ruwan inabia a lokacin da ya hadu da Abram.

Genesis 14:19

Menene Melkizedik ya faɗa wa Abram?

Melkizedik ya albarki Abram, ya kuma albarka Allah Mafi Ɗaukaka.

Menene Abram yayi bayan Melkizedik ya yi masa magana?

Abram ya ba Melkizedik kaso ɗaya bisa goma na komai.

Genesis 14:21

Wane tayi ne sarkin Saduma yayi wa Abram?

Sarkin Saduma yayi nufin barin Abram ya ajiye dukka abubuwan idan ya na wa sarkin dukka mutanen.

Don menene Abram ba ya son dukiyan?

Ibram ya ɗaga hannunsa sama zuwa ga Yahweh, Allah Maɗaukaki, kuma ba ya son sarkin Saduma ya ce ya sa Ibram ya yi arziki.

Yaya ne Ibram ya amince ƙyautan Saduma?

Ibram ya faɗa cewa ba ya son mallakar saidai abin da matasan samari suka ci da kuma rabon mazajen dake tare da ni.