Genesis 16

Genesis 16:1

Menene tunanin Saratu game da yadda za ta ba wa Ibram zuriya?

Saratu fa faɗa wa Ibram ya kwana da baiwanta Hjara domin ta haifu masu.

Menene ya faru sakanin Hajara da Saratu sa'adda Hajara ta yi junabiyu?

Bayan da Hajara ta yi junabiyu, ta fara duban Saratu da reni.

Genesis 16:5

Wane ƙara ne Saratu ta kawo wa Ibram kuma yaya ne Ibram ya amsa?

Saratu ta kawo wa Ibram ƙaran cewa laifin shi ne da Hajara ta wulakanta ta, kuma Ibram ya ce wa Saratu ta yi wa Hajara abin da ta gan ya gamshe ta da.

Yaya ne Saratu ta yi wa Hajara bayan da ta haifu, kuma menene Hajara ta yi?

Saratu ta takura mata sosai, sai ta gudu daga gare ta.

Genesis 16:9

A cikin jeji, menene mala'ikar Yahweh ya ce wa Hajara ta yi?

Mala'ikan Yahweh ya ce wa Hajara ta dawo wurin Saratu ta kuma yi mata biyayya.

Wane alkawari ne mala'ikar Yahweh yayi wa Hajara?

Mala'ikan Yahweh ya yi wa Hajara alkawari cewa zuriyarta za su ruɓanɓaya sosai.

Genesis 16:11

Don menene an ce wa Hajara ta sa wa ɗan ta suna Isma'ila?

An ce wa Hajara ta sa wa ɗan ta suna Isma'ila domin Yahweh ya ji ƙuncinta.

Yaya ne Isma'ila zai yi wa sauran mutane?

Isma'ila zai yi magaftaka da dukkan mutane, zai kuma zauna a ware da 'yan,uwansa."

Genesis 16:13

Wane suna ne Hajara ta ba wa Yahweh?

Hajara ta ba Yahweh sunar, "Allah ne mai ganina."

Genesis 16:15

Shekarun Ibram nawa ne a lokacin da aka haife Isma'ila?

Ibram na da shekaru tamanin da shidda a lokacin aka haifi Isma'ila.