An yi amfani da kalmar "sama" saboda Betel na yankin da ke tudu fiye da Shekem.
Allah yai magana da kan sa a fakaice. AT: "Ka gina bagadi a can domina, Allahn ka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-123person)
"ya ce wa iyalin sa"
"Ku jefar da gumakan ku" ko "ku watsar da allolin karya dake tare da ku"
Wannan al'adar da aka saba ce ta yin tsarki kafin a wajen yin sujada ga Allah.
Sa sababbin tufafi alama ce ta nuna cewa sun maida kan su da tsarki kafin tunkarar Allah. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-symaction)
Ma'anonin "ranar" zasu iya zama 1) ranar da Yakubu ya gujewa Isuwa, ko 2) "ranar" na nufin lokacin da Yakubu ya shiga cikin ƙunci. AT: "lokacin da nake cikin mawuyacin hali" ko "lokacin da nake cikin matsala" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)
"saboda haka dukkan iyalan gidan Yakubu sun bada" ko "dukkan iyalin sa da barorin sa sun bayar"
A nan "a hannun su" na nufin abin da suka mallaka. AT: "da suka mallaka" ko "da suke dashi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)
"zobban su" (UDB). Ma'anar na iya zama 1) zinariyar da ke kunnuwansu za'a iya amfani da su wajen yin wasu allolin, ko 2) suka dauki yan kunnen daga birnin Shekem bayan sun kai masa hari sun kashe dukan mutanen. Zobban zasu tuna masu da zunuban su.
Allah ya zubawa mutanen garin tsoron Yakubu da iyalin sa anyi maganar sa kamar tsoro wani abu ne da ke faɗowa kan mutane. Kalmar "tsoron" zata iya zama "fargaba." AT: "Allah ya sanya tsoronsu ya fãɗo a bisa biranen" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-abstractnouns)
A nan "biranen" na nufin mutanen da suka rayu a garin. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)
Ya nuna babu mai yaƙar wani tsakanin iyalin Yakubu. Amma 'ya'yansa biyu, Simiyon da Lebi sun yaƙi yan'uwan Shekem Kan'aniyawa bayan ya ci zarafin ɗiyar Yakubu. Yakubu na tsoron zasu dauki fansa a Farawa 34:30. AT: "iyalin Yakubu" ko "gidan Yakubu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)
Wannan sunan birni ne. Duba yadda aka fassara wannan a Farawa 28:18. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)
Mai fassara zai iya ƙara dan bayani mai cewa: "Sunan El Betel na nufin 'Allahn Betel.'" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)
"a wurin Allah ya bayyana kansa ga Yakubu"
Wannan sunan mace ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)
Mai jiya wata mace ce dake lura da yaron wata matar. Ana girmama mai jiyar sosai don tana da tasiri ga iyalin.
Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "A ka bizne ta a gangare daga Betel" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)
Jimlar "gangare daga" an yi amfani da ita ne domin an bizne ta a wurin da yake bai kai bisar yankin Betel ba.
Mai fassara zai iya ƙara dan bayani mai cewa: "Sunan Allon Bakut na nufin 'itacen rimi inda ake kuka." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)
Za a iya tabbatarwa cewa suna Betel. AT: "Sa'ad da Yakubu ya zo daga Fadan Aram, yayin da yake a Betel" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)
A nan "albarka" na nufin a bayyana abubuwa masu kyau akan wani da yi masa fatan alheri.
Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "amma ba za a sake kiran sunanka Yakubu ba" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)
"Allah ya cewa Yakuba"
Allah ya fadawa Yakubu ya hayayyafa don su mamaye duniya. Kalmar "hayayyafa" na bayyana yadda zai zama da "albarka." Duba yadda aka fassara wannan a Farawa 1:22. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-doublet da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)
A nan "al'umma" da "al'ummai" na nufin zuriyar Yakubu wanda zasu gina ƙasashen. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)
A nan "tafi daga" an yi amfani da ita ne domin akan yi tsammanin Allah na zama a sama ko saman duniya. AT: "Allah ya bar shi"
Wannan ginshiƙin tunatarwa ne wanda a taƙaice na nufin babban dutse da aka kafa a karshen sa.
Wannan alama ce cewa yana miƙa ginshiƙin ga Allah. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-symaction)
Masu fassara zasu iya ƙara dan bayani mai cewa "Sunan Betel na nufin 'gidan Allah'"
Wannan wani suna ne na garin Betlehem.
"ta na samun matsaloli wajen wajen haihuwa"
"Lokacin da naƙudar tayi tsanani"
wani da ke taimakon mace yayin haihuwa
"numfashin mutuwa" numfashin karshe ne kafin mutum ya mutu. AT: "kafin ta mutu, yayin da take numfashin ta na karshe" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)
Mai fassara zai iya ƙara dan bayani mai cewa: "Sunan Benoni na nufin 'dan tausayi.'" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)
Mai fassara zai iya ƙara dan bayani mai cewa: "Sunan Benyamin na nufin 'dan hannun dama.'" Jimlar "hannun dama" na nuna wurin jinkai na musamman.
Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "sai aka bizne ta" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)
"a gefen hanya" (UDB)
"Alamar kabarin Rahila ne har wa yau"
"har zuwa yanzu." Wannan na nufin har lokacin da marubucin ke rubuta wannan.
Wannan ya nuna iyalin Isra'ila da barorinsa na tare da shi. Cikakkiyar ma'anar wannan bayani za a iya fayyace shi. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)
Wannan sunan baranyar Rahila ce. Duba yadda aka fassara wannan sunan a Farawa 29:28 (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)
Wannan ta fara sabon batu, wanda ya ci gaba a ayoyin da ke biye.
"'ya'ya maza 12" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)
Wannan ya nuna ba Benyamin cikin su wanda aka haifa a ƙasar Kan'ana kusa da Betlehem. An faɗi Fadan Aram ne saboda yawancin su a can aka haife su. AT: "waɗanda a ka haifa masa a Fadan Aram, in banda Benyamin da aka haifa a ƙasar Kan'ana" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)
A nan "zo" kan iya zama "je." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-go)
Wannan wani suna ne na birnin Hebron. Mai yiwuwa an sa sunan ne don martaba Mamri, abokin Ibrahim wanda ya zauna can. Duba yadda aka fassara wannan a Farawa 13:16. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)
Wannan sunan wani gari ne. Duba yadda aka fasaara wannan a Farawa 23:1
"shekaru 180" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)
"Ishaku ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya kuma mutu." Jimlar "ya yi numfashin sa na ƙarshe" da "mutu" na nufin kusan abu ɗaya. Duba yadda aka fasara irin wannan jimlar a Farawa 25:7. AT: "Ishaku ya mutu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-doublet)
Wannan hanya ce ta cewa mutum ya mutu da taushin rai. Duba yadda aka fassara wannan a Farawa 25:7. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-euphemism)
Wannan na nufin Ishaku ya mutu, ruhun shi ya tafi wurin da magabatan sa suka tafi. AT: "ya je wurin iyalin sa da suka mutu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)
Jimlar "tsohon mutum" da "cike da kwanaki" na nufin kusan abu ɗaya. Sun bayyana Ishaku ya yi rayuwa ta dogon lokaci. AT: "bayan yayi rayuwa ta dogon lokaci ya kuma tsufa sosai" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-doublet)