Genesis 34

Genesis 34:1

Yanzu

A nan amfanin wannan kalmar shine na alamar sabon sashi na labarin

Dina

Wannan sunan 'yar Liya ne. Duba yadda aka fassara wannan sunan a Farawa 30:19. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Bahibiye

Wannan sunan wani kungiyar mutane ne. Duba yadda aka fassara wannan sunan a Farawa 10:15. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

yariman garin

Wannan Hamor ne ba Shekem ba. Kuma, "yarima" a nan ba yana nufin dan sarki ba. Yana nufin Hamor ne shugaban mutane a wannan yankin

ya ɓata ta, ya kuma kwana da ita

Shekem yayi wa Dina fyaɗe. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-euphemism)

Ya shaƙu da Dina

"Ta dauke masa hankali" (UDB). Wannan na magana kan Shekem yana kaunar Dina kuma ya so ya zauna tare da ita kamar wani abu na matsa masa ya zo wurin ta. AT: "yana so matuƙa ya zauna da Dina" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

yi mata magana mai taushi

Wannan na nufin yana yi mata magana mai sosa zuciya don ya gamsar da ita yana son ta haka kuma yana son ta kaunace shi.

Genesis 34:4

Yanzu Yakubu

"Yanzu" an yi amfani da ita a nan don nuna canji daga labari zuwa matashiya game da Yakubu. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-background)

Yakubu ya ji cewa ya

Kalmar "ya" na nufin Shekem

ya ƙazantu

Wannan yana nufin cewa Shekem ya ƙasƙantar da Dina sosai ta hanyar tilasta mata ta kwana da shi.

ya kame bakinsa ko yayi shiru

Wannan hanya ce ta cewa Yakubu bai ce ko yi wani abu kan matsalar ba. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

Genesis 34:6

Hamor ... ya tafi wurin Yakubu

"Hamor ... ya tafi wurin Yakubu"

Mutanen ransu ya ɓaci

"mutanen sun fusata"

Suka fusata sosai ... bai kamata a aiwatar da irin haka ba

Wannan zai iya zama maganar da dan Yakubu yayi, kamar yadda ya ke a UDB. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-quotations

ya kunyatar da Isra'ila

A nan kalmar "Isra'ila" na nufin dukan iyalin Yakubu. Isra'ila a matsayin mutane sun kunyata. AT: "ya ƙasƙantar da iyalin Isra'ila" ko "ya kawo abin kunya ga mutanen Isra'ila" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

tilasta kansa bisa ɗiyar Yakubu

"cin zarafin yarinyar Yakubu"

domin bai kamata a aiwatar da irin haka ba

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "domin bai kamata a aiwatar da irin haka ba" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

Genesis 34:8

Hamor ya yi magana da su

"Hamor ya yi magana da Yakubu da 'ya'yan sa"

na ƙaunar ɗiyarka

Kalmar "kaunar" na nufin son da ke tsakanin namiji da mace. AT: "kaunar ta da son auren ta"

ka bayar da ita a gare shi a matsayin mata

A wasu al'adun, iyaye kan zaɓa wa yayan su wadanda zasu aura.

Ku yi auratayya da mu

A yi auratayya na nufin auren wanda ba asalin ku ɗaya ba. AT: "barin auratayya tsakanin mutanen ku da mutanen mu"

za a buɗe ƙasar a gare ku

"za a buɗe ƙasar a gare ku"

Genesis 34:11

Shekem ya ce wa mahaifinta

"Shekem ya ce wa mahaifin Dina wato Yakubu"

Bari in sami tagomashi a idanunku, duk kuma abin da kuka ce mani zan bayar

A nan "idanun" na matsayin tunani ko ra'ayin mutum. AT: "idan zaka amince mini, to zan baka duk abinda kake buƙata" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

sadaki

A wasu al'adun, akan buƙaci namiji ya bada kuɗi, kadara, dabbobi, da wasu kyaututtuka ga iyalin budurwar a lokacin aure.

Ya'yan Yakubu suka amsa wa Shekem da Hamor mahaifinsa tare da zamba

Kalmar "zamba" zata iya komawa "karya". AT: "Amma yaran Yakubu sun yi wa Shekem da Hamor ƙarya lokacin da suka amsa masu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-abstractnouns)

Shekem ya ƙazantar da Dina

Wannan yana nufin cewa Shekem ya ƙasƙantar da Dina sosai ta hanyar tilasta mata ta kwana da shi. Duba yadda kuka fassara "ƙazantacce" a cikin Farawa 34:4.

Genesis 34:14

Suka ce masu

"'Ya'yan yakubu suka cewa Shekem da Hamor'"

Ba za mu iya yin wannan abu ba, mu bayar da 'yar'uwarmu

"Ba zamu yarda mu bada Dina aure ba"

domin zai zama abin kunya a gare mu

"domin zai zama abin kunya a gare mu." A nan "mu" na nufin 'ya'yan Yakubu da dukkan mutanen Isra'ila. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-exclusive)

bayar da 'ya'yanmu mata a gare ku, mu kuma zamu ɗauki 'ya'yanku mata a gare mu

Wannan na nufin zasu bar wani daga cikin iyalin Yakubu ya auri wani mazaunin ƙasar Hamor.

Genesis 34:18

Maganganunsu suka gamshi Hamor da ɗansa Shekem

A nan "kalmar" na nufin abin da aka faɗa. AT: "Hamor da ɗansa suka yarda da abinda 'ya'yan Yakubu suka faɗa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

yin abin da suka ce

"su yi kaciya"

yarinyar Yakubu

"Yarinya Yakubu Dina"

saboda kuma shi ne taliki mafi daraja a dukkan gidan mahaifinsa

Za'a iya fasara wannan a matsayin sabuwar jimla. Mai yiwuwa Shekem ya san cewa sauran mutanen zasu yarda a yi masu kaciya domin suna girmama shi sosai. AT: "Shekem ya san cewa duk mutanen da ke gidan sa zasu yarda da shi domin an fi darajanta shi a tsakanin su" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Genesis 34:20

ƙofar birninsu

Abin da aka saba gani ne shugabanni su haɗu a ƙofar birni domin yanke shawara a hukumance.

Mutanen nan

"Yakubu, 'ya'yan sa, da kuma mutanen Isra'ila"

salama da mu

A nan "mu" ta ƙunshi Hamor, ɗansa da dukkan mutanen da suka yi magana dasu a ƙofar birnin. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-inclusive)

bari su zauna cikin ƙasar su kuma yi sana'a a ciki

"bari su zauna cikin ƙasar su yi kasuwanci a ciki "

tabbas, ƙasar na da isasshen girma domin su

Shekem yayi amfani da kalmar "tabbas" domin ƙara armashi ga batun. "saboda, tabbas, ƙasar na da isasshen girma domin su" ko "saboda, da gaske, akwai isasshen fili domin su"

ɗauki 'ya'yansu mata ... mu bayar da 'ya'yanmu mata

Wannan na nufin aure tsakanin matan wata ƙabila da mazan wata ƙabila. Duba yadda aka fasara makamantan jimloli a cikin Farawa 34:8

Genesis 34:22

Muhimmin Bayani:

Hamor da ɗansa Shekem sunci gaba da magana ga dattawan gari.

A wannan matakin kaɗai mutanen za su yarda su zauna da mu kuma mu zama mutane ɗaya. Idan a ka yi wa kowanne namiji a cikin mu kaciya, kamar yarda suke da kaciya.

"Sai dai ƙadai idan a ka yi wa kowanne namiji a cikin mu kaciya, kamar yarda mutanen Isra'ila ke da kaciya, za su yarda su zauna da mu kuma mu zama mutane ɗaya"

Ba dukkan dabbobinsu da kaddarorinsu - dukkan dabbobinsu zasu zama namu ba?

Shekem yayi amfani da tambaya don tabbatar cewa dabbobi da kadarorin Yakubu zasu zama na mutanen Shekem. Ana iya fassara wannan azaman bayani. AT: "Dukkan dabbobin su da kadarorinsu zasu zama namu." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

Genesis 34:24

Kowanne namiji a ka yi masa kaciya

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "Don haka Hamor da Shekem suka sami wanda ya yiwa dukan maza kaciya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

A rana ta uku

"uku" lamba ce ta uku. Za a iya cewa. AT: "Bayan kwana biyu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-ordinal)

sa'ad da suke cikin zafi tukuna

"sa'ad da mutanen garin ke cikin zafi tukuna"

kowannen su ya ɗauki takobinsa

"suka ɗauki takubban su"

suka kai hari ga birnin

A nan "birnin" na nufin mutane. AT: "sun kai hari ga mutanen birnin" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

tabbacin tsaro, suka kashe dukkan mazajen

Za a iya fasara wannan a matsayin sabuwar jimla. "tsaro. Simiyon da Lebi suka kashe dukkan mazajen birnin"

ta kaifin takobi

A nan "kaifin" na nufin kaifin takobi. AT: "ta wurin kaifin takobin su" ko "da takobin su" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-synecdoche)

Genesis 34:27

gawarwaki

"gawarwakin Hamor, Shekem, da mutanen su"

suka washe garin

"suka sace duk wani abu mai kyau dake birnin"

saboda mutanen sun ɓata 'yar'uwarsu

Shekem kadai ya ci zarafin Dinah, amma 'ya'yan Yakubu sun dauki iyalin Shekem da duk mazaunin garin a matsayin masu hannu a ciki

Suka ɗauki garkunan su

"'ya'yan Yakubu suka ɗauki garkunan"

dukkan dukiyarsu

"duk abin da suka mallaka da kuɗi"

Dukkan 'ya'yayensu da matayensu, suka ɗauke

"suka ɗauke dukkan 'ya'yayensu da matayensu"

Genesis 34:30

Kun kawo mani matsala

Kawowa wani matsala an bayyana shi kamar matsala wata aba ce da ake kawowa tare da dorawa akan wani. AT: "Kun kawo mani matsala babba" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

kun sa in yi ɗoyi ga mazaunan ƙasar

Sa mutanen garin su nuna ƙiyayya kan Yakubu an bayyana shi kamar yayan Yakubu sun mai dashi yana ɗoyi a zahiri. AT: "kun maishe ni abin kwatanci ga mutanen gari" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

Ni kima ne ... gãba da ni, su kuma kawo mani hari, daganan zan hallaka, ni da gidana

A nan kalmar "Ni" da "mani" na nufin iyalan gidan Yakubu. Yakubu yace "Ni" ko "mani" kawai saboda shi ne shugaba. AT: "Gidana kima ne ... gãba da mu, su kuma kawo mana hari, daganan zamu hallaka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-synecdoche)

idan suka tattara kansu tare don gãba da ni, su kuma kawo ma ni hari

"su kafa runduna su kawo mani hari" ko "su kafa runduna su kawo mana hari"

daga nan zan hallaka

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "zasu hallaka ni" ko "zasu hallaka mu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

Ya kamata Shekem ya yi da 'yar'uwarmu kamar karuwa?

Simiyon da Lebi sun yi amfani da tambaya wajen tabbatar da cewa Shekem yayi mugun abu da ya cancanci mutuwa. AT: "Bai kamata Shekem ya yi wa 'yar'uwarmu kamar ita karuwa ce!" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)