Genesis 33

Genesis 33:1

mutane ɗari huɗu

"mutane 400" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)

Yakubu ya raba 'ya'yan ... matayen barori

Wannan ba yana nufin Yakubu ya raba yayan daidai ba. Yakubu ya raba yayan yadda kowanne ya ko ta tafi tare da mahaifiyarta. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

barorin mata

"barorin mata." Wannan na nufin Bilha da Zilfa.

Shi da kansa kuma ya tafi gaba da su

A nan "dakansa" na nuna Yakubu ya tafi shikadai a gaban wasu. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rpronouns)

Ya rusuna

A nan kalmar "rusuna" na nufin duƙawa don nuna ƙasƙanci tare da bangirma ga wani. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-symaction)

Genesis 33:4

same shi

"tarar da shi"

ya rungume shi, ya rungumi wuyansa, ya sumbace shi

Za'a iya fasara wannan zuwa sabon jimla. AT: "Isuwa ya sa kafadarsa a kan Yakubu, ya rungume shi, ya kuma sumbace shi"

Suka yi kuka

Ana iya fassara wannan a sarari. AT: "Sai Isuwa da Yakubu suka yi kuka saboda suna cike da farin cikin sake ganin juna" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

ya ga mata da yaran

"ya ga mata da yaran da ke tare da Yakubu"

'Ya'yan da Allah ta wurin alherinsa ya ba bawanka ne

Jimlar "bawanka" hanyar bangirma ce da Yakubu ya dubi kansa. AT: "wadannan ne ya'yan da Allah ta wurin alherinsa ya ba bawanka." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-123person)

Genesis 33:6

barorin mata

"barorin mata." Wannan na nufin Bilha da Zilfa.

Ya rusuna

A nan kalmar "rusuna" na nufin duƙawa don nuna ƙasƙanci tare da bangirma ga wani. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-symaction)

Mene ne kake nufi da dukkan waɗannan ƙungiyoyi da na tarar

Maganar "dukkan wadannan ƙungiyoyin" na nufin kungiyoyin barorin da Yakubu ya aika su kai kyautai ga Isuwa. AT: "Me ya sa ka aiko duk wadan nan kungiyoyin su zo wuri na?"

Domin in sami tagomashi a gaban shugabana

A nan "gaban" na nufin tunanin mutum ko ra'ayin sa. AT: "Domin ka, ya shugaba na, ka gamsu da ni" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

shugaba na

Jimlar "shugaba na" hanyar bangima ce ta nuna Isuwa. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-123person)

Genesis 33:9

Ina da isassu

Kalmar "dabbobi" ko "kaya" an fahimce ta. AT: "I na da isassun dabbobi" (UDB) ko "I na da isassun kaya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-ellipsis)

idan na sami tagomashi a idanunka

A nan "idanunka" na nufin tunani ko ra'ayin mutum. AT: " idan na sami tagomashi a idanunka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

kyauta ta daga hannuna

A nan "hannu" na nufin Yakubu. AT: "wadan nan kyaututtuka da na ke baka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-synecdoche)

hannu na, domin da gaske

Za'a iya fasara wannan a matsayin sabuwar jimla. "hannu na. Domin tabbas"

na ga fuskar ka, kuma kamar ganin fuskar Allah ne

Ma'anar wannan batu nada dan duhu. Mai yiwuwa ma'anar ta zama 1) Yakubu na murna cewa Isuwa ya gafarta masa kamar yadda Allah ya gafarta masa ko 2) Yakubu na mamakin sake ganin dan'uwansa kamar yadda yayi mamakin ganin Allah ko 3) Yakubu ya natsu domin zuwa gaban Isuwa kamar yadda ya natsu a gaban Allah. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-simile)

na ga fuskar ka

A nan "fuska" na nufin Isuwa. Yana da kyau a fasara "fuska" saboda amfanin kalmar a nan da "fuskar Allah" da "fuska da fuska" a Farawa 32:29. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-synecdoche)

da aka kawo maka

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "wanda bayina suka kawo maku" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

Allah ya aiwatar da alheri zuwa gare ni

"Allah yayi mani da kyau" ko "Allah ya albarkace ni sosai"

Yakubu ya lallashe shi, Isuwa kuma ya karɓe su

Abin da aka saba ne aƙi amsar kyauta da farko, amma sai a amsa kafin mai badawa ya yi fushi.

Genesis 33:12

Shugabana ya sani

Wannan wata hanya ce ta bangirma da Isuwa ke wa kansa . AT: "kai,shugabana, ka sani" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-123person)

yaran ƙanana ne

Ana iya bayyana ma'anar a bayyane. AT: "yaran sun yi ƙanƙantar da bazasu iya tafiya da sauri ba" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Idan a ka kora su da ƙarfi a rana ɗaya

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "Idan a ka kora su da ƙarfi a rana ɗaya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

bari shugabana ya tafi gaba da bawansa

Wannan wata hanya ce ta bangirma da ake wa Yakubu. AT: "Shugaba na, Ni baranka ne. Ina roko ka tafi gaban baranka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-123person)

bisa ga saurin dabbobin dake a gabana

"bisa ga saurin dabbobin da na ke kulawa zasu iya tafiya"

Seyir

Wannan wani yanki ne mai tsaunika a Edom. Dubi yadda aka fassara wannan a 32:3 (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Genesis 33:15

Me yasa zaka yi haka?

Yakubu yayi amfani da tambaya ya nuna Isuwa bai kamata ya bar mutane ba. AT: "Kada kayi haka!" ko "bai kamata kayi haka ba!" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

Shugabana ka

Wannan wata hanya ce ta bangirma da ake wa Isuwa. AT: "kai, shugabana, ka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-123person).

Sukkot

Masu fassara zasu iya ƙara dan bayani cewa, "Sunan Sukkot na nufin 'mahalli'" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

ya gina wa kansa gida

Akawai alamun gidan harda iyalin sa. AT: "ya gina wa kansa gida da iyalinsa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

domin dabbobin sa

"domin dabbobin da yake kulawa"

Genesis 33:18

Muhimmin Bayani:

Wannan ya fara sabon sashi na labarin. Marubucin ya nuna abin da Yakubu yayi bayan ya huta a Sukkot.

Lokacin da Yakubu ya zo daga Fadan Aram

"Bayan Yakubu ya bar Fadan Aram"

Sa'adda Yakubu ya ... ya kasance ... ya kafa sansani

An faɗi Yakubu ne saboda shi ne shugaban iyalin. Wannan ya nuna iyalinsa na tare da shi. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Ya kafa sansani kusa da

"Ya kafa sansani kusa da"

fili

"filin ƙasa"

Hamor

Wannan sunan mutum ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

mahaifin Shekem

Shekem sunan wani gari ne da kuma sunan wani mutum

El Elohi Isra'ila.

Mai fassara zai iya ƙara dan bayani mai cewa: "sunan El Elohi Isra'ila na nufin Allah, Allahn Isra'ila." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)