Genesis 32

Genesis 32:1

Mahanayim

Mai fassara zai iya ƙara dan bayani cewa "sunan Mahanayim na nufin 'sansani biyu.'"

Genesis 32:3

Seyir

Wannan yanki ne mai duwatsu a cikin yankin Idom. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Ga abin da zaku cewa shugabana Isuwa: Ga abin da bawanka Yakubu ya ce: 'Ina ... a idanun ka

Wannan na da baka cikin baka. Wato magana cikin magana. AT: "Wannan ne abin da nake so ka faɗawa shugabana Isuwa. Ku shaida masa cewa ina ... a idanun sa." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-quotesinquotes da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-quotations)

shugabana Isuwa

Yakubu na amfani da kalmomi masu tsabta yana kwatanta dan'uwansa a matsayin "shugaba na."

baranka Yakubu

Yakubu na amfani da kalmomi masu tsabta yana kwatanta kansa a matsayin "bara"

domin in sami tagomashi a idanunka

A nan "idanunka" na nufin tunanin mutum ko ra'ayin sa. AT: "domin in sami tabbacin ka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Genesis 32:6

mutum dari huɗu

"mutum 400" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)

tsorata

Wannan wani yanayi ne na mara daɗi da mutum ka tsinci kansa lokacin da akwai hatsarin da ke fuskantar sa ko wasu.

haushi

"damuwa:" ko "mawuyacin hali"

ga sansani ɗaya ya kawo mana hari, daganan sansanin da ya rage zasu kuɓuce

A nan "sansani" na nufin mutane. AT: "ya kawo mana hari a sansani ɗaya, daganan sansanin da ya rage zasu kuɓuce" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Genesis 32:9

Allah na mahaifina Ibrahim, da Allah na mahaifina Ishaku, Yahweh

Wannan ba yana nufin alloli da yawa ba, amma ga Allah daya da suke yiwa sujada. AT: "Yahweh, wanda shine Allahn kaka na Ibrahim da baba na Ishaku" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Yahweh, wanda ya ce mani, 'Ka koma ga ƙasarka da danginka, zan kuma wadata ka

Wannan magana ce cikin magana. AT: "Yahweh, Kai wanda ka ce in koma ƙasa ta da dangi na, ka kuma ce zaka wadata ni" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-quotesinquotes da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-quotations)

da danginka

"da ga iyalinka"

zan wadata ka

"Zan yi alheri gare ka" ko "za yi maka yin kyau"

Ban cancanci dukkan ayyukanka na alƙawarin aminci ba da dukkan yarda da ka yi domin bawanka ba

Kalmar "amincewa" da "dukkan yarda" zasu iya zama "aminci" da "biyayya." Ban cancanci ka ci gaba da zama da aminci gareni ba ko ka zama da yarda gare ni, bawan ka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

Baran ka

Wannan hayar cewa "ni" da ladabi ce

yanzu na zama sansanai biyu

A nan "na zama" na nufin abin da yake da shi yanzu. AT: "gashi yanzu ina da mutane, danbbobi, da abin hannu da ke tare da ni domin in yi sansani biyu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-synecdoche)

Genesis 32:11

yantas da ni

"cece ni"

daga hannun ɗan'uwana, daga hannun Isuwa

A nan kalmar "hannu" na nufin iko. Jimloli biyun mai yiwuwa nada ma'ana ɗaya. Ta biyun ta bayyana mana yadda dan'uwan da Yakubu ke ƙudiri shine Isuwa. AT: "daga ikon dan'uwana, Isuwa" ko "daga dan'uwana, isuwa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-parallelism)

Ina tsoron sa, cewa zai

"I na sakkar zai yi"

Amma ka ce, 'Babu shakka zan sa ka wadata ... yawansu!

Wannan magana ce cikin magana. AT: "Amma ka ce mani zaka wadata ni, za kuma ka maishe da zuriyata ... yawansu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-quotesinquotes da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-quotations)

wadata ka

"yi maka alheri" ko "kulawa da kai"

Zan maida zuriyarka kamar rairayin teku

Wannan na magana akan zuriyar Yakubu mai ɗinbin yawa kamar rairai na bakin teku. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-simile)

wanda ba za'a iya ƙirgawa ba

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "wanda ba mai iya ƙirgawa saboda yawan su" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

Genesis 32:13

Ɗari biyu

"200" (Duba:" /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)

ashirin ... talatin ... arba'in ... goma

"20 ... 30 ... 40 ... 0" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)

da ƙanan su

"da kana nan su"

Waɗannan ya bayar dasu cikin hannun bayinsa

A nan "cikin hannun" na nufin a bada iko a kansu. AT: "Ya raba su zuwa ƙananun garke, ya ba kowanne baran sa iko akan garke" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

Ku sanya tazara tsakanin kowanne garken

"Bari a sami tazara tsakanin kowanne garken"

Genesis 32:17

Ya sa ka'ida

"ya bada umarni"

tambaye ka ... da ke gabanka?'

Wannan magana ce cikin magana. AT: "duk wanda ya tambaya ka shugabanka, ina zaka je, ko kuma wa ya mallaki wadannan dabbobin da ke gaban ka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-quotesinquotes da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-quotations)

Kai na wanene?

"wanene shugaban ka?"

dabbobin wane ne waɗannan da ke gabanka?

"dabbobin wane ne waɗannan da ke gabanka?"

Daga nan za ka ce, 'Na bawanka ne Yakubu. Kyauta ce a ka aiko wa shugabana Isuwa. Duba, shi ma yana zuwa bayan mu.'

Wannan magana ce cikin magana. AT: "Ina so ga shaida masa cewa dukan wadannan na Yakubu ne, da baransa, kuma zai ba Isuwa shugaban sa. Bayan nan ka faɗa masa Yakubu na kan hanya zai same shi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-quotesinquotes da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-quotations)

baranka Yakubu

Yakubu na nuna kansa a matsayin baran Isuwa cikin natsuwa

ga shugabana Isuwa

Yakubu na nuna Isuwa a matsayin shugaban sa cikin natsuwa.

zuwa bayan mu

A nan "mu" na nufin baran da ke magana da sauran barorin da ke kawowa Isuwa kargunan. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-exclusive)

Genesis 32:19

ya sake bada umarnai ga ƙunguya ta biyu

"ya umarci ƙungiya ta biyu"

Tilas kuma ku ce, 'Bawanka Yakubu

Ma'anonin zasu iya zama cewa: 1) "Kuma zaku ce, 'baran ka Yakubu"' ko 2) "za ku ce, 'baranka Yakubu.'"

Zan tausar da shi

"Zan tausar da shi " ko "Zan sa fushin sa ya tafi"

zai karɓe ni

"zai amshe ni da zuciya ɗaya"

Sai kyaututtukan suka tafi gaba da shi

A nan "kyaututtuka" na nufin baran da ke kai kyaututtukan. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Shi dakansa ya tsaya

A nan "dakansa" na bayyana cewa Yakubu bai tafi tare da baran ba. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rpronouns)

Genesis 32:22

barorin matayensa su biyu

"barorin matayensa su biyu." Wannan na nufin Zilfa da Bilha

kudidifi

wuri mara zurfi a rafi wanda ke da saukin hayewa

Yabbok

Wannan sunan kogi ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

dukkan mallakarsa

"dukkan abin da yake da shi"

Genesis 32:24

har gari ya waye

"har wayewar gari" (UDB)

kwankwaso

"ƙugu." Wannan wani wuri ne inda ƙashin ƙafar sama ya haɗu da kwankwaso.

kwankwason Yakubu ya goce sa'ad da yake kokawa da shi

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "mutumin ya goce wa Yakubu kwankwaso yayin da suke kokowa da shi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

gari yana wayewa

"rana zata fito da sauri"

albarka

A nan "albarka" na nufin a furta abin kirki akan wani tare da yi masa fatan alheri.

Ba zan bar ka ka tafi ba sai ka albarkace ni

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "Tabbas bazai yiwu ba! sai ka albarkace ni, kafin in barka ka tafi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-doublenegatives)

Genesis 32:27

Isra'ila

Masu fassara zasu iya ƙara wani dan bayani mai cewa "sunan Isra'ila na nufin 'yayi gwagwarmaya da Allah.'" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

tare da mutane

A nan "mutane" na nufin mutane gaba ɗaya

Genesis 32:29

Ya ce, "Me yasa kake tambaya sunana?"

"Ya ce, ' Me yasa kake tambayar sunana?"' Wannan tambayar da bata buƙatar amsa an yi ta ne domin ta bada mamaki, tsokaci da sa Yakubu yin binbini akan abin da ya faru tsakanin sa da wancan mutumin da yayi gwagwarmaya da shi. AT: "Kada ka tambayeni suna na!" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

Feniyel

Masu fassara zasu iya ƙara wani dan bayani mai cewa "sunan Feniyel na nufin 'fuskar Allah.'" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

fuska da fuska

"fuska da fuska" na nufin mutum biyu na ganin juna a zahiri, a kusa.

kuma rayuwata ta kuɓuta

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "duk da haka ya barni da rai" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

Genesis 32:31

Shi ya sanya har wa yau

Wannan ya canza labarin zuwa matashiya ga zuriyar Isra'ila. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-background)

har zuwa yau

Wannan na nufin harwa yau da marubucin ke rubuta wannan.

jijiyoyin kwankwaso

Wannan na nufin tsokar da ke hade ƙashin kwankwaso da mahadar sa

mahadin kwankwaso

"ƙugu"

yayin gocewar

"yayin ƙoƙarin"