Wannan kalmar an yi amfani da ita ne a nuna tsaiko a cikin labarin. A nan marubucin ya fara bayyana sabon sashe na labarin.
A nan "maganganun" na nufin abin da suke faɗi. AT: "Yakubu ya ji cewa 'ya'yan Laban sun ce" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)
'Ya'yan Laban na yaya abin saboda sun yi fushi. AT: "duk abin da Yakubu ya dauka na mahaifin mu ne" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-hyperbole)
Waɗannan jimla guda biyun na ma'anar abu ɗaya ne. Na biyun na bayana fuskar Laban ne. AT: "Yakubu ya lura cewa Laban baya jin daɗinsa kuma" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-parallelism)
"mahaifin ku Ishaku da kakan ku Ibrahim"
Yakubu ya aika a kira Rahila da Liya su same shi a fili inda yake tare da tumaki"
Za'a iya bayyana wannan ajimloli biyu. AT :"a garkensa. Ya kuma ce masu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-sentences)
"Na lura mahaifinka baya farin ciki da ni yanzu"
Kalmar "kun" na nufin Rahila da Liya. AT: "Ku ma da kanku ku san yadda na bautawa mahaifinku da dukka karfina" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-you)
"ya yi mani ƙarya" ko "baya yi mani adalci ba"
"abin da ya ce zai biya ni"
Ma'anonin zasu iya zama 1) illa a fili (UDB) ko 2) ya sa Yakubu ya sha wuya a kowacce hanya.
"Dabbobi masu dabbura-dabbura"
"garken suka haifi"
"dabbobi masu zãne"
"Ta haka ne Allah ya ba da dabbobin mahaifinku a gare ni"
Yakubu ya ci gaba da ba wa matansa labari, Liya da Rahila.
"Lokacin barbara"
A nan "dabbobin" na nufin matan awakin. AT: "barbara da matan awakin na dabbobin" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)
"masu zãne ne, da kyalloli, da masu ɗigo"
Ma'anonin zasu iya zama 1) Allah da kansa ya bayyana a siffar mutum, ko 2) ɗaya daga cikin yan saƙon Allah ya bayyana. Tunda ba'a fahimci jimlar ba, ya fi sauki a fasara shi da "mala'ikan Allah."
"sai na amsa"
"I, ina jinka" ko "I, menene?" Duba yadda aka fassara wannan a Farawa 22:1.
Mala'ikan Allah ya ci gaba da yin magana ga Yakubu.
Wannan wata hanya ce ta cewa "kalli sama." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)
A nan "dabbobin" na nufin matan awakin. AT: "barbara da matan awakin na dabbobin" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)
"masu zane da dabbura-dabbura"
Yakubu ya kwara mai a kan ginshiƙin domin ya miƙa shi ga Allah. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-symaction)
"ƙasar da aka haife ka"
Wannan ba yana nufin sunyi magana tare ba. Yana nuna sun yarda da juna.
Rahila da Liya sunyi amfani da tambaya su tabbatar da cewa babu wani abu da ya rage mahaifinsu ya bayar. AT: "Babu sauran abinda ya rage da zamu gada wurin mahaifin mu!" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)
Sun yi amfani da tambaya su nuna fushin su kan yadda mahaifin su yake yi masu. Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "mahaifin mu ya maishe mu kamar bare maimakon yaya!" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)
Za'a iya bayyana wannan. AT: "ya sayau da mu don ribar sa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)
Laban yana amfani da kuɗin da ya kamata ya ba 'ya'yansa mata gaba ɗaya ana magana da shi kamar dai shi dabbar daji ce wacce ta ci kuɗin kamar abinci. AT: "ya gama amfani da kuɗinmu gaba ɗaya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)
"na mu ne da 'ya'yanmu"
A nan "yanzu" ba tana nufin "a wannan lokacin ba" amma ana amfani da shi ne don jawo hankali ga bayanai masu mahimmanci da zasu biyo baya.
"ku yi duk abin da Allah ya ce kuyi"
Yakubu ya dauki dukan 'ya'yansa. An anbaci yayan sa ne domin sune magadan sa. AT: "ya'yansa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)
"Ya kora dukkan dabbobinsa" A nan "dabbobinsa" na nufin dukan dabbobin gidansa.
"har da sauran dabbobin da ya samu lokacin da yake Fadan Aram"
"Ya tafi aƙsar Kan'ana inda mahaifinsa yake"
"Lokacin da Laban ya tafi don yanke gashin hisan tumakinsa"
Wannan na nufin Kogin Yuferatis.
"yayi tafiya zuwa"
"tsauninkan Giliyad" ko "tsaunin Giliyad"
Al'adar Yahudawa ce su fara ƙirga ranar tafiya a matsayin ranar farko. AT:"kwana biyu bayan sun barshi"
Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT:"wani ya faɗawa Laban" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)
Yakubu kadai aka ambata domin shine shugaban iyalin. A bayyane yake cewa iyalin sa sun tafi tare da shi. AT:"Yakubu ya gudu da matansa da 'ya'yansa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)
"sai Laban ya ɗauki"
"ya bi Yakubu"
Laban yayi tafiyar kwana bakwai do ya taras da Yakubu.
"ya same shi"
Kalmar "sai" an yi amfani da ita anan domin nuna alamar canji daga labarin zuwa gabatarwa gama da Laban. AT: "a daren nan Allah ya zo wurin Laban a mafarki" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-background)
Jimlar "mai kyau ko mara kyau" an yi amfani da su ne da nufin "komai." AT: "kada ka ce wani abu domin ka hana Yakubu tafiya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-merism)
Kalmar "yanzu" an yi amfani da ita anan domin nuna alamar canji daga labarin zuwa gabatarwa akan Yakubu da Laban. AT: "Lokacin da Laban ya taras da Yakubu, Yakubu ya kafa rumfarsa a ƙasar tudu. Laban shi ma ya kafa sansani tare da danginsa a ƙasar tudu ta Giliyad" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-background)
Laban yayi magana kan ƙoƙarin Yakubu na daukar iyalin sa su koma ƙasar Kan'ana kamar Yakubu ya dauke su a matsayin kamammun yaƙi kuma yana matsa masu su tafi tare da shi. Laban na yayatu saboda yayi fushi yana kuma son Yakubu ya yadda cewa yayi laifi domin abin da yayi. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-simile da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-hyperbole)
"gudu a asirce"
"da farin ciki"
Kayan bushe-bushen na nufin kaɗe-kaɗe. AT: "tare da kaɗe-kaɗe" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)
a bin kiɗa ne mai kai kamar ganga da za'a iya bugawa tare da kuma ƙarafuna zagaye da ke bada amo idan an girgiza shi (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-unknown)
A nan "jikoki" sun ƙunshi jikoki maza da mata. AT: "na yi sumbar sallama ga jikokina" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-gendernotations)
"Yanzu kayi aikin wawanci"
Wannan ba wai yana nufin "wannan lokacin ba,"amma an yi amfani da shi ne don jan hankali ga amfanin abin da ya biyo baya.
Kalmar "kai" na nufi duk wanda suke tare da Yakubu. AT: "Ina da isassun mutanen da zasu cutar da kai" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-you)
"ka" na nufin Yakubu kaɗai. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-you)
A nan "gidan" na nufin iyali. AT: "ka zauna gida tare da mahaifi da sauran iyali" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)
"gumaka na"
"na gudu a asirce saboda na ji tsoro kuma na yi tunanin za ka karɓe 'ya'yanka mata da ƙarfi daga gare ni"
Ana iya bayyana wannan a cikin tsari mai kyau. AT: "zamu kashe du wanda ya saci allolinka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-litotes)
Kalmar "mu" na nufin dangin Yakubu da ya haɗa da dangin Laban. Dukan dangin zasu kula su tabbatar cewa komai na tafiya dai-dai. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-inclusive)
"ka tantance abin da ke naka tare dani ka ɗauka"
Wannan ya canza daga labari zuwa matashiya akan Yakubu. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-background)
Wannan na nufin Zilfa da Bilha
"bai sami gumakan sa ba"
Kalmar "ashe" anyi amfani da ita ne don nuna canji daga labarin zuwa matashiya akan Rahila. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-background)
wuri ne a bayan raƙumi da mutum ke hawa
Kiran wani "shugabana" hanya ce ta girmama shi.
"domin ba zan iya tsayawa a gabanka ba"
Wannan na nufin lokaci a wata da mace ke zubar da jini daga mahaifarta. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-euphemism)
"Yakubu ya cewa Laban"
Jimlar "menene laifi na" da "menene zunubi na" na nufin kusan abu ɗaya. Yakubu na tambayar Laban ya faɗa masa abin da yayi ba dai-dai ba. AT: "Me nayi ba dai-dai ba da zaka taso mini haka?" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-parallelism)
A nan kalmar "da zafi" na nufin Laban ya tunkari Yakubu da hanzari da nufin ya kama shi. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)
"Me ka samu da yake kayan gidanka?"
A nan kalmar "mu" na nufin dangin Yakubu da na Laban. AT : "Ka fito da duk abin da ka samu gaban danginmu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-inclusive)
A nan "mu biyun" na nufin Yakubu da Laban. Jimlar "su shara'anta mu" na nufin a sansance mai gaskiya a cikin wata rashin jituwa. AT: "zasu shara'anta tsakanin mu biyun" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-inclusive)
Yakubu ya ci gaba da magana ga Laban
"shekaru 20" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)
macen tumaki
Wannan na nufin basu taɓa ɓarin ciki ko haifar mataccen da ba.
Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "Lokacin da naman jeji ya kashe daya daga cikin dabbobin ka ban kawo maka ba" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)
Ga Yakubu don ƙidaya matattun dabbobin Laban a matsayin asara daga garken nasa an yi maganarsa kamar yana da nauyi da zai ɗauka a kafaɗunsa. AT: "Maimakon na kirga ta a matsayin asara daga garkenku, sai na dauke ta a matsayin asara daga garkena" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)
Shan wahala cikin yanayin zafi da sanyi an bayyana shi kamar yanayin dabba cde da ke cin Yakubu. AT: "Ina tare da dabbobin ka da rana zafi da dare cikin sanyin dusar ƙanƙara" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)
Yakubu ya ci gaba da magana da Laban
"shekaru 20 na karshe" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)
"shekaru 14" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)
"Ka canza abin da ka ce zaka biya ni sau goma." Duba yadda aka fasara "lada na" a Farawa 31:7.
Yakubu na magana kan Allah ɗaya ne ba uku ba. AT: "Idan ba domin Allah na mahaifina, Allah na Ibrahim, da wanda Ishaku ke tsoro, yana tare dani ba"
A nan kalmar "mahaifi" na nufin iyaye, Ishaku.
A nan kalmar "tsoro" na nufin "tsoron Yahweh," wanda ke nufin ka matuƙar girmama shi tare da nuna haka ta wurin yi masa biyayya
Wannan na nufin rashin komai. AT: "ba tare da komai ba" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)
Za'a iya bayyana "tsanantuwa" a matsayin "tsanani." AT: "Allah ya dubi yadda nayi aiki tuƙuru da yadda ka tsananta mini" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-abstractnouns)
Laban yayi amfani da tambaya ya nuna ba abin da zai iya yi. Ana iya fassara wannan tambayar a matsayin sanarwa. AT: "amma, babu abin da zan iya yi don in dawo da yaya na mata da jikokina tare da ni." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)
A nan kalmar "shaida" ba tana nufin mutum ba, amma tana nufin alkawarin da Yakubu da Laban suka yi. Anyi maganar alkawarin kamar mutum ne wanda yana wurin lokacin da suka yi yarjejeniyar aiwatar wa cikin salama ga juna. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-personification)
Wannan na nufin ƙaton dutse aka sa a ƙarshen ta don a yi sheda a wurin da wannan mahimmin abu ya faru
"a ɗora kan yan uwansu"
Cin abinci tare sashi ne na yin alkawarin ga juna. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)
Mai fassara zai iya ƙara dan bayani a ƙasa cewa: "Sunan Yagar Saha Duta na nufin 'tarin shaidu' a yaren Laban." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)
Mai fassara zai iya ƙara dan bayani a ƙasa cewa: "Sunan Galid na nufin "tarin shaidu' a yaren Yakubu. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)
Duwatsu basa shaida kamar mutum a zahirance. AT: "tarin zai zama abin tunawa tsakani na da kai" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-personification)
Mai fassara zai iya ƙara dan bayani a ƙasa cewa: "Sunan Galid na nufin "tarin shaidu' a yaren Yakubu. Duba yadda aka fasara wannan a Farawa 31:45 (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)
Mai fassara zai iya ƙara dan bayani a ƙasa cewa: "Sunan Mizfa na nufin 'wakin gini.'" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)
A nan "ɓace ga juna" na nufin in bama tare. AT: "idan bama tare da juna" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)
A nan "mu" na nufin Laban da Yakubu. AT: "ko da ba wanda ke ganin mu"
"tunawa." Wannan ya ƙara armashi ga abin da aka faɗa a gaba.
Wannan tarin duwatsu zasu zama tuni ne da kuma iyaka ga Laban da Yakubu game da alƙawarin su. Sun yi maganar su kamar mutane shaidu. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-personification)
Ibrahim kakan Yakubu ne. Naho kakan Laban ne. Mahaifin Ibrahim da Naho Tera ne. Ba dukan su ke sujada ga Yahweh ba.
Kalmar "tsoro" na nufin Yahweh, wanda Ishaku ke matukar girmamawa ta wurin yi masa biyayya.
Cin abinci tare alama ce ta yin alƙawari da juna. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)
Aya 55 ita ce ayar farko ta sura 32 a cikin ainihin juya Ibraniyanci, amma ayar sura 31 a yawan ci Littafi Mai Tsarki na wannan lokacin. Mun shawarci a bi tsarin yadda aka shirya Littafi Mai Tsarki na yaren ku.
Wannan na nufin marmarin abu mai kyau zai faru ga wani