Genesis 30

Genesis 30:1

Da Rahila ta ga cewa ba ta haifa wa Yakubu 'ya'ya ba

"Lokacin da Rahila ta fahimci cewa ta kasa daukar ciki"

Ba ni 'ya'ya

"Ka sa ni in yi ciki"

ko in mutu

Rahila tana wuce gona da iri don nuna bacin ranta game da rashin yara. AT: "Zan ji ba ni da daraja kwata-kwata" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-hyperbole)

Fushin Yakubu ya ji ƙuna gãba da Rahila

An yi maganar fushin Yakubu kamar wuta ne. AT: "Yakubu ya yi fushi da Rahila" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

Ina a madadin Allah ne, wanda ya hana ki samun 'ya'ya?

Yakubu ya yi amfani da wannan tambayar ne ya tsauta wa Rahila. Ana iya fassara shi azaman bayani. AT: "Ni ba Allah ba ne, Ba ni ba ne na ke hana ki samun 'ya'ya!" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

Genesis 30:3

Ta ce

"Rahila yace"

wannan baiwata ce Bilha ... in sami 'ya'ya ta wurin ta

A wancan lokacin, wannan hanya ce karɓaɓɓiya ga mace bakarariya ta sami 'ya'yan waɗanda doka za ta iya zama nata. Cikakkiyar ma’anar wannan na iya zama bayyane. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

bisa gwiwoyina

Wannan wata hanyar faɗin cewa ɗan da Bilha ta haifa zai zama na Rahila. AT: "mini" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

Genesis 30:5

haifa wa Yakubu ɗa

"ta haifi ɗa na miji wa Yakubu"

ta kira sunansa

"Rahila ta sanya masa suna"

kira sunansa Dan

Masu fassarar wannan na iya sharinhinta cewa "ma'anar sunan Dan shi ne 'ya shari'anta.'" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Genesis 30:7

Bilha ... sake ɗaukar ciki

"Bilhah ... ta sake samun ciki"

Da kokawa mai girma na yi kokawa da 'yar'uwata

An yi amfani da maganan nan "kokawa na yi kokawa" domin a jadada maganar, an kuma yi maganar koƙarin da Rahila ta yi ta sami 'ya'ya kamar 'yar uwarta, kamar tana fada na jiki ne da Liya. AT: "Na yi fama mai girma domin in sami 'ya'ya kamar babar 'yar uwata Liya" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

Ta kira sunansa Naftali

Masu fassarar wannan na iya sharihinta cewa "ma'anar sunan Naftali shine 'gwagwarmayata.'"

Genesis 30:9

Sa'ad da Liya ta ga

"Lokacin da Liya ta san da hakan"

ta ɗauki Zilfa, baiwarta, ta bayar da ita ga Yakubu a matsayin mata

"ta ba da Zilfa, baiwarta, ga Yakubu a matsayin mata"

Wannan rabo ne!

"Wannan sa'a mai kyau ne"

kira sunansa Gad

Masu fassarar wannan na iya sharihinta cewa "Ma'anar sunan Gad shine 'rabo.'"

Genesis 30:12

kira sunansa Asha

Masu fassarar wannan na iya sharihinta cewa "Ma'anar Asha shi ne 'farin ciki.'" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Genesis 30:14

manta'uwa

Wannan 'ya'yan itace ne da ake cewa ya na ba da karfin ba da 'ya'ya da marmarin kwana da masoyi. AT: "kwayar soyaya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-unknown)

Ƙaramin al'amari ne a gare ki ... miji na?

"Ba ki damu ba ... miji na? Wannan tambaya ne domin tsautawa Rahila.Ana iya fassara wannan tambayar azaman sanarwa. AT: "munin ya yi haka ... miji na.? (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

To zai kwana da ke

"To Yakubu zai kwana" ko "To zan bar Yakubu ya kwana"

Genesis 30:16

da 'ya'yan manta'uwa na ɗana

"don farashin manta'uwa ɗana." Duba ya aka juya "manta'uwa" a Farawa 30:14.

Allah ya ba ni ladana

An yi maganar yadda Allah ya ba Liya lada kamar yadda wani ubangida na biyan ma'aikaci ne da ya yi masa aiki. AT: "Allah ya yi mani sakamako" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

ta kira sunansa Issaka

Masu fassara wannan na iya sharihinta cewa: "Ma'anar sunan Issaka shine 'akwai sakamako.'"

Genesis 30:19

Ta kira sunansa Zebulun

Masu fassara wannan na iya sharihinta cewa: "Ma'anar sunan Zebulun shine 'daraja.'"

kuma kira sunanta Dina

Wannan sunar ɗiyar Liya ce. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Genesis 30:22

Allah ya tuna da Rahila ya kuma saurare ta

Maganar "kira zuwa ga tunani" na nufin tunawa. Wannan baya nufin Allah ya manta da Rahila. Yana nufin ya yi la’akari da bukatarta. AT: "Allah ya duba Rahila, ya kuma ba ta abin da ta ke so" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

Allah ya ɗauke kunyata

Ana magana game da Allah da ya sa Rahila ta daina jin kunya kamar “kunya” wani abu ne da mutum zai iya ɗauka daga wani. Ana iya bayyana kalmar ta "kunya" a matsayin "abin kunya". AT: "Allah ya sa ban daina jin kunya ba" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-abstractnouns)

Ta kira sunansa Yosef

Masu fassara wannan na iya sharihinta cewa: "Ma'anar sunan Yosef shine 'bari ya kara.'" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Yahweh ya ƙara mani wani ɗan

'Ya'ya fari na Rahila daga baiwarta ce Bilha.

Genesis 30:25

Bayan da Rahila ta haifi Yosef

"Da Rahila ta haifi Yosef"

in kuma tafi

"domin in tafi"

ka san hidimar da na ba ka

Yakubu na tunar da Laban shirin da su ka yi (Farawa 29:26). AT: "Ka san na dade ina bauta maka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-abstractnouns)

Genesis 30:27

Idan yanzu na sami tagomashi a gaban ka

Idanu suna wakiltar gani, kuma gani yana wakiltar tunani ko hukunci. AT: "Idan na sami tagomashi a gare ka" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

ta wurin amfani da sihiri na gane

"Na gano ta ruhaniya da sihiri ayyuka"

Ka faɗi ladanka

Ana iya bayyana wannan a bayyane. AT: "Ka faɗa mini nawane zan biya ka domin ka zauna a nan" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Genesis 30:29

yadda dabbobinka suka kasance tare da ni

"lafiyar dabbobinka tun da na fara kiwon su"

kuma sun ƙaru a yalwace

"amma yanzu wadatarka sun karu sun kuma yi girma"

Domin 'yan kaɗan kake da su kafin in zo

"garkenku sun kasance kadan kafin na yi muku aiki"

Yanzu yaushe zan samar wa nawa gidan shi ma?

"Yanzu wani lokaci ne zan fara lura da nawa iyalin?" Yakubu ya yi tambaya ne domin ya jadada cewa shi ma ya na so ya fara tanadi wa iyalinsa. Ana iya fassara wannan tambayar azaman sanarwa. AT: "Yanzu ina so in lura da iyalina!" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

Genesis 30:31

Me zan biya ka

"Me zan iya biya muku" ko "Me zan iya ba ku." Ana iya bayyana wannan a bayyane. AT: "Me zan iya biya muku don ku tsaya ku yi min aiki" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

zan ware daga cikin su duk wasu tumaki dabbare-dabbare da masu ɗigo, da waɗanda ke baƙaƙe daga cikin tumakin, da masu ɗigo da kyalloli daga cikin awakin

"in kuma ware kowani tumaki mai ɗigo, dukka baƙaƙe, da kuma kowani akuya mai ɗigo"

Waɗannan ne za su zama ladana.

"Wannan ne sakamakon zama na a nan"

Genesis 30:33

Amincina zai yi shaida game da ni daga baya

Kalmar nan "aminci" na nufin "gaskiya." Wannan yana magana ne game da mutunci kamar dai mutum ne wanda zai iya ba da shaida game da wani ko kuma game da shi. AT: "Daga baya kuma za ka sani ko na yi maka aminci ko ba haka ba" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-personification)

Duk wadda ba kyalla ba ce ko mai ɗigo daga cikin awaki, da baƙa daga cikin tumaki, duk wadda a ka samu a wurina, a ɗauke shi a matsayin sata

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "Idan ka sami wani akuya mara ɗigo ko tumaki da ba baƙaƙe ka ɗauke su a matsayin sata" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

Bari ya kasance bisa ga maganarka

AT: "Ya kasance yadda ka faɗi" ko "za mu yi kamar yadda ka faɗa" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Genesis 30:35

duk wata mai fari a jikinta

"kowani akuya da ke da fari a jikinta"

bayar da su cikin hannun

"Hannu" a nan na matsayin iko ko kula. AT: "ba 'ya'yansa su kula da su" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Genesis 30:37

ɗanyun tsabgun auduga ... rassan itacen almond ... rassan itacen durumi

Dukka waɗannan itatuwan masu farin katako ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-unknown)

ya kuma fera fararen zãne a kan su, ya sanya fararen itatuwan da ke cikin ƙiraren su bayyana

"ya kuma fera bawon domin fararen zãnen itatuwan su nuna"

kwamamen ruwa

dogayen buɗaɗɗun buɗaɗɗun ruwa don dabbobi su sha

Genesis 30:39

Dabbobin suka yi ta barbara

"Dabbobin suka haifu"

haihuwar 'ya'yai masu zãne, da kyalloli, da masu ɗigo

haifar 'ya'ya masu zãne, da ɗigo"

ya ware nasa dabbobin domin kansa kaɗai

"ya ware dabbobin sa wani gyefe"

Genesis 30:41

a gaban idanun dabbobin

"idanu" a nan na nufi "kalo". AT: "domin dabbobin su kuma kale su" (Dubi: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

a tsakiyar ƙiraren

"a gaban ƙiraren"

dSai ya zama dabbobin marasa ƙarfi na Laban ne, ƙarfafan kuma na Yakubu ne

"Don haka raunanan zuriyar sun kasance na Laban, yayin da zuriyar ta fi ta Yakubu." Kuna iya bayyana wannan har ma a bayyane. AT: "Don haka raunanan zuriya ba su da ratsi ko tabo don haka na Laban ne, yayin da zuriya mafi ƙarfi ke da ratsi ko tabo don haka na Yakubu ne" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Genesis 30:43

Mutumin

"Yakubu"

ya zama wadatacce sosai

"ɓunkasa ƙwarai" ko "ya zama mai arziki sosai"