Genesis 29

Genesis 29:1

mutanen gabas

Wannan na nufin mutanen Fadan Aram, ƙasar na gabancin ƙasar Kan'ana.

kuma, duba, garkunan tumaki uku na kwance a gefen ta

Kalmar "duba" na matsayin alama ne a farkon wani aukuwa a babban labari. Mai yiwuwa harshenku na da wani hanyar yin wannan.

daga waccan rijiyar

"domin daga waccan rijiyar." Wannan maganar na ba da alamar canji ne da ga labarin zuwa bayanin ƙarin haske ne game da yadda makiyaya ke shayar da dabbobin. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-background)

za su yi wa garkunan ban ruwa

"makiyayan za su shayar" ko "masu kulla da tumakin za su shayar"

bakin rijiyar

Anan "bakin" a hanya ce ta nufin buɗewa. AT: "buɗe rijiyar" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

Genesis 29:4

Yakubu yace masu

"Yakubu ya cewa mikiyayan"

'Yan'uwana

Wannan wani hanyar gai da baƙo ne cikin da'a.

Laban ɗan Nahor

Anan "ɗa" na nufin ɗa namiji. Wata ma'ana mai yiwuwa ita ce "Laban jikan Nahor." (UDB)

kuma, duba can, Rahila ɗiyarsa na zuwa tare da tumaki

"Duba! Rahila ɗiyarsa na zuwa da tumaki"

Genesis 29:7

rana tsaka ne

"rana na haske sosai"

da za a tattara garkuna tare

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "domin ka tattara dabbobin" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

a tattara tare

Ma'anar wannan shine a tattarasu a shinge domin da dare. Ana iya bayana ma'anar wannan a fili. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

su yi kiwo

"su ci ciyawa a fili."

Ba za mu iya yi masu banruwa ba

"Dole ne mu jira mu shayar dasu."

sai dukkan garkunan sun tattaru tare

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "sai sauran makiyayan dabbobin sun tattara dabbobinsu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

mu yi wa tumakin banruwa

"sa'annan zamu shayar da tumakin"

Genesis 29:9

ɗan'uwan mahaifiyarsa

"kawunsa"

bakin rijiyar

Anan "bakin" a hanya ce ta nufin buɗewa. AT: "rijiyar" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

Genesis 29:11

Yakubu ya sumbaci Rahila

A tsohuwar Gabas ta Tsakiya, sananniya ce a gaishe da dangi da sumba. Koyaya, ana yin shi tsakanin maza. Idan yarenku yana da kyakkyawar gaisuwa ga dangi, yi amfani da hakan. Idan ba haka ba, yi amfani da abin da ya dace.

kuka da ƙarfi

Yakubu ya yi kuka, domin murna. Ana iya ba da cikaken ma'anar wannan magana a fili. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

dangin mahaifinta

"mai dangantaka da mahaifinta"

Genesis 29:13

Yakubu ya gaya wa Laban dukkan waɗannan abubuwa

"sai Yakubu ya faɗa wa Laban dukka abun da ya gaya wa Rahila"

ƙashina ne da namana

Wannan jumlar tana nufin suna da alaƙa kai tsaye. AT: "dangina" ko "ɗan iyalina" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Genesis 29:15

Kã bauta mani a banza ... dangina ne?

Laban yayi amfani da tambaya ya fifita cewa ya kamata ya sakawa Yakubu don aikin da ya yi masa. Za'a iya fasara wannan tambayar kamar bayani. Za'a iya bayyana wannan da gabagaɗi. AT: "Ya kamata in saka maka domin aikin da kayi mini ko da yike kai dan uwana ne" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-litotes)

Yanzu dai Laban na da

Kalmar "yanzu" an yi amfani da ita anan ne domin alamar canji daga labari zuwa matashiyar bayanin game da Laban da 'ya'yan sa mata. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-background)

Idanun Liya tausasa ne

Ma'anonin zasu iya zama 1) "Idanun Liya tausasa ne" ko 2) "Idanun Liya a fili suke"

Yakubu ya ƙaunaci Rahila

A nan kalmar "kaunaci" na nufin sha'awar jiki tsanin namiji da mace.

Genesis 29:19

maimakon in bayar da ita ga wani mutumin

"maimakon in bayar da ita ga wani mutum"

suka yi masa kamar kwanaki kaɗan

"amma lokacin yayi masa kamar kwanaki kaɗan"

domin ƙaunar da yake yi mata

"domin ƙaunar da yake yi mata" ko "saboda ƙaunar da yake yi mata"

Genesis 29:21

Ka bani matata, domin kwanakina sun kammalu - domin in aure ta

A nan "kwanaki" na nufin dogon lokaci. Jimlar "kwanaki na sun kammalu" za a iya bayyana shi da gabagaɗi. AT:"Ka bani Rahila domin in aure ta, domin na yi maka aikin shekara bakwai!" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

yi biki

"shirya bikin aure." Mai yiwuwa Laban ya sa wasu suka shirya bikin. AT:"ya samu wasu su shirya bikin" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Genesis 29:23

wanda ya kwana da ita

Ya nuna Yakubu bai san yana tare da Liya ba saboda dare yayi baya kuma gani. Cikakkiyar maganar nan a bayyane take. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Laban ya ɗauki baiwarsa Zilfa ... baranyarta

A nan mai rubutun ya bada matashiya game da yadda Laban ya ba da Zilfa ga Liya. Mai yiwuwa ya bada Zilfa ga Liya kafin aure. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-background)

Zilfa

Wannan sunan baranyar Liya ne (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

ashe Liya ce

"Yakubu yayi mamakin ganin Liya kan gado tare da shi." Kalmar "ashe" a nan na nuna Yakubu yayi mamaki da abin da ya gani.

Mene ne wannan ka yi mani

Yakubu yayi amfani da tambaya ya bayyana fushin sa da mamakin sa. AT: "Ba zan iya gaskata cewa kun yi mini wannan ba!" Ana iya fassara wannan tambayar a matsayin sanarwa. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

Ba domin Rahila na bauta maka ba?

Yakubu yayi amfani da wannan tambayar ya bayyana illar wasa da hankalin da Laban yayi masa. Ana iya fassara wannan tambayar a matsayin sanarwa. AT: "Na bauta maka shekara bakwai domin in auri Rahila!" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

Genesis 29:26

Ba al'adarmu ba ce mu bayar

"A iyalin mu ba ma bayar da"

Ka kammala satin amarcin wannan ɗiyar

"Ka kammala satin amarcin Liya"

za mu kuma baka ɗayar

Cikakkiyar ma’anar ana iya bayyana ta a sarari. AT: "sati mai zuwa zamu baka Rahila" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Genesis 29:28

Yakubu ya yi haka, ya kammala satin Liya

"Yakubu yayi abin da Laban ya buƙata, ya gama satin amarcin Liya"

Bilha

Wannan sunan baranyar Rahila ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Yakubu ya kwana da Rahila

Wannan hanya ce ta nuna sun yi dangantakar auratayya a fakaice. AT: "Yakubu ya auri Rahila" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-euphemism)

ya kaunaci Rahila

Wannan na nufin kaunar jiki tsakanin namiji da mace.

Genesis 29:31

ba a ƙaunar Liya

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "Yakubu baya kaunar Liya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

ba'a kaunar

Wannan na fayyace yadda Yakubu ke kaunar Rahila fiye da Liya. AT: "ba'a kaunar ta kamar Rahila!" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-hyperbole)

ya buɗe mahaifarta

Allah ya ba Liya damar ta dauki ciki an bayyana shi kamar an buɗe mahaifarta. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

bata da ɗa

"bata iya ɗaukan ciki"

Liya ta ɗauki ciki ta haifi ɗa

"Liya ta ɗauki ciki ta haifi ɗa"

ta kuma kira sunansa Ruben

Masu fassara zasu iya sa dan bayani da zai ce: "Sunan Ruben na nufin 'duba, ɗa'" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Yahweh ya dubi azabata

Liya na dandana aƙuba domin Yakubu ya yashe ta. Kalmar "azatarwa" za ta iya zama aikatau. AT: "Yahweh ya dubi azabata" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-abstractnouns)

Genesis 29:33

Daga nan ta sake ɗaukan ciki

"Sai Liya ta samu ciki"

ta haifi ɗa

"ta haifi ɗa"

Yahweh ya ji cewa ba a ƙauna ta

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "Yahweh ya ji cewa mai gidana ba ya ƙauna ta" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

ta kira sunan sa Simiyon

Masu fassara zasu iya gara dan bayani da zai ce "sunan Simiyon na nufin 'Ji." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

mijina zai haɗe dani

"mijina zai rungume ni"

na haifa masa 'ya'ya maza uku

"na haifi 'ya'ya maza uku"

a ka kira sunansa Lebi

Masu fassara zasu iya gara dan bayani da zai ce "Sunan Lebi na nufin 'haɗewa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Genesis 29:35

Ta sake ɗaukar ciki

"Liya ta sake daukar ciki"

haifar ɗa

"ta haifi ɗa"

ta kira sunansa Yahuda

Masu fassara zasu iya gara dan bayani da zai ce "Sunan Yahuda na nufin 'yabo." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)