Genesis 28

Genesis 28:1

Tilas ba za ka ɗauki

"kada ka ɗauki"

Ka tashi ka tafi

"tafi yanzu"

Fadan Aram

Wannan wani sunane kuma na yankin Mesofotamiya wanda a yau na ƙasar Iraki. Duba yadda aka juya wannan a Farawa 25:19. (Duba /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

gidan

Wannan na nufin zuriyar wani ne ko 'yan dangin AT: "iyali" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Betuwel

Betuwel shi ne mahaifin Rebeka. Duba yadda ka juya wannan sunan a Farawa 22:20. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

mahaifin mahaifiyarka

"kakanka"

ɗaya daga cikin 'ya'ya mata

"daga 'ya'ya mata"

ɗan'uwan mahaifiyarka

"kawu"

Genesis 28:3

Muhimmin Bayani:

Ishaku ya ci gaba magana da Yakubu

sa ka yi 'ya'ya ka kuma ruɓanɓanya

Kalmar nan "ninka" ta bayyana yadda Allah zai sa Yakubu ya yi 'ya'ya. AT: "ba ka 'ya'ya da yawa da zuriyar" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-doublet)

Bari ya baka albarkar Ibrahim, gare ka, da zuriyarka a bayanka

Wannan yana magana ne game da albarkar wani kamar wata ni'ima abu ce da mutum zai iya bayarwa. AT: Allah ya albarkace ka da zuriyarka kamar yadda ya albarkace Ibrahim" ko "Allah ya ba ka da zuriyarka abin da ya alkawartar wa Ibrahim" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-abstractnouns)

domin ka iya gãdon ƙasa

An yi maganar yadda Allah zai ba Yakubu da zuriyarsa ƙasar kamar wani ɗa ne da ke gãdan kuɗi da mallaka a wurin mahaifinsa. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

ƙasa inda ka ke zama

"ƙasar da ka kasance a ciki"

wadda Allah ya ba Ibrahim

"wadda Allah ya alkawatar wa Ibrahim"

Genesis 28:5

Betuwel

Betuwel mahaifin Rebeka ne. Duba yadda ka fassara wannan a cikin Farawa 22:20. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Genesis 28:6

Muhimmin Bayani:

Labarin ya canja daga Yakubu zuwa Isuwa

Yanzu

Ana amfani da wannan a nan domin sa alamar canji daga labarin zuwa bayanin ba da haske game da Isuwa. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-background)

ka ɗauki mata

"ya ɗauki mata wa kansa"

Ya kuma ga cewa Ishaku ya albarkace shi

"Isuwa ya ga cewa Ishaku ya riga ya albarkace Yakubu"

Tilas, ba za ka ɗauki mata

"ka da ka ɗauki"

matan Kan'aniyawa

"'ya'ya mata na Kan'ana"

Genesis 28:8

Muhimmin Bayani:

Wannan na ci ga ba da ba da ƙarin haske game da Isuwa.

Isuwa ya ga

"Isuwa ya ga ne"

matan Kan'aniyawa ba su gamshi Ishaku mahaifinsa ba

"mahaifinsa Ishaku bai amince da matan Kan'ana ba"

Sai

"Sabili da haka"

bayan ga matan da ya ke da su

"a haɗe da matan da ya ke da su"

Mahalat

Wannan sunan ɗaya a cikin 'yar Isma'ila. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Nebayot

Wannan sunan ɗaya daga cikin 'ya'yan Isma'ila maza (Dubi: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Genesis 28:10

Muhimmin Bayani:

Labarin ya koma game da Yakubu

Ya iso dai-dai wani wuri ya kuma tsaya wurin dukkan dare, saboda rana ta fãɗi

"Ya iso wani wuri, sai ya zauna a dukkan dare domin rana ta fãɗi"

Genesis 28:12

Ya yi mafarki

"Yakubu ya yi mafarki"

an kafa bisa duniya

"karshen da ke taɓa kasa"

kai cikin sama

"Wannan na nufi wurin da Allah ya ke

Duba

Kalmar "duba" a nan na jawo hankali zuwa bayanin ban mamaki da ke zuwa a gaba.

Yahweh ya tsaya a bisansa

Ma'ana mai yiwuwa 1) "Yahweh na tsaye a saman hanyar hawan bene" ko 2) "Yahweh na tsaye a gaba da Yakubu"

Ibrahim mahaifinka

Ma'anar "mahaifi" a nan shi ne "kaka." AT: "Ibrahim kakanka"

Genesis 28:14

Muhimmin Bayani:

Allah ya ci gaba da magana da Yakubu a mafarki.

Zuriyarka za su zama kamar ƙurar ƙasa

Allah ya kwatanta yawan zuriyar Yakubu da ƙurar ƙasa domin ya jadada girmar yawan su. AT: "Za ka sami zuriya fiye da abun da za ka iya kirgawa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-simile)

kuma za ka bazu nesa zuwa yamma

Anan kalmar "ka" a nan na nufin mutum ɗaya ne, amma a nufin zuriyar Yakubu ne. Ana magana da Yakubu shi kadai domin shi ne kan iyalin. AT: "zuriyarka kuma zasu bazu zuwa yamma" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-synecdoche)

za ka bazu

Ma'anar wannan shine mutanen za su wuce iyakar ƙasarsu su mamaye yankin ƙasar.

zuwa yamma, zuwa gabas, zuwa arewa, zuwa kuma kudu

Ma'anar wannan maganar maganar shi ne "a kowani gyefe." AT: "a kowani gyefe" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-synecdoche)

Ta wurin ka da ta wurin zuriyarka dukkan iyalan duniya za su yi albarka

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "Zan albarkaci dukka iyalin duniya ta wurin ka da zuriyarka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

gama ba zan barka ba. Zan yi dukkan

"gama ba zan barka ba sai na yi dukka"

Zan kiyaye ka

"zan kiyaye ka daga matsala" ko "Zan kare ka"

Zan sake kawo ka cikin wannan ƙasa

"Zan sa ke kawo ka wannan ƙasar"

Genesis 28:16

gidan Allah ... ƙofar sama

Maganar "ƙofar sama" na bayana cewa wannan wurin ne a shigar "gidan Allah" da "shigar idan Allah ya ke." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-doublet)

Wannan ne ƙofar sama ce

Ana maganar shigar inda Allah ya ke kamar wani masarauta da ke da ƙofa wadda wani ke buɗe wa mutane su shiga cikin. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

Genesis 28:18

ginshiƙi

Wannnan ginshiƙin na tunawa ne, wato wani babban dutsen a aka kafa.

ya zuba mai a kansa

Aikata wannan na nuna cewa Yakubu ya ƙebe ginshiƙin ga Allah. Cikakkiyar ma'anar wannan bayanin za a iya bayyana a sarari. AT: "zuba mai a kai domin ya ƙeɓe ginshiƙin ga Allah" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-symaction da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Betel

Masu fassarar wa na iya sharihinta cewa "Ma'anar sunanBetel shi ne 'gidan Allah."

Luz

Wannan sunan wani birni ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Genesis 28:20

ya yi wa'adi

"ɗau alkawari da Allah"

Idan Allah zai ... Yahweh zai zama Allah na

Yakubu yana magana da Allah a cikin mutum na uku. Ana iya bayyana wannan a cikin mutum na biyu. AT: "Idan za ka ... sai kai, Yahweh, za ka zama Allahn da zan bauta wa" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-123person)

wannan hanya da na ke tafiya

Wannan na maganar tafiyar Yakubu ne zuwa nema mata, ya kuma koma gida. AT: "a wannan tafiya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

ba ni gurasa in ci

Anan "gurasa" na wakiltar kowani abinci. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-synecdoche)

gidan mahaifina

Anan "gida" na wakiltar iyalin Yakubu. AT: "ga mahaifina da sauran 'yan iyali" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

tsarkakakken dutse

Wannan na nufin cewa dutsen na alamar inda Allah ya bayyana mishi kuma zai kasance inda mutane za su bauta wa Allah. AT: "gidan Allah" ko "wurin Allah"