Genesis 27

Genesis 27:1

idanun sa ba ya gani sosai

Wannan yana magana game da kusan makaho kamar idanun fitila ne kuma haske ya kusan fita. AT: "ya kusa makance" (Dubi: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

Ya ce masa

"ya kuma cewa Isuwa"

Gani nan

"Ina nan" ko "Ina sauraro." Duba yadda zaka fassara wannan a cikin Farawa 22:1.

Ya ce

"Sai Ishaku yace"

Duba nan

Maganar "duba nan" na jadadda abin da ke zuwa a gaba. AT: "saurare ni a hankali" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Ban san ranar mutuwata ba.

Ma'anar wannan shi ne Ishaku ya san cewa ya kusa mutuwa. AT: "Ina iya mutuwa a kowani rana" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

mutuwa

Wannan na nufin mutuwa ta jiki.

Genesis 27:3

Muhimmin Bayani:

Ishaku ya ci gaba da ba da umarni ga babban ɗansa Isuwa.

makamanka

"ƙayan farauta"

kwarinka

Kibiya kwalliya ce ta rike kibiyoyi. AT: "Kibar kibanku" (Dubi: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

yi farauta

"ka yi mini farautar naman jeji"

Ka yi mini dage-dage, irin wanda na ke ƙauna

Kalmar "dage-dage" na nufin abin da ke da dandano mai dadi. AT: "dafa mun naman mai dandano da na ke ƙauna" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

albarkace ka

A zamani Littafi Mai Tsarki, mahaifi kan sa wa 'ya'yansa albarka na musamman.

Genesis 27:5

Rebeka ta ji lokacin da Ishaku ke magana da Isuwa ɗansa

"Rebeka ta ji Ishaku yana magana da ɗansa Isuwa"

Isuwa ya tafi ... ya kawo

Ana iya kara kalmar "sai" domin a nuna cewa Rebeka na wa Yakubu magana domin abin ta ji ne, kuma lokacin da ta ke masa magana Isuwa ya tafi. AT: " Sa'ad da Isuwa ya tafi ... ya kawo," (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-connectingwords)

da Isuwa ɗansa ... ɗanta

Isuwa da Yakubu dukkasu 'ya'yan Ishaku da Rebeka. Ake kira su "ɗansa" da "ɗanta" domin a jadada cewa ɗaya a cikin iyayan na son ɗayan ɗa fiye da ɗayan.

Ka farauto mini nama ka shirya mini dage-dage domin in ci in albarkace ka a gaban Yahweh kafin mutuwata

Wannan ambaton ne a cikin zance. Ana iya bayyana shi azaman zance na kai tsaye. AT: "Ya ce da Isuwa ya 'farauto naman jeji, ya kuma shirya nama mai dandano da ya ke ƙauna.' Ishaku zai albarkaci Isuwa a gaban Yahweh, kafin ya mutu. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-quotesinquotes da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-quotations)

kawo mini nama

"kawo mini naman jejin da ka farauto"

shirya mini abinci mai dandano

"dafa mini nama mai dandano da na ke so."

Genesis 27:8

Muhimmin Bayani:

Rebeka ta yi magana da karamin ɗanta Yakubu.

Yanzu

Ma'anar wannan ba shi ne "a wannan lokaci" ba, an yi amfani da shi ne domin a jawo hankali zuwa maganar da ke zuwa.

ka yi biyayya da muryata kamar yadda zan umarce ka

Rebeka tace "muryata" a nufin abin da ta ke faɗa. AT: "Ka yi mini biyayya waje aikata abin da na faɗa ma ka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

zan kuma shirya dage-dage mai daɗi da su domin mahaifinka, kamar yadda ya ke ƙauna

Kalmar "dage-dage" na nufin wani abu ne da ke da dandano mai daɗi. Dubi yadda aka juya makamacin wannan jimlar a Farawa 27:3.

Za ka kai shi wurin mahaifinka

"Sai ka kai wa mahaifinka"

domin ya ci ya albarkace ka

"bayan ya ci sai ya albarkace ka"

kafin ya mutu

"kafin mutuwarsa"

Genesis 27:11

ni kuma sulɓi ne

"Ni mutum da jiki mai santsi" ko " ba ni da gargasa"

na kuma zama mayaudari a gare shi

"zai kuma yi tunani cewa ni makaryaci ne" ko "zai san cewa ina yaudarar shi ne"

Zan jawo wa kaina la'ana ba albarka ba

An yi maganar sa la'ana ko albarka kamar su wani abu ne da ake iya sa a bisan wani. AT: "Ta dalilin haka kuma, zai la'ance ni, ba albarkace ni ba" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

Genesis 27:13

Ɗana, bari duk wata la'ana ta auko mini

"bari la'anarka ya kasance a gare ni, ɗa na." AT: "bari mahaifinka ya la'ance ni a maimakonka, ɗa na" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

yi biyayya da muryata

Rebeka tace "muryata" don nufin abin da take faɗa. AT: "yi abun da na faɗa maka" ko "yi mini biyayya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

kawo su wurina

"kawo mini ɗan akuya"

Genesis 27:15

ta sa fatar 'yan awaki a hannunsa

fatar akuyan na nan da gashin a kai.

Sai ta sa dage-dagen mai daɗi da gurasar da ta shirya a hanun ɗanta Yakubu

"Ta ba wa ɗanta Yakubu dage-dagen da ta shirya da gurasa"

Genesis 27:18

ya ce

"mahaifinsa kuma ya ce" ko "Ishaku ya amsa" (UDB)

Gani nan

"I, ina saurara" ko " na am, mene ne?" Duba yadda ka fassara wannan a Farawa 22:1.

Na yi kamar yadda ka ce da ni

"Na yi abin da ka mini in yi"

sauran abin da na farauto

Kalmar "farauto" na nufin namomin jeji da wani ya farauto ya kashe. Duba yadda aka fassara "farauto" a Farawa 27:3.

Genesis 27:20

Ya ce

"Yakubu amsa"

kawo su wurina

Wannnan karin magana na nufin cewa Allah ne ya sa wanna ya faru. AT: "taimake ni in yi nasara wurin farauta (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

ko kai ɗana ne Isuwa ko ba haka ba

"in kai asalin ɗana ne Isuwa"

Genesis 27:22

Yakubu ya je wurin Ishaku mahaifinsa

"Yakubu ya maso wurin Ishaku mahaifinsa'

Muryar kam ta Yakubu ce

Anan Ishaku yayi magana game da muryar Yakubu kamar wakiltar Yakubu. AT: "muryarka kamar na Yakubu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Amma hannayen na Isuwa ne

Anan Ishaku yayi maganar hannayen Isuwa a matsayin wakiltar Isuwa. AT: "amma hannayenka na kamar na Isuwa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Genesis 27:24

ya ce

Ishaku ya yi wannan tambayar kafin ya albarkace ɗansa. AT: "Amma Ishaku ya tambaya" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-events)

ci abin da ka farauto

Kalmar "farauto" na nufin naman jeji da mutane ke yin farauta su kuma kashe. Duba yadda aka juya "farauto" a Farawa 27:5.

ya kuma sha

"Ishaku ya kuma sha"

Genesis 27:26

ya sunsuni ƙamshin suturarsa ya albarkace shi

Ana iya bayana a fili cewa suturar na ƙamshin na Isuwa. AT: "ya sunsuna suturarsa, su ka kuma yi ƙamshi kamar suturar Isuwa, sai Ishaku ya albarkaceshi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

ya kuma sunsuna

"Ishaku kuma ya sunsuna"

ya albarkace shi

"ya kuma sa masa albarka." Wannan na nufin yadda mahaifi ke sa wa 'ya'yansa albarka cikin hanya na ƙwarai.

Duba

Ana amfani da kalmar "duba" a bayyananniyar ƙarin magana da ke da ma'anar "gaskiya ne." AT: "Gaskiya, ƙamshin ɗana" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

da Yahweh ya sawa albarka

Anan kalmar "mai-albarka" na nufin cewa Yahweh ya sa kyawawan abubuwa sun faru ga filin kuma ya zama mai amfani. AT: "da Yahweh ya sa shi ya wadata" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

Genesis 27:28

Muhimmin Bayani:

Wannan albarkar Ishaku ne. Ya na tunanin cewa da Isuwa ya ke magana, amma da Yakubu ya ke magana.

ba ka

A nan "ka" na nufin Yakubu ne kadai. Amma albarka zai bi har zuriyar Yakubu. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-you da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-synecdoche)

raɓar sama

"raɓar" shi ne digon ruwa wanda yake fitowa akan tsiro cikin dare. Ana iya bayyana wannan a bayyane a cikin fassarar. AT: "raɓa da dare daga sama domin ba wa abinci gona ruwa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

ƙasa mafi dausayi

Ana maganar ƙasa mai kyau domin amfanin gona kamar ƙasar na da ƙiba ko arziki. AT: "ƙasa mai kyau domin abinci gona" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

ya ba ka hatsi da ruwan Inabi mai yawa

Idan "hatsi" da "giya" ba a san su ba, ana iya bayyana wannan gaba ɗaya. AT: "abinci and abin sha da yawa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Genesis 27:29

kai ... na ka

Anan waɗannan karin magana suna ɗaya ɗaya kuma suna nufin Yakubu. Amma albarkar ta shafi zuriyar Yakubu. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-you da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-synecdoche)

'yan'uwanka maza ... 'ya'yan mahaifiyarka maza

Ishaku na sa Yakubu albarka, amma yana nufi har ma da zuriyarsa da zasu mulkance zuriyar Isuwa da kuma zuriyar sauran 'yan'uwan da mai yiwuwa Yakubu ya ke da su. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-synecdoche)

'ya'yan mahaifiyarka maza kuma su rusuna maka

"'ya'yan mahaifiyarka maza kuma rusuna maka"

Duk kuma wanda ya la'ance ka ya zama la'annanne

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "Allah ya la'ance duk wanda ya la'ance ka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

duk wanda ya albarkace ka ya zama mai albarka

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "Allah ya albarkace duk wanda ya albarkace ka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

Genesis 27:30

ya fita daga wurin mahaifinsa

"ya fita daga rumfar mahaifinsa Ishaku"

farautar ɗanka

"ɗanka" a nan wata hanya ne cikin da'a da ya ke nufin abinci da ya shirya. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-123person)

albarkace ni

Wannan na nufin yadda mahaifi ke sa wa 'ya'yansa albarka cikin hanya na ƙwarai.

Genesis 27:32

ya ce da shi

"ya ce da Isuwa"

Ishaku ya gigice

"Ishaku ya fara rawan jiki"

Genesis 27:34

ya yi kuka da baƙinciki matuƙa

baƙin cikin Isuwa na kamar an ɗanɗana wani abu ne marasa daɗi. AT: "ya yi kuka da karfi" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

ya karɓe albarkarka

Wannan ƙarin magana ne mai ma'anar cewa Yakubu ya karɓi da ke na Isuwa. AT: "Na albarkace shi a maimakon ka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

Genesis 27:36

Ashe ba haka ya sa aka ba shi suna Yakubu ba?

Isuwa ya yi amfani da tambaya ya jadada fushinsa da Yakubu. AT: "Sunar Yakubu ne ya dace da ɗan'uwana!" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

Yakubu

Masu fassarar na iya sharihinta cewa "ma'anar sunar Yakubu shi ne "ya riƙe diddige." Sunan kuma na kamar sunar da ke ma'ana "ya yaudare" a harshen asalin.

ya karɓe ... albarka

Wannan yana magana ne game da matsayin ɗan fari kamar abu ne wanda mutum zai iya ɗauka. AT: "Ya yaudare ne, na ba shi ka shi biyu daga gadon da yakamata in karɓa a matsayin ɗan fari!" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

yanzu ya karɓe albarkata

An yi maganar albarka kamar wani abu ne da mutum ke iya karɓa. AT: "yanzu ya yaudare ka wajen sa masa albarka a maimako na" (Dubi: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

Ba ka rage wata albarka domina ba

Isuwa ya san cewa ba zai yiwu ba mahaifinsa ya albarkace shi da abubuwa da albarkace Yakubu da su ba. Isuwa na tambaya ko akwai wani abu da Ishaku zai ce da shi, wadda bai ambata ba a sa'ad da ya ke albarkace Yakubu.

Me kuma zan yi maka, ɗana?

Ishaku ya yi tambaya domin ya jadada cewa ba shi da wani abu kuma da zai iya yi. AT: "Ba wani abu kuma da zan iya yi maka!" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

Genesis 27:38

Ko albarka ɗaya ba ka rage mini ba mahaifina?

Ana iya bayyana wannan a cikin tsari mai kyau. "Maihaifina, ka na da ko albarka ɗaya domina"

Genesis 27:39

ce masa

"ce da Isuwa"

nisa daga wadatar duniya

Wannan karin magana ne da ke nufin ƙasa mai kyau. AT: "nesa da ƙasa mai kyau" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

naka ...kai

A cikin Farawa 27: 39-40 waɗannan karin magana ɗaya ne kuma suna nufin Isuwa, amma abin da Ishaku ya ce ya shafi zuriyar Isuwa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-synecdoche).

raɓar sararin sama

"raɓar" shi ne digon ruwa wanda yake fitowa akan tsiro cikin dare. Ana iya bayyana wannan a bayyane a cikin fassarar. AT: "raba da dare daga sama domin ba wa amfanin gona ruwa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Ta wurin takobinka za ka rayu

A nan "takobi" na nufi hargitsi. AT: "Za ka yi fashi da kisan mutane kafin ka sami abun da ka ke bukata na zaman rayuwa" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

za ka kawar da karkiyarsa daga wuyanka

Wannan na magana game da wani da ke da maigida kamar ikon maigidan a kan mutumin wani karkiya ne da mutum ya ɗauka. AT: "za ka yantar da kanka daga mulkin shi" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

Genesis 27:41

Isuwa ya ce a cikin zuciyarsa

A nan "zuciyarsa" na wakiltar Isuwa da kansa. AT: "Isuwa ya ce wa kansa" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-synecdoche)

kwanakin makokin mahaifina sun kusa

Wannan na nufin iyakar kwanakin da mutum ke makoki idan wani ɗan iyali ya mutu.

aka faɗa wa Rebeka kalmomin da babban ɗanta Isuwa ya faɗa

"kalmomi" a nan na matsayin abin da Isuwa ya faɗa. AT: "Sai wani ya faɗa wa Rebeka game da shirin Isuwa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

Duba

"Saurara" ko "Mayar da hankali"

ta'azantar da kansa

"yana sa kansa ya ji daɗi"

Genesis 27:43

Yanzu

Ma'anar wannan ba wai "a wannan lokaci" ne, amma an yi amfani da shi domin a jawo hankalin ga muhimmin maganar da ke zuwa.

gudu wurin Laban

"ma za ka bar nan, ka kuma ta fi wurin Laban"

na ɗan lokaci

"na wani lokaci"

sai fushin ɗan'uwanka ya huce

"sai ɗan'uwanka ya huce da fushinsa"

fushin ɗan'uwanka ya huce daga gare ka

Ba a yin magana da fushi yanzu kamar fushin ya juya zuwa wata hanyar dabam daga mutumin. AT: "har sai ya daina fushi da kai" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

Don me zan rasa ku dukka a rana ɗaya?

Rebeka ta yi amfani da tambaya ta jadada damuwarta. AT: "ba na so in rasa ku dukka a rana ɗaya!' (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

Genesis 27:46

Na gaji da rayuwa

Rebeka namagana haka domin ta jadada yadda take jin haushin matan Hittiyawa da Isuwa ya aura. AT: "Ina cike da baƙin ciki" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-hyperbole)

'ya'yan Het mata

"waɗannan matan Hittiyawa" ko "zuriyar Het"

'yanmata irin waɗannan mataye, waɗansu daga cikin 'yan matan ƙasar

Maganar "'ya'yan ƙasar" na nufin matan ƙasar. AT: "kamar waɗannan matan da su ke zama a wannan ƙasar" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

wanne abu ne mai kyau zai zama a rayuwata?

Rebeka ta yi amfani da tambaya ta jadada yadda baƙin ciki zai zama idan Yakubu ya aure matan Hittiyawa. AT: "Rayuwata za ta munana!" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)