An yi amfani da wannan kalmar ne anan domin a nuna sabon sashi na labarin
"an yi yunwa" ko "an yi wata yunwa"
Za ka iya fayyace ƙasar da wannan ke nufi. AT: "a ƙasar da Ishaku da iyalin sa suke rayuwa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)
Kalmar "a kwankin" na nufin lokacin da Ibrahim ya rayuwa. AT: "wanda ya faru a kwanakin rayuwar Ibrahim" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)
Yahweh ya fara magana da Ishaku
"ya bayyana ga Ishaku"
Abin da aka saba faɗi ne barin ƙasar alƙawari kamar "ficewa" zuwa wani wuri. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)
"domin a gare ka da zuriyarka ne zan bayar da ƙasashen"
"zan tabbatar da alƙawarin dana yi wa Ibrahim mahaifinka"
Yahweh ya ci gaba da magana ga Ishaku
"Zan sa zuyirarka ta zama da yawa"
Wannan na magana kan yawan zuriyar Ishaku kamar yawan taurarin sama. Duba yadda aka fasara wannan a Farawa 22:15. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-simile)
Wannan na nufin duk abin da muke gani a sama, har da rana, wata, da taurari.
Za'a iya bayyana wannan da gabagaɖi. AT: "Zan albarkaci dukkan ai'ummai duniya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)
Jimlar "ya yi biyayya da murya ta" da "ya kiyaye dokokina,da farillaina, da shari'una da ka'idodina" na nufin kusan abu ɗaya. AT: "Ibrahim ya yi biyayya gareni tare da yin duk abin da na umarce shi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-parallelism)
A nan "murya" na nufin Yahweh. AT: "biyayya gare ni" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)
Ishaku ne kadai aka ambata domin shi ne shugaban iyalin, amma dukan iyalin sa na tare da shi. AT: "Don haka Ishaku da iyalinsa ya zauna a Gerar" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)
A nan "tsoro" na nufin rashin tabbas da mutum ke fuskanta lokacin da ya fahimci wani hatsari a gare shi ko wasu. "Ya ji tsoro ya ce"
"domin ya dauƙi Rebeka"
Kalmar "ya duba" ta nuna abin da Abimelek ya gani ya bashi mamaki"
Ma'anonin zasu iya zama 1) yana taɓa ta kamar yadda maigida ke taɓa matar sa ko 2) yana dariya tare da magana da ita yadda maigida ke magana da matar sa.
Mai yiwuwa Abimelek ya aiki wani ya faɗawa Ishaku cewa ya son ganin sa. AT: "Abimelek ya aiki wani ya kirawo Ishaku wurin sa" (Duba: fighs_metonymy)
Wannan na nufin magana a baka cikin wata baka. Za'a iya cewa magana a fakaice. AT: "Don me ka ce, ita 'yar'uwata ce'?" ( /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-quotesinquotes da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-quotations)
"don ya same ta."
Abimelek yayi amfani da wannan tambaya don ya ƙalubalanci Ishaku. AT: "Da baka yi mana haka ba!" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)
Wannan na nufin sa wani ya zama mai laifi kamar "laifi" wani abune da ake ɗorawa wani. AT: "da kuma ka jawo mana laifi na ɗaukar matar wani" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)
A nan "mu" na nufin Abimelek da mutanen sa. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-exclusive)
A nan "taɓawa" na nufin a taɓa mutum ta hanyar da zai cutar da shi. AT: "duk wanda ya cutar da mutumin nan" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)
Mai yiwuwa Abimelek yayi tunanin Faɗawa wani ya kashe duk wanda zai cutar da Ishaku ko Rebeka. Za'a iya bayyana wannan da gabagaɗi. AT: "Zan kashe shi" ko "Zan umarci mutane na su kashe shi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)
Wannan ya fara wani sabon sashi na labarin. Ya canza daga bayani kan yadda Ishaku ke kiran Rebeka yar'uwar sa, ya fara da faɗin yadda Ishaku ya zama da arziƙi har Filistiyawa na masa baƙin ciki.
"a Gerar"
Wannan na nufin "ninki ɗari na abin da ya shuka." Za'a iya fasara ta da "hatsi mai yawa" (UDB). (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)
"Ishaku ya zama da arziƙi" ko "ya yi arziƙi"
"ya dinga bunƙasa sosai har sai da ya yi girma sosai"
Wannan zai kunshi harma da awaki. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)
A nan "iyalai" na nufin ma'aikata ko barori. AT: "barori da yawa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)
A nan wannan kalmar ba tana nufin "a wannan lokacin" ba. Tana nuna inda abin da ake magana a labarin ya fara. Za'a iya fasara ta da kalmar "Don" a nuna cewa wannan sakamako ne na abin da ya faru a Farawa 26:12. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-connectingwords)
Jimlar "a kwanakin" na nufin lokacin mutum. AT: "lokacin Ibrahim, mahaifin sa, yana rayuwa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)
Ma'anonin zasu iya zama 1) wannan wani abune da zai matsawa Ishaku da Iyayensa su tafi. AT: "Sai Abimelek yace" ko "A karshe Abimelek yace" ko 2) Abimelek ya yi wannan kudiri domin ya lura mutanen sa na kishi tare da nuna zafin rai ga Ishaku. AT: "Saboda haka sai Abimelek yace" ( /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-connectingwords)
"kana da ƙarfi fiye da yadda muke"
Ishaku kaɗai aka ambata saboda shi ne sugaba, amma iyalinsa da barorin sa sun tafi tare da shi. AT: "Saboda haka Ishaku da iyalin sa suka tafi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)
A nan "Ishaku" na nufin Ishaku da barorin sa. AT: "Ishaku da barorin sa sun tona" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)
"Wadda barorin Ibrahim suka tona"
Jimlar "a kwanakin" na nufin lokacin mutum. AT:"lokacin Ibrahim, mahaifin sa, yana rayuwa" . Duba yadda aka fassara wannan a Farawa 26:15 (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)
Wannan ne dalilin da ya sa Ishaku ya tona su. Wasu hanyoyin da za'a iya fsasara wannan ya ƙunshi 1) Tun sa'adda wannan ya faru da farko, wannan jimlar zata iya zuwa kafin jimlar game da Ishaku ya tone su, kamar a UDB, ko 2) Wannan jimlar zata iya farawa da "Ishaku yayi wannan saboda Filistiyawa sun ɓata su." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-events)
"sun cika su da ƙasa"
Wannan na nufin ruwan da suka samo lokacin da suke tona sabuwar rijiya. Ya nuna cigaba da fitar sabon ruwa mai daɗ. AT: "sabon ruwa" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)
"mutanen da ke kiwon dabbobi"
A nan "namu" na nufin makiyayan Gerar (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-exclusive)
Masu fassarar zasu iya ƙara dan bayani a ƙasa "Sunan Esek na nufin "rikici" ko "gardama." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)
"Sai barorin Ishaku suka sake haƙa " (UDB)
"makiyayen Gerar suka yi gardama da makiyayen Ishaku"
"saboda haka Ishaku ya dada"
Masu fassarar zai iya bada dan bayani da zai ce "sunan Sitna na nufin 'banbanta' ko 'ƙalubalanta.'" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)
Masu fassarar zai iya bada dan bayani da zai ce "Sunan Rehobot na nufin 'bada dama domin' ko 'wurin da ba komai.'" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)
Ishaku na magana game da kansa da iyalinsa.
A nan "haura" mai yiwuwa na nuna tafiya arewa. Ka furta ya haura yadda harshen ka ya bada dama. AT: "Ishaku ya haura daga can zuwa Biyasheba"
"zai ruɓanɓanya zuriyarka" ko "za sa zuriyar ka ta ƙaru kwarai"
"saboda barana Ibrahim" ko ka mai da ma'anar a zahirance. AT: "saboda na yiwa bawa na Ibrahim alkawari hakan zan yi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)
Zaka iya gane dalilin da ya sa Ishaku ya gina bagadi. AT: "Ishaku ya gina bagadi a can domin yin hadaya ga Yahweh" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)
A "kira" na nufin yin addu'a ko sujada. A nan "sunan" na nufin Yahweh. AT: "Ya yi addu'a ga Yahweh" ko "yin sujada ga Yahweh" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)
"ya je wurin Ishaku"
Wannan sunan namiji ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)
Ma'anonin zasu iya zama 1) "abokin Abimelek" ko 2) "Masu ba Abimelek shawara."
Wannan sunan namiji ne. Duba yadda aka fasara shi a Farawa 21:22. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)
Wannan na nufin Abimelek, Ahuzat, da Fikol. Ɗayan su ne ya yi magana, sai sauran su ka amince. Ba wai sun yi maganar tare ne a lokaci guda ba. AT: "ɗayan su ya ce"
"mun sa ni" ko "muna da tabbaci"
"don haka muna so muyi yarjejeniya"
Ana iya sa wannan kamar sabon jimla. "Kirki ne kadai mu ka nuna maka"
Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "Yahweh ya sa maka albarka" (Dubi: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)
Ci da sha tare na cikin alkawari tsakanin juna. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)
"su" na nufin "Abimelek, Ahuzat, da Fikol." AT: "dukkan su su ka ci" (UDB)
"suka farka da asuba"
"Don haka, ya kira rijiyar Shiba." Masu fassarar na iya sharihinta cewa "Kalmar Shiba na kamar kalmar da ke ma'anar 'rantsuwa'". (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)
Masu fassarar na iya sharihinta cewa "ma'anar Biyasheba na iya zama "rijiyar rantsuwa" ko "rijiyar bakwai." (Duba Farawa 21:31)
Yawancin Farawa 26 game da Ishaku ne. Waɗannan ayoyin suna magana ne akan babban ɗansa Isuwa.
"40" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)
"ya yi aure." Ana iya bayana a fili cewa ya aure mata biyu. AT: "ya auri mata biyu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)
Waɗannan sunayen matan Isuwa ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)
Waɗannan sunayen maza ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)
"zuriyar Het" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)
Anan "su" na nufin Yudit da Basemat. Ana maganar baƙin ciki kamar wani abu ne da wani ke ba wa wani dabam. AT: "Suka sa Ishaku da Rebeka baƙin ciki" ko "Ishaku da Rebeka suka yi baƙin ciki sabili da su" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)