Wannan na nufin mutane da ake ambata a aya 2-4.
"Ishaku ya gãji dukka mallakar Ibrahim." Dai-dai ne uba ya raba tarin dukiyarsa lokacin da ya tsufa, ba ya bari bayan mutawarsa wasu su yi ba.
"Ibrahim ya rayu shekaru 175" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)
"Ibrahim ya yi nunfashinsa na ƙarshe sanan ya mutu." "nunfashinsa na ƙarshe" da "mutuwa" na da ma'ana ɗaya ne. AT: "Ibrahim ya mutu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-doublet)
Waɗannan magana biyun na nufin abu ɗaya ne, kuma ana jadadda cewa Ibrahim ya yi rayuwa har ya tsufa. AT: "Da ya yi rayuwa sosai har ya tsufa kwarai kuwa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-doublet)
Ma'anar wannan shi ne, bayan Ibrahim ya mutu ruhun sa ya je inda ruhun 'yan'uwansa wadda su ka mutu kafin shi. AT: "Ya sadu da 'yan iyalinsa wadda su ka riga su ka mutu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)
Ifron na da fili a Makfela da kogon da ke filin. Ibrahim ya saya filin a wurin Ifron.
"Ibrahim ya saya wannan fili"
Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "Su ka bizne Ibrahim" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)
Ma'anar wannan sunar shine "rijiyar rayayye wanda ya ke kallo na." Duba yadda aka juya sunan wannan wurin a Farawa 16:13, (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)
Ana amfani da wannan kalmar a Turanci wajen gabatar da sabon sashin labari da kuma ba da bayani game da Isma'ila.
Za'a iya bayyana wadannan a jimla guda biyu. "Wadannan sune sunayen 'yayan Isma'ila goma sha biyu. Sun jagoranci ƙabilun da aka basu sunna su, kuma kowannen su na da garinsu da ƙauyukansu."
"12" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)
A nan kalmar "yarima" na nufin mutanen ke shugabanci ko jagorancin ƙabilu, ba wai yana nufin su yayan sarakuna bane.
"Isma'ila ya rayu shekaru 137" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)
Kalmar "yayi numfashinsa na ƙarshe" da "ya mutu" na nufin kusan abu ɗaya. AT: "mutu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-doublet)
Wannan na nufin bayan Isma'ila ya mutu, an kai jikin sa wurin yan'uwansa da suka mutu kafin shi. Za'a iya bayyana wannan da gabagaɗi. AT: "ya sadu da iyalin sa da suka riga suka mutu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)
"zuriyar sa ta zauna"
"tsakanin Habila da Shur"
Habila na wani wuri ne a Hamadar yankin Larabawa. Duba yadda aka fassara wannan a Farawa 2:11 (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)
"ya fuskanci"
Ma'anonin zasu iya zama 1) "basu zauna da salama a tsakanin su ba" (UDB), ko 2) "sun gujewa sauran danginsu."
Wannan jimlar ta gabatar da labarin zuriyar Ishaku na cikin Farawa 25:19-35:29. AT: "Wannan shi ne labarin zuriyar Ishaku, ɗan Ibrahim" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)
"shekaru 40" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)
"lokacin da ya auri Rebeka"
Betuyel mahaifin Rebeka ne. Duba yadda aka fassara wannan sunan a Farawa 22:20. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)
Wannan wani suna ne na yankin Mesofotamiya, wadda take a daidai wurin da ƙasar Iraƙi ta yanzu take. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)
"bata iya dauƙar juna biyu"
A bayyane yake cewa Rebeka ta yi juna biyu dauke da yara biyu a lokaci ɗaya. AT: "Rebeka, matarsa, ta sami juna biyu na 'yan biyu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)
"yaran na cikin ta na bugun junan su" ko "Yaran ka yi turereniya a cikin ta"
Rebeka na da juna biyu dauke da 'yan biyu. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)
"Ta je ta tambayi Yahweh game da haka." Ba cikakken bayanin inda ta je. Mai yiwuwa ta je wani keɓeɓɓen wurin ne ta yi addu'a, ko ta je wani wuri ne domin miƙa hadaya.
"yace da Rebeka"
Wannan yaren waƙa ne. Idan harshen ka na da tanadi domin waƙa, zaka iya yin amfani da wannan a nan. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-poetry)
A nan "al'umma biyu" na nufin yara biyun. Kowannan yaro zai zama uba ga al'umma. AT: "al'umma biyu zata fito daga yan biyun da ke tare da ke" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)
A nan "mutane biyu" na matsayin yara biyun. Kowanne zai zama uba ga al'umma. Za'a iya fasara wannan da aikatau. AT: "yayin da kika haifi wadannan yaran zasu yi gaba da juna" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)
Ma'anar Wannan sune 1) "babban yaro zai bautawa ƙaramin yaro" ko 2) "zuriyar babban zata bautawa zuriyar ƙaramin." Idan zai yiwu, a fassara shi yadda mutane zasu fahimci kowacce ma'ana.
Kalmar "gashi" a nan na ƙara jadada abun zai biyo. "haƙĩƙa"
Ma'anar Wannan sune 1) fatar sa ja ne da gashi mai yawa a jikinsa, ko 2) yana da jar gashi a jikin sa. AT: "ja da kuma gashi kamar tufafin gashi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-simile)
Masu fassara na iya ƙara sharihinta cewa "Sunar Isuwa na kamar kalmar da ke nufin "gargashi."
"riƙe bayar tafin kafar Isuwa"
Masu fassara na iya ƙara sharihinta cewa "Ma'anar sunar Yakubu shi ne "ya riƙe diddigen."
"shekaru 60" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)
"zama mai farauta, ya na kashe dabbobi domin abinci"
"mutum mai salama"
Wannan na magana game da lokaci kamar wani abu ne wanda za'a iya kashi. AT: "ya kasance a runfofi yawacin lokaci" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)
An yi amfani da wannan a ba da alaman canjin magana, zuwa ba da ƙarin haske game da Ishaku da Rebekah. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-background)
Ma'anar kalmar "ƙauna" a nan shine "rahama" ko "fĩfĩta"
"domin ya na cin namomin da Isuwa ya harbo" ko "domin a jin dadin naman jeji da Isuwa ke kamowa"
Tunda ya ke wannan shine farkon labari game da wani abu da ya faru a wani lokaci, wasu masu juya wannan na iya farawa a cewa "Wata rana, Yakubu ya dafa" kamar yadda ya ke a UDB.
"shirya taushe" ko "dafa miya." Wannan taushen an shirya shi da wake ne. (Duba: Farawa 25:31)
"ƙarfinshi ya ƙare domin yana jin yunwa" ko Yana jin yunwa"
"ƙarfin na ya ƙare da yunwa" ko "Ina jin yunwa"
Masu fassara na iya sharihinta cewa "ma'anar sunar Idom shine "ja.'"
"damarka ta ɗan fari na gadon mallakar ubanmu" (UDB)
Isuwa ƙara azama a maganar sa domin ya jadada irin yunwan da yake ji. AT: "Ina jin yunwa kamar zan mutu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-hyperbole)
Isuwa ya yi amfani da tambaya domin ya jadada cewa cin abinci ya fi muhimminci mishi da damar ɗan fari. AT: "Gado ba shi da amfani a gare ni idan na mutu da yunwa!" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)
Ana iya ba da gamsashen bayani a fili abun da Yakubu ke so Isuwa ya rantse a kai. AT: "A farko ka rantse mini za ka sayar mun da damarka na ɗan fari" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)
Wannan wani irin wake ne kanana. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-unknown)
"Isuwa ya nuna cewa bai daraja matsayinsa na ɗan fari ba."