Genesis 24

Genesis 24:1

Yanzu

An yi amfani da wannan kalmar ne anan don nuna dan tsaiko a cikin labarin. A nan marubucin ya fara bayyana sabon sashi na labarin.

Sa hannunka a ƙarƙashin cinyata

Ibrahim na shirin roƙon bawansa ya rantse zai yi wani abu. Sa hannun sa ƙarƙashin cinyar Ibrahim na nufin yana da tabbacin zai yi abin da ya rantse zai yi. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-symaction)

zan sa ka ka rantse

Za'a iya bayyana wannan a matsayin umarni. AT: "rantse" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-imperative)

rantse da Yahweh

Kalmar "rantse da" na nufin yin amfani da sunan wani ko wani abu a matsayin ginshiƙin ko ikon da aka kafa rantsuwar. "yi mani alkawari da Yahweh a matsayin sheda"

Allah na sama da kuma Allah na duniya

"Allah na sama da kuma Allah na duniya." Kalmomin " sama" da "ƙasa" an yi amfani da su tare ne domin nuna duk abin da Allah ya halitta. AT: "Allahn komai da komai na sama da ƙasa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-merism)

Sama

Wannan na nufin wurin da Allah yake

mata daga cikin Kan'aniyawa

"mata daga cikin Kan'aniyawa" ko "daga Kan'aniyawa." Wannan na nufin matan Kan'aniyawa.

da nake zama a cikinsu

"da nake zama a cikinsu." A nan "nake" na nufin Ibrahim da iyalin sa da barorinsa. AT: "da nake zama a cikinsu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Amma zaka

Za'a iya furta wannan a matsayin umarni. AT: "rantse da cewa za ka tafi" ko "amma tafi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-imperative)

dangi na

"iyalina"

Genesis 24:5

yaya kenan

"me zan yi idan"

ba za ta biyo ni ba

"ba za ta biyo ni ba" ko " ta ƙi mu dawo tare"

Ko ya zama tilas in mayar da ɗanka zuwa ƙasar da ka baro

"Ko in mayar da ɗanka zuwa ƙasar da ka baro"

Ka tabbata cewa ba ka komar da ɗana can ba

Jimlar "ka tabbbata" ta ingiza umarnin da ya biyo baya. "Ka tabbata cewa ba ka komar da ɗana can ba" ko "Ka da ka yarda ka komar da ɗana can ba"

wanda ya ɗauko ni daga gidan mahaifina

A nan "gida" na nufin mutanen da iyalinsa. AT: "wanda ya ɗauko ni daga gidan mahaifina da sauran iyalinsa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

ya yi mini tabbataccen alƙawari

"ya yi tabbataccen alƙawari gare ni"

cewa, 'Ga zuriyarka zan bada wannan ƙasa'

Wannan magana ce cikin baka a wata baka. Za'a iya furta wannan a fakaice. AT: "ya cewa ga zuriyarka zan bada wannan ƙasa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-quotesinquotes da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-quotations)

zai aiko mala'ikan sa

Kalmar "zai" da "sa" na nufin Yahweh

Genesis 24:8

Muhimmin Bayani:

Aya 8 ci gaba ne na ka'idodin da Ibrahim ya ba bawansa

Amma in matar ba ta son ta biyo ka

"Amma in matar ba ta son ta biyo ka." Ibrahim na amsa tambayar bawansa daga Farawa 24:5. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-hypo)

ka kuɓuta daga rantsuwata

"ka kuɓuta daga rantsuwata da ka yi mani." Rashin cika alkawari an bayyana shi kamar mutum ya kujewa wani abin da ya kamata. AT: "ba sai ka yi mini abin da ka rantse mini ba" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

ya sa hannunsa a ƙarƙashin cinyoyin Ibrahim shugabansa

Wannan na nuna tabbbacin zai yi abin da ya rantse. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-symaction)

ya yi masa rantsuwa

"ya yi masa rantsuwa"

game da wannan al'amari

"game da bukatar Ibrahim" ko "zai yi abin da Ibrahim ya buƙace shi"

Genesis 24:10

ya tafi. Haka nan ya ɗauki

Jimlar ta fara da "haka nan ya ɗauki" ta bada ƙarin bayani game da abin da bawan ya ɗauka lokacin tafiya. Ya tattarasu kafin ya tafi.

Hakanan ya ɗauki duk waɗansu kyaututtuka da suka kamata daga wurin shugabansa

Wannan na nufin ya ɗauki abubuwa masu kyau da yawa da shugaban sa ke so ya baiwa iyalin matar.

ya ɗauka ya tafi

"ya kama hanya ya tafi" ko " ya kama hanya yayi tafiyar sa"

birnin Nahor

Mai yiwuwa ma'anoni su ne 1) "birnin da Nahor ya zauna" ko 2) "birnin da ake kira Nahor." Idan zaka fasara shi ba tare da zaɓar ma'ana ba, ka iya yin haka. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Ya sa raƙuman suka kwakkwanta

Rakuma dabbobi ne masu bisa da dogayen ƙafafu. Ya sa suka kwankwanta a kan ƙasa. "Ya sa raƙuman sun kwankwanta ƙasa"

rijiyar ruwa

"rijiyar ruwa" ko "rijiya" (UDB)

ɗibar ruwa

"samo ruwa" (UDB)

Genesis 24:12

Sai ya ce

"Sai bawan ya ce "

ka ba ni nasara a yau ka kuma nuna amintaccen alƙawarinka ga shugabana Ibrahim

Za ka iya furta wanna da kalmar "ta wurin." Wannan ya nuna a zahiri yadda bawan ya ke son Allah ya cika alkawarin sa. AT: "ka nuna amintaccen alƙawarinka ga shugabana Ibrahim ta wurin bani nasara yau" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-connectingwords)

ka ba ni nasara

"ka ba ni nasara." Bawan na so ya samarwa yaron Ibrahim mata nagari. Kalmar "nasara" zata iya zama aikatau. AT: "ka taimake ni don inyi nasara" ko "ka bani ikon yin abin da ya kawo ni nan" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-abstractnouns)

ka nuna amintaccen alƙawarinka ga shugabana Ibrahim

Wannan aminci ne saboda alkawarin da Allah ya yi da Ibrahim. Kalmar "amintaccen" za'a iya cewa "ka yi aminci." AT: "ka nuna amintaccen alƙawarinka ga shugabana Ibrahim" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-abstractnouns)

Duba

A nan kalmar "duba" ta ƙara armashi ga abin da ya biyo.

ƙoramar ruwa

"ƙoramar ruwa" ko "rijiya"

'yan'matan mutanen birnin

"'yan'matan birnin"

Ka sa abin ya kasance kamar haka

"Ka sa abin ya kasance kamar haka" ko "bari haka ya kasance"

In na ce da budurwar ina roƙon ki ki saukar da abin ɗiban ruwanki domin in sha

Wannan magana ce a bakã cikin wata bakã. Za'a iya bayyana hakan a fakaice. AT: "In na ce da budurwar ina roƙon ki ki saukar da abin ɗiban ruwanki domin in sha" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-quotesinquotes da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-quotations)

ina roƙon ki ki saukar da abin ɗiban ruwanki

Matan suna ɗaukar abin ɗibar ruwa a kafaɗa. Sai ta saukar kafin ta ba namiji ruwa in ya bukata.

abin ɗibar ruwa

Wata matsakaiciyar gora ce da ake yi da yinbu domin ajiye ko zuwa abu ruwa-ruwa

ka nuna amintaccen alƙawarinka ga shugabana

Kalmar "amintacce" za a iya cewa "zama da aminci". AT: "ka nuna amintaccen alƙawarinka ga shugabana" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-abstractnouns)

Genesis 24:15

ya zamana kafin

Wannan jimlar an yi amfani da ita ne a nuna inda aikin ya fara. idan harshenka na da wata hanyar yin wannan, zaka iya duba yiwuwar amfani da shi a nan.

Duba

Kalmar "duba" a nan na ankarar da mu muyi la'akari da bayanin banmamaki da zai biyo baya.

Abin ɗibar ruwa

Wata matsakaiciyar gora ce da ake yi da yinbu domin ajiye ko zuwa abu ruwa-ruwa. Duba yadda aka fassara wannan a Farawa 24:12

Rebeka 'yar Betuwel ce ɗan Milka, matar Nahor, ɗan'uwan Ibrahim

"Uban Rebeka ne Betuwel. Iyayen Batuwel ne Milka da Nahor. Nahor ɗan'uwan Ibrahim ne"

Betuwel

Betuwel uba ne wurin Rebeka. Duba yadda aka fassara wannan suna a Farawa 22:20. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Nahor

Wannan sunan namiji ne. Duba yadda aka fassara sunan a Fassara 11:22. ( Duba : /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Milka

Milka matar Nahor ce kuma uwa ga Betuwel. Duba yadda aka fasara wannan suna a Farawa 11:29. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Sai ta tafi ƙoramar ... ta hauro

Ƙoramar na ƙasa da inda bawa ya tsaya

Genesis 24:17

ya same ta

"ya sami budurwar"

sam mani ruwa

"dan ruwa kadan"

Abin ɗibar ruwa

Wata matsakaiciyar gora ce da ake yi da yinbu domin ajiye ko zuwa abu ruwa-ruwa. Duba yadda aka fassara wannan a Fawara 24:12

Shugabana

"shugabana". A nan matar ta yi amfani da wannan kalmar bangirman ga mutumin, duk da ba baiwar shi bace.

sai ta yi sauri ta sauke abin ɗiban ruwan ƙasa a hannunta

"sai ta yi sauri ta sauke abin ɗiban ruwan." Tana dauke da abin ɗibar ruwan a kafaɗar ta. Ta saukar da shi domin ta bada ruwa ga baran.

Genesis 24:19

Zan ɗebo ruwa

"zan samo ruwa"

Sai ta yi sauri ta juye abin ɗebo ruwan

"Sai ta yi sauri ta juye abin ɗebo ruwan"

kwami

"kwamin shan ruwa" (UDB). Kwami wani dogon buɗaɗɗen mazibin ruwane wanda ake zubawa dabbobi su sha.

Genesis 24:21

Mutumin

"Baran" (UDB)

dube ta

"ya dubi Rebeka" ko "ya dubi yar budurwar"

domin ya gani

Koyon wani abu akan dube shi kamar gani. AT: "a sani" (UDB) ko "a tabbatar" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

ya ba tafiyarsa nasara

"ya ba tafiyarsa nasara" ko " ya sa tafiyarsa da nasara." Za ka iya bayyana abin da baran ya kudurta. AT: "yana nuna masa wadda zata zama matar Ishaku" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

ko a'a

Kuna iya bayyana cikakken bayanin da aka fahimta. AT: "ko bai yi nasara a tafiyarsa ba" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-ellipsis)

zoben zinariya na hanci mai nauyin rabin ma'auni

"zoben zinariya na hanci mai nauyin giram shida" (UDB). Na'uyin na nuna darajar zoben. AT:"zoben zinariya na hanci mai tsada" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-bweight)

ƙarau guda biyu na azurfa na sawa a dantse wanda ya kai nauyin ma'auni goma

"ƙarau guda biyu na azurfa na sawa a dantse domin ta da yakai giram 110." Nauyin na nuna girma da darajar su. AT: "ƙarau guda biyu na azurfa domin dantse ta" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-bweight)

Ke "yar wane ne

"Wanene mahaifin ki"

ko akwai masauki a gidan mahaifinku

"ko akwai wuri a gidan mahaifinku"

domin mu

Da alamu wadansu mutanen sun tafi tare da baran Ibrahim. A nan "mu" na nufin baran da wadanda suke tafiya tare da shi. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-exclusive

zamu kwana

"mu kwana a nan" ko "mu kwana"

Genesis 24:24

Ta ce

"Rebeka ta ce" ko "budurwar ta ce"

gare shi

"ga baran"

Ni 'yar Batuwel ce ɗan Milka wanda ta haifawa Nahor

"Batuwel ubana ne, iyayen shi kuma sune Milka da Nahor"

muna kuma da ciyawa da abincin dabbobi

An fahimta cewa ciyawa anbincin raƙuma ne. Zaka iya bayyana wannan bayani. AT: "muna kuma da ciyawa da abincin dabbobi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-ellipsis)

domin ku kwana

"domin ku kwana" ko "inda zaku tsaya daren nan"

domin ku

A nan "ku" na nufin baran da waɗanda suke tafiya tare. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-you)

Genesis 24:26

Mutumin

"baran" (UDB)

ya durƙusa

Wannan alama ce ta ƙasƙantar da kai gaban Allah. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-symaction)

bai yashe da alƙawarinsa mai aminci ba da kuma amincinsa ga shugabana

"bai yashe da alƙawarinsa mai aminci ba da kuma amincinsa ga shugabana." Kalmar "amincinsa" da "alherinsa" za su iya zama "zama da aminci da alherinsa." AT: "ya ci gaba da zama da aminci da alherin sa domin alƙawarinsa ga shugabana" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-abstractnouns)

bai yashe da

Za'a iya bayyana wannan da gabagaɗi. AT: "ya ci gaba da nuna" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-litotes)

yan'uwa

"iyali" ko "dangi"

Genesis 24:28

budurwar ta yi gudu ta je ta faɗa wa iyalin gidan mahaifiyarta

A nan "iyalin" na nufin duk mutanen da ke gidan mahaifiyarta. AT: "ta yi gudu ta je ta faɗa wa mahaifiyarta da duk waɗanda suke nan" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

duk abin da ya faru dangane da waɗannan al'amura

"duk abin da ya faru"

Yanzu

An yi amfani da wannan kalmar ne domin nuna dan tsaiko cikin labarin. A nan marubucin ya yi bayani akan Rebeka. Marubucin ya gabatar da dan'uwan ta, Laban, a labarin. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-background da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-participants)

Da ya ga wannnan zobe na hanci ... kuma bayan ya ji duk abin da Rebeka 'yar'uwarsa ta faɗa

Waɗannan abubuwa sun faru ne kafin ya ruga wurin mutumin. Wannan ya nuna dalilin da yasa Laban ya ruga wurin mutumin. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-events)

bayan ya ji duk abin da Rebeka 'yar'uwarsa ta faɗa, "Wannan shi ne abin da mutumin ya ce da ni,"

Wannan zai iya zama magana ce a fakaice. AT: "bayan ya ji duk abin da Rebeka 'yar'uwarsa ta faɗa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-quotations)

duba

"da gaske." Kalmar "duba" a nan ta ƙara armashi ga abin da ya biyo baya.

Genesis 24:31

Zo

"Zo ciki" ko "Shigo"

kai mai albarka na Yahweh

"kai wanda Yahweh ya sawa albarka"

kai

A nan kalmar "kai" na nufin baran Ibrahim. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-you)

Me yasa kake tsayuwa a waje?

Laban yayi amfani da wannan tambaya ya gayyaci baran Ibrahim zuwa gidan sa. Za'a iya juya wannan tambaya a matsayin sanarwa. AT: "baka buƙatar zama a waje." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

Sai mutumin ya zo gidan

Kalmar "ya zo" za'a iya fasara ta a matsayin "ya tafi". (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-go)

ya sauke wa raƙuman kaya

Ba'a fayyace wanda yayi wannan aikin ba. Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "baran Laban ya sauke wa raƙuma kaya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

Sai aka ba raƙuman ciyawa da abincin dabbobi aka kuma tanaɗi ruwa

Wannan bai bayyana wanda yayi aikin ba. Idan ka bayyana wannan a zahiri yi amfani da "baran Laban" a matsayin batun magana. AT: "baran Laban ya ba raƙuman ciyawa da abincin dabbobi, aka kuma tanaɗi ruwa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

domin ya wanke ƙafafunsa ... shi

"ga baran Ibrahim da mutanen da suke tare da shi su wanke ƙafafun su"

Genesis 24:33

Suka kawo

A nan, kalmar "su " na nufin iyalin Laban ko na baran gidan

kawo masa abinci

"kawo abinci ga baran"

sai na faɗi abin da zan faɗa

"sai na faɗi abin da zan faɗa" ko "faɗa maku dalilin zuwa na nan"

ya yi girma sosai

A nan kalmar "ya" na nufin Ibrahim

girma sosai

"ya zama mai dukiya ƙwarai"

Ya bada

Kalmar "ya" na nufin Yahweh

Genesis 24:36

Muhimmin Bayani:

Baran Ibrahim ya ci gaba da magana ga iyalin Rebeka

ta haifi ɗa ga shugabana

"ta haifi ɗa"

ya bayar da ... gare shi

"shugabana ya bashi ... ga ɗan sa"

Shugabana ya sa na rantse, cewa

"Shugabana ya sa na rantse cewa zan yi duk abin da ya buƙaci in yi. Ya ce"

daga cikin 'yanmatan Kan'aniyawa

Wannan na nufin matan Kan'aniyawa. AT: "daga matan Kan'aniyawa" ko "daga Kan'aniyawa"

waɗanda a ƙasarsu na yi gidana

"waɗanda na girma cikin su." A nan "na" na matsayin Ibrahim da duk iyalin sa da barorin sa. AT: "waɗanda tsakanin su na girma" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

ga dangina

"ga dangi"

Genesis 24:39

Muhimmin Bayani:

Baran Ibrahim ya ci gaba da magana ga iyalin Rebeka

in a ce matar ba zata biyo ni ba fa

Wannan abu ne da zai iya faruwa. AT: "in a ce matar ba zata biyo ni ba fa." ko "Me zan yi idan matar ba zata biyo ni?" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-hypo)

anda nayi tafiya a gabansa

Bautawa Yahweh an yi maganar sa ne kamar Ibrahim na tafiya da kasancewar Yahweh. AT: "wanda nake bautawa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

baka nasara bisa tafiyarka

"zai mai da hanyoyin ka da nasara"

cikin dangina

"iyali"

Amma zaka kuɓuta daga rantsuwata in ka zo wurin 'yan'uwana in ba su baka ita ba. To zaka kuɓuta daga rantsuwata

Wannan misalin yanayi ne da Ibrahim bai tsammaci zai faru ba. Mai yiwuwa ma'anar kan zan 1) "Akwai hanya ɗaya tak da zaka iya yantuwa daga rantsuwa ta: Idan ka zo ga dangi na suka ƙi baka ita, to zaka yantu daga rantsuwa ta" ko, 2) ginawa kan aya 40, "Idan ka je wurin iyalin babana ka kuma nemi yarin ya, ka yi abin da na buƙaci kayi ke nan. Idan ba zasu baka ita ba, to zaka yantu daga alkawarin da ka rantse mani." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-hypo)

zaka kuɓuta daga rantsuwata

"zaka kuɓuta daga rantsuwata da ka yi mini." Rashin cika alkawari an bayyana shi kamar mutumin ya yantu daga wani abu da ya daure shi. AT: "ba sai kayi abin da ka rantse mani zakayi ba" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

in ka zo wurin yan'uwa na

Harsuna na amfani da kalmomin zo da tafi dabam-dabam.AT: "idan ka je wurin yan'uwa na" ko "idan ka je gidan yan'uwa na" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-go)

Genesis 24:42

Muhimmin Bayani:

Baran Ibrahim ya ci gaba da yin magana ga iyalin Rebeka

ƙorama

"rijiya"

gani nan a tsaye a bakin ƙorama

Baran ya yi kutse ga abin da yake roƙon Allah yayi ta wurin ankaras da Allah inda yake a tsaye

ka sa budurwar da ta zo ... wato macen da zan ce ... macen da ta ce dani

Baran ya koma wajen bayyana buƙatar sa, kuma yana da abu uku da zai faɗa game da macen da yake da begen zata zo.

ɗiban ruwa

"ta sami ruwa"

abin ɗiban ruwa

Wata matsakaiciyar gora ce da ake yi da yinbu domin ajiye ko zuwa abu ruwa-ruwa. Duba yadda aka fassara wannan a Farawa 24:12

bari ta zama macen

Baran ya gama bayyyana buƙatar sa

Genesis 24:45

Muhimmin Bayani:

Baran Ibrahim ya ci gaba da yin magana ga iyalin Rebeka

magana a cikin zuciyata

An bayyana yin addu'a a cikin zuciyar mutum kamar yin magana cikin zuciya. Kalmar "zuciya" na nufin tunanin sa da zuciyarsa. AT: "addu'a (UDB) ko "addu'a a asirce" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Ku ji

"da gaske" ko "nan take." Kalmar "ku ji" a nan na ankaras da mu ga maida hankali ga bayanan banmamaki da suka biyo.

abin ɗiban ruwa

Wata matsakaiciyar gora ce da ake yi da yinbu domin ajiye ko zuwa abu ruwa-ruwa. Duba yadda aka fassara wannan a Farawa 24:12

sai ta je wajen ɗiban ruwa

Jimlar "je wajen" an yi amfani da ita ne saboda ƙoramar na wani wuri ne ƙasa da inda baran ke tsaye.

ƙorama

"rijiya"

shayar da raƙuman

"ta bada ruwa ga raƙuman"

Genesis 24:47

Muhimmin Bayani:

Baran Ibrahim ya ci gaba da yin magana ga iyalin Rebeka

Yar Betuwel, ɗan Nahor, wanda Milka ta haifa masa

"Betuyel mahaifi na ne. Iyayen sa kuma Nahor da Milka ne"

zobe ... ƙarau

a wannan labarin, duk waɗannan abubuwan an yi sune da zinariya. Duba yadda aka fassara su a Farawa 24:21

na sunkuya

Wannan alama ce ta ƙaskanci wurin Allah. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-symaction)

ya bishe ni a madaidaiciyar hanya

"ya kawo ni nan"

wanda ya bishe ni

Kalmar "bishe ni" zata iya nuna dalilin da yasa baran ya yi sujada ga Allah. AT: "saboda Yahweh ya bishe ni" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-connectingwords)

dangin shugabana

Wannan na nufin Betuyel, yaron ɗan'uwan Ibrahim.

Genesis 24:49

Muhimmin Bayani:

Baran Ibrahim ya ci gaba da yin magana ga iyalin Rebeka

Yanzu kuma

"Yanzu" (UDB). A nan "yanzu" ba tana nufin "nan take ba", amma an yi amfani da ita ne domin jan hankali ga batutuwa masu amfani da suka biyo.

in kuna shirye ku nuna zumunci mai aminci da amana, ku faɗa mini

Yadda zasu nuna aminci da amana a fili ya ke. AT: "ku faɗa mini in kuna shirye ku nuna zumunci mai aminci da amana ga shugabana ta wurin ba shi Rebeka ta zama matar ɗan sa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

kai

Kalmar " kai" na nufin Laban da Betuyel (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-you)

mai aminci da riƙon amana

Waɗannan kalmomi za'a iya bayyana su kamar "aminci da amana."

Amma idan har

Bayanai da aka fahimta ka iya zama a fayyace. AT: "Amma in baku a shirye ku nuna zumunci mai aminci da amana ga shugabana" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-ellipsis)

domin in bi dama ko hagu

Mai yiwuwa ma'anar ta hada da 1) yanke shawarar abin da za'a yi an bayyana shi ne kamar mutum zai juya wani sashin ko wani. AT: "domin in san matakin da zan dauka" ko 2) baran na so ya san ko akwai buƙatar ya tafi wani wurin. AT: "domin in ci gaba da tafiya ta" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

Genesis 24:50

Betuyel

Wannan shine mahaifin Laban da Rebeka

Al'amarin daga Yahweh ya zo

"Yahweh ya sa duk wadannan abubuwa su faru"

ba zamu iya ce maka ya yi kyau ko bai yi kyau ba

Suna cewa basu da yancin yin zaɓi ko abin da Allah yayi mai kyau ne ko mara kyau. AT: "bai kamata mu shara'anta abin da Yahweh ke yi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

Duba

Kalmar "duba" a nan ta ƙara armashi ga abin da zai biyo baya

Rebeka na gabanka

"Ga Rebeka nan"

Genesis 24:52

kalmomin su

"Kalaman Laban da Betuyel." A nan "kalmomi" na a matsayin abin da suka faɗi. AT: "abin da Laban da Betuyel suka ce" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

sai ya sunkuyar da kansa ƙasa

Sunkuyar da kai gaban Allah alama ce ta sujada gare shi. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-symaction)

kayayyaki na zinariya da azurfa

"kayan zinariya da azurfa" ko "kayayyaki da aka yi da zinariya da azurfa "

kyautai masu daraja

"kyautai masu tsada" ko "kyautai masu tamani"

Genesis 24:54

shi da mazajen dake tare da shi

"Baran Ibrahim da mutanen sa"

Suka kwana har gari ya waye

"suka yi barci a wannan dare"

sun tashi da safe

"sun tashi safiya ta gaba"

Ku sallame ni

"ku bar ni in tafi in koma"

waɗansu 'yan kwanaki kamar goma tukuna

"akalla ta ƙara kwana goma"

goma

"10" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)

Bayan nan

"Daga nan"

Genesis 24:56

ya ce

"Baran Ibrahim ya ce"

da su

"ga yan'uwan Rebeka da mahaifiyar ta"

kada ku hana ni

"Kada ku ɓata man lokaci"(UDB) ko "Kada ku sani in jira"

Yahweh ya sa tafiyata ta yi nasara

A nan "tafiyata" na nufi baƙuntar sa. AT:"Yahweh ya sa tafiyata ta yi nasara" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Ku sallame ni

"Ku barni in tafi"

Genesis 24:59

Sai suka aika 'yar'uwarsu Rebeka

"iyalin suka tura Rebeka"

yar'uwarsu

Rebeka yar'uwar Laban ce.AT: "dangin su" ko "yar'uwar Laban"

baranyarta

Wannan na nufin baiwar da ta kula da Rebeka tun tana ƙarama, ta lura da ita tun tana ƙarama, har yanzu tana bauta mata.

yar'uwarmu

Rebeka ba yar'uwa bace ga kowa a iyalin ta. Amma suna kiranta haka su nuna suna ƙaunarta. AT: "Kaunatacciyar mu Rebeka"

muna addu'a ki zama uwar dubun dubbai goma

A nan "uwar" na nufin kakanni. AT: "muna addu'a ki zama uwar dubun dubbai goma" ko "bari ki samu ziri'a mai yawa sosai"

dubun dubbai goma

Wannan na nufin lamba mai yawa ko wadda bata iya ƙirguwa. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)

da ma zuriyarki ta mallaki ƙofar maƙiyansu

Sojoji kan karya ganuwar biranen maƙiyansu su kuma ci mutanen da yaƙi. AT: "bari zuriyarki su yi nasara akan maƙiyanki gaba ɗaya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Genesis 24:61

Sai Rebeka ta tashi, ita da barorinta mata suka hau raƙuma

"Sai Rebeka ta tashi, ita da barorinta mata suka hau raƙuma"

Da haka baran ya ɗauki Rebeka ya yi tafiyarsa

"Ta wannan hanyar baran Ibrahim ya dauki Rebeka tare da shi ya koma inda ya fito"

Yanzu

Wannan kalmar ta kawo canji cikin labarin. Tana magana kan yadda baran ya samo mata, yanzu kuma zata yi magana ka Ishaku

Beyer Lahai Roi

Wannan sunan wata rijiyar ruwa ce a Negeb. Duba yadda aka fasara ta a cikin Farawa 16:13.

Genesis 24:63

Ishaku ya fita domin yin nazari a saura da yammaci

"Da yammacin wata rana Ishaku ya fita filidomin yin tunani." Wannan zai yiwu dogon lokaci ne bayan da baran da Rebeka suka baro gidan iyayenta tunda dole suyi tafiya mai nisa.

Da ya duba tudu, ya hanga, sai ya ga raƙuma na tafe

Kalmar "duba" a nan ta ankaras da mu ga mai da hankali ga bayani mai banmamaki da ya biyo baya, "Da ya duba tudu, ya hanga, yayi mamakin ganin raƙuma na tafe"

Rebeka ta duba

"Rebeka ta duba sama"

sai ta diro daga kan raƙumin

"sai ta sakko daga kan raƙumin da sauri"

Sai ta ɗauki gyale ta yi lulluɓi

"Sai ta ɗauki gyale ta yi lulluɓi ta rufe fuskarta." Wannan alama ce ta bangirma da kamun kai ga mijin da zata aura. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-symaction da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

lulluɓi

yadin tufa da ake amfani da shi a rufe kai, kafaɗa da fuska

Genesis 24:66

ya ɗauki Rebeka, ta zama matarsa

Duka jimlolin na nufin Ishaku ya auri Rebeka. AT: "ya auri Rebeka" ko "ya ɗauki Rebeka, ta zama matarsa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-doublet)

Ishaku ya ta'azantu

Za'a iya bayyyan wannan da gabgaɗi. AT: "Rebeka ta ta'azantar da Ishaku" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)