Genesis 23

Genesis 23:1

Sarai ta rayu tsawon shekaru ɗari da ashirin da bakwai

"Sarai ta yi rayuwa shekaru 127" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)

Waɗannan su ne shekarun Sarai

Wasu juyi basu da wannan maganar. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-doublet)

Kiriyat Arba

Wannnan sunan wani birni ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Ibrahim ya yi makoki da kuka domin Sarai

"Ibrahim ya yi bakin cikin, ya yi kuka domin Sarai ta mutu"

Genesis 23:3

ya tashi ya bar wurin da matarsa ta mutu

"ya tashi ya bar ganga jikin matarsa"

ya'yan Het

Anan "'ya'ya" na nufin 'yan zuriyar da zo ta wurin Het. AT: "zuriyar Het" (UDB) ko "Hitiyawa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

a cikin ku

Ana iya bayana wannan maganar a matsayin wuri. "a ƙasar ku" ko "a nan"

Ina roƙo ku ba ni mallaka

"Sayar mun da fili" ko "Yardar mun in saya wani fili"

matattuna

AT: "mata ta da ta mutu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-nominaladj)

Genesis 23:5

shugabana

An yi amfani da wannan domin a martaba Ibrahim.

yariman Allah

Wannan karin magana ne. Ma'anar wannan mai yiwu shine "mutum mai karfin iko" (UDB) ko "shugaba mai matukan iko." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

matattunka

Ana iya sa wannan a sauki haka "mata." AT: "matarka da ta mutu" ko"matarka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-nominaladj)

inda ka zaɓa a maƙabartunmu

"inda ya fi kyau a maƙabartunmu"

hana maka maƙabartarsa

"hana ka da wurin bizina"

Genesis 23:7

rusuna

Ma'anar wannan shine durƙusawa ƙasa cikin tawali'u domin nuna bangirma da daraja ga wani. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-symlanguage)

wa mutanen ƙasar, ga "ya'yan Het

"ga 'ya'yan Het da suke zama a wurin"

Ifron ... Zohar

Waɗannan sunayen maza ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

kogon Makfela, wadda ya mallaka, wadda ya ke a ƙarshen filinsa

"kogon da ke a ƙarshen filinsa a Makfela"

kogon Makfelah

"kogon da ke Makfelah." Makfelah sunan wani wuri ne. Ifron na da fili a Makfelah, kogon kuma na cikin filin ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

sayar mini da shi a gaban jama'a

"sayar mini da shi a bainar mutane"

zama mallaka

"zama fili na da zan iya amfani da ita a matsayayin nawa"

Genesis 23:10

Ifron kuma na zaune a cikin 'ya'yan Het

Wannan ƙarin haske ne ko bayani game da Ifron. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-background)

a kunnuwan 'ya'yan Het

Ana iya bayyana kalmar ta "ji" a matsayin "sauraro." AT: "domin dukka 'ya'yan Het su ji ni" ko "sa'ad da 'ya'yan Het su na saurara" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-abstractnouns)

duk waɗanda su ka zo ƙofar birninsa

Wannan na bayana su wanene a cikin 'ya'yan Het su ka saurari maganar. AT: "duk waɗanda su ka tataru a ƙofar birninsa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-distinguish)

ƙofar birninsa

A ƙofar birni ne shugabanen birnin ke zama su ɗauki muhimmin shawarwari.

a gaban 'ya'yan mutanena maza

Anan "gaba" na nufin mutanen da suka zama shaidu ne. AT: "da 'yan ƙasana a matsayin shaiduna" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Na ba ka shi domin bizne matacciyarka

"Na ba ka. Ka bizne mataccenka"

Genesis 23:12

sunkuyar da kansa ƙasa

Ma'anar wannan shine durƙusawa ƙasa cikin tawali'u domin nuna bangirma da daraja ga wani. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-symlanguage)

mutanen ƙasar

"mutanen da suke zama a yankin"

Amma in ka na so

Kalmar "amma" na nuna banbancin magana. Ifron na so ya ba wa Ibrahim fili; Ibrahim kuma na so ya biya kuɗin filin. AT: "A'a, In ka yarda" ko "A'a, amma in ka yarda da wannan"

Zan biya kuɗin filin

"Zan ba ka kuɗin filin"

Genesis 23:14

Ina roƙo ya shugabana ka saurare ni

"Ka ji ni, ya shugabana" ko "Ka saurareni mallam"

Ɗan yankin ƙasa na shekel ɗari huɗu menene wannan a tsakanina da kai?

Ifron na nufin cewa tundashike shi da Ibrahim masu arziki ne, shekel 400 ƙaramin kuɗi ne. AT: "kuɗin filin shekel ɗari hudu ne. Wannan ai ba komai ba ne a gare ni da kai." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

shekel ɗari hudu na azurfa

Wannan a kimanin kilo 4.5 na azurfa. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-bweight)

ya auna shekel ɗari huɗu kamar yadda Ifron ya ambata

Ibrahim ya auna wa Ifron dai-dai shekel da ya ambata" ko "Ibrahim ya auna wa Ifron iyakar azurfan"

Ifron ya ambata a kunnuwan dukkan 'ya'yan Het maza

"kimanin azurfa da Ifron ya ambata"

bisa ga mizanin ma'aunin fatake

"amfani da mizanin ma'aunin fatake." Ana iya sa wannan a wa ta sabon jimla. AT: "Ya auna azurfan kamar yadda fatake suke auna wa"

Genesis 23:17

wato da filin da kogon da ke cikinsa, da duk itatuwan da ke cikin filin

Wannan maganar ya bayana abun da marubucin ke ma'ana da "filin Ifron." Ba filin kadai ba, amma har da kogon da itatuwan da ke filin.

an sayar wa da Ibrahim

"Ya zama mallakar Ibrahim bayan ya saye ta shi" ko "zama na Ibrahim bayan da ya saya"

a gaban 'ya'yan Het maza

Anan "gaba" na matsayin yadda mutanen suka zama shaidu. AT: "da mutane Het suna kallo a matsayin shaidu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

duk waɗanda su ka zo ƙofar birninsa

Wannan na magana game da 'ya'yan Het wanda su ka Ibrahim lokacin da ya ke sayan mallakar. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-distinguish)

birninsa

"birnin da ya ke zama." Wannan maganar na nuna cewa Ifron na waccan birnin ne. Ba wai birnin mallakar sa ba ne.

Genesis 23:19

Bayan wannan

"Bayan ya saya filin"

cikin kogon filin

"kogon da ke filin"

filin Makfela

"filin cikin Makfela"

wato Hebron

Ma'ana mai yiwuwa sune 1) Mamre wani suna ne na Hebron, ko 2) A baya ana kira Hebron da sunar Mamre, ko 3) Mamre na ku sa da babban birnin Hebron, shiyasa mutane su ka saba kira Hebron.

miƙa su ga Ibrahim daga 'ya'yan Het maza domin ya zama maƙabarta.

"ya zama mallakar Ibrahim na binza, a sa'ad da ya saye ta daga 'ya'yan Het maza"