"Waɗannan abubuwa" na nufin lokacin yaƙin sarakunan da kuma ceton da Ibram ya wa Lot.
Wannan na nufin cewa Yahweh ya yi magana. AT: "Yahweh ya faɗa saƙonsa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)
Anan "magana" na wakiltar saƙon Yahweh ne. AT: "saƙon Yahweh" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)
Allah yayi amfani da waɗannan kalmomi domin ya bayana wa Ibram halinsa da kuma dagantakarsa da Ibram. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)
"biya." Wani na nufin biyan da wani ya cancanta. mai yiwuwa ma'ana biyu ne 1) "Ni ne kadai ka ke bukata" ko 2) Zan ba ka dukka abin da ka ke bukata."
"Ibram ya ci gaba da cewa, da ya ke ka ba ni"
Kalamar "gashi" na jadada cewa kalmar Yahweh ta sa ke zuwa ga Ibrahim.
Wannan na nufin Eliyaza ne daga Damaskus.
"wanda za ka zama mahaifinsa" ko "asalin ɗan ka." Ɗan Ibram zai zama magajin sa.
'ƙirga taurari"
Kamar yanda Ibram ba zai iya ƙidaya taurari ba, haka nan ba zai iya ƙidaya zuriyarsa ba domin za su kasance da yawa.
Wannan na nufi ya amince cewa abin da Yahweh ya faɗa gaskiya ne.
"Yahweh ya lisafta imanin Ibram a kan adalci" ko "Yahweh ya ɗauke Ibram adali ne domin Ibram ya gaskanta da shi"
Yahweh na tunar da Ibrahim game da abin da ya riga ya yi domin Ibrahim ya san cewa Yahweh na da ikon ba wa Ibram abin da ya alkawatar masa.
"same ta" ko "domin ka mallake ta"
Ibram na tambaya domin ya kara samun tabbaci cewa Yahweh zai ba shi kasar.
"jikin dabbobi da tsunstayen da suka mutu"
"Ibram ya kore tsuntsayen." Ya tabbatar cewa tsuntsaye ba su ci dabbobin da suka mutu ba.
Wannan ƙarin magana ne. AT: "Ibrahim ya yi barci mai zurfi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)
"matsananciyar duhu da ta razanar da shi"
"mamaye shi"
"'yan ƙasan waje" ko "wanda ba 'yan gida ba"
Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "masu ƙasar kuwa za su maishe zuriyarka bayi, su kuma tsananta musu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)
Yahweh ya ci gaba da yi wa Ibram maganar sa'ad da Ibram yana cikin mafarkin.
Anan "hukunta" na nufin abin da zai faru bayan Allah ya yi shari'a. AT: "Zan azabtar" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)
Wannan karin magana ne. AT: "mallaka mai matuƙan yawa" ko "wadatar dukiya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)
Wannan wata hanya ɗabi'a ne na cewa "za ku mutu." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-euphemism)
"za ku tsufa kafin ku mutu, iyalinku kuwa su yi muku jana'iza"
Tsara ɗaya a nan na nufi tsawon shekaru ɗari. "bayan shekaru ɗari huɗu"
"zuriyarka za su sake dawo nan." Zuriyar Ibrahim za su sake komowa ƙasar da Ibram ke zama, da kuma ƙasar da Yahweh ya alkawatar ma sa.
"bai cika ba" ko "sai ya yi muni kafin zan hukunta su"
Allah ya yi wannan domin ya nuna wa Ibram cewa ya na yin yarjejeniya tare shi.
"wuce tsakanin layin naman dabba"
Ta faɗin wannan, Allah na ba da ƙasa wa zuriyar Ibram. Allah na yin haka a wacan lokacin amma zuriyar ba za su shiga ƙasar ba sai bayan shekaru da yawa.
kogin Yuferetis mai girma.
Waɗannan sune sunayen kungiyar mutanen da suke zama a ƙasar. Allah a yardar wa zuriyar Ibrahim su ci nasara yaƙi da waɗannan mutane, su kuma ɗauki ƙasar. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)