Genesis 16

Genesis 16:1

To yanzu

Ana amfani da wannan kalmar a cikin Turanci don gabatar da sabon ɓangaren labarin da bayanan asali game da Sarai. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-background)

baiwa

"baiwa." Wacennan baiwa za ta bauta wa matan gidan.

daga samun 'ya'ya

"daga haifan 'ya'ya"

Na sami 'ya'ya ta wurinta

"Zan ta da iyalina ta wurinta"

Ibram ya saurari muryar Sarai

"Ibram ya yi abin da Sarai ta ce"

ta fara duban uwargijiyarta da raini

"ta raina uwargijiyarta" ko "ta dubi kan ta da daraja fiya da uwargijiyarta"

uwargijiyarta

Ana nufin da Sarai ne a nan. AT: "mai mallakarta" ko "Sarai"

Genesis 16:5

Wannan kuskuren da na yi

"Wannan rashin adalcin da na yi"

saboda kai ne

"hakin ka ne" ko "laifin ka ne"

Na bada baiwata gare ka

Sarai na nufi cewa ya kwana da baiwarta. AT: "Na ba ka baiwa ta domin ka kwana da ita" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-euphemism)

aka sayar da ni a idonta

Wannan na iya zama mai aiki. AT: "ta na kiyayya da ni" ko " ta fara tsane ni" ko "ta dubi kan ta da daraja fiye da ni" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

Sai Yahweh ya shari'anta tsakanina da kai

"Ina so Yahweh ya faɗa ko tsakani na kai wa ye da laifi" ko " Ina so Yahweh ya yanke shawara tsakanin mu biyu wa ya yi daidai. Maganar "shari'anta tsakani" na nufin yanke shawara a kan wanda ya aikata daidai tsakanin su.

Duba

"Saurare ni" ko "Kawo hankalin ki"

ƙarƙashin ikonki

ƙarƙashin izni ki"

Sai Sarai ta takura mata sosai

Sarai ta nuna wa Hajara mumunar hali"

sai ta gudu daga gare ta

"sai Hajara gudu daga gare Sarai"

Genesis 16:7

mala'ikan Yahweh

Ma'ana mai yiwuwa 1) Yahweh ya mayar da kanshi a kamanin mala'ika, ko 2) wannan wani mala'ikan Yahweh ne, ko 3) wannan ɗan saƙo ne daga Allah na musamman (wasu malamai na tunani wai Yesu ne). Tunda shike ba'a fahimci wannan maganar ba, ya fi kyau a juya wannan cewa "mala'ikan Yahweh."

jeji

Yankin jeji da ta je hamada ne. AT: "hamada"

Shur

Wannan sunan wani wuri ne kuduncin Kan'ana da kuma gabacin Masar.

uwargijiyata

Ana nufi da Sarai ne a nan. Uwargiji na da iko a kan baiwarta. AT: "mamalaki." Duba yadda aka fassara "mai mallakarta" a Farawa 16:1.

Genesis 16:9

Mala'ikan Yahweh yace da ita

"Mala'ikan Yahweh yace da Hajara"

Mala'ikan Yahweh

Duba bayanin kula game da wannan jimlar a cikin Farawa 16: 7.

mala'ikan Yahweh yace da ita, "Zan

Sa'ad da ya ce "Zan," yana game da Yahweh ne. A sa'ad da ana fassara wannan maganar, a yi amfani da kalmar "Zan" wa Yahweh kamar yadda mala'ikan Yahweh ya yi.

Zan ruɓanɓaya zuriyarki sosai

"Zan ba ki zuriya ma yawa ƙwarai"

wuce ƙirge

"sosai, da ba wanda zai iya ƙirgawa"

Genesis 16:11

Duba

"Saurara" ko "Kula"

haifi ɗa

"haifuwan ɗa namiji"

za ki kira sunansa

"Za ki kira sunansa." Kalmar "ki" na nufi da Hajara.

Isma'ila, saboda Yahweh ya ji

Masu fassarar wannan na iya sharihinta cewa "ma'anar sunar 'Isma'ila' shine "Allah ya ji.'"

ƙunci

Ta sha ƙuncin da wahala

Zai zama jakin jeji

Wannan ba zagi ba ne. Yana yiwuwa Isma'ila zai kasance da yanci da kuma ƙarfi kamar jakin jeji. AT: "Zai kasance kamar jakin jeji a cikin mutane" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

Zai yi magaftaka da dukkan mutane

"Zai zama maƙiyin kowani mutum"

zai kuma zauna a ware da

Ma'anar wannan na iya zama "zai yi zaman rashin jituwa da wasu."

Genesis 16:13

Yahweh wanda ya yi magana da ita

"Yahweh, domin ya yi magana da ita"

Ko zan ci gaba da gani, ... ni?

Hajara ta yi amfani da tambaya ta nuna mamakin cewa tana nan a raye kodayake ta ga Allah. Mutane na tsammanin cewa zasu mutu in sun ga Allah. AT: "Ina mamaki ina a raye har yanzu, ... ni" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

Saboda haka ake kiran rijiyar Beyer Lahai Roi

Masu fassarar wannan na iya sharihinta cewa ma'anar "Beyer Lahai Roi" ita ce "rijiyar rayaye, wanda yaki gani na." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

tana nan tsakanin Kadesh da Bered

Wannan na nufin cewa marubucin da masu karatu sun san wuri da ake magana a kai. AT: "ba shakka tana tsakanin Kadesh da Bered" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Genesis 16:15

Hajara ta haifar

Ana iya ba da gamsashen bayani cewa Hajara ta dawo wurin Sarai da Ibram. AT: "Sai Hajara ta koma, ta kuma haifi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

sa wa ɗansa suna, wadda Hajara ta haifa

Hajara ta sa wa ɗansa suna" ko "sunar ɗansa da Hajara"

Ibram na

Wannan na ba da ƙarin haske ne game da shekarar Ibram sa'ad da waɗannan abubuwa sun faru. Mai yiwuwa harshenku na da yadda ake ba da irin wannan ƙarin hasken. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-background)

haifi Isma'ila wa Ibram

Ma'anar wannan shine "ta haifi wa Ibram ɗa, Isma'ila." An maida hankali a kan cewa Ibram na da ɗa.