Genesis 14

Genesis 14:1

Muhimmin Bayani:

Biranen da aka kira a Farawa 14:1 su na da 'yancin kansu. (Dubi: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Sai ya zamana

Ana amfani da wannan maganan wajen fara wani sabon sashi ne na labarin. Idan harshen ku na da yanda a ke faɗin wannan kuna iya amfani da shi nan.

a kwanakin

"a lokacin"

suka kai yaƙi

"suka tafi yaƙi" ko "suka fara yaƙi" ko "suka yi shirin yaƙi"

Genesis 14:3

Waɗannan sarakuna baya guda bayar suka taru

Bayanai cewa sojojinsu suna tare dasu ana iya bayyane. AT: "Waɗannan sarakuna biyar na ƙarshe da rundunarsu sun haɗu wuri ɗaya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Suka yi bauta shekaru sha biyu

Abubuwan da suka faru a ayoyi 4-7 sun faru ne kafin aya ta 3. Yarenku na iya samun hanyar nuna wannan.

Suka bautawa Kedorlawoma

Mai yiwu suna biyan haraji a warin shi, suna kuma bauta a matsayin sojojin shi. AT: "suna karkashin mulkin Kedorlawoma" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

suka yi tayawe

"sun ƙi bauta masa" ko "sun daina yi masa hidima"

Rafayim ... Zuzim ... Emim ... Horitiyawa

Waɗannan sunayen kungiyar mutanne ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Ashterot Karnayim ... Ham ... Shaveh Kiriatayim ... Se'ir ... El Faran

Waɗannan sunayen wurare ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Genesis 14:7

Muhimmin Bayani:

Ayoyi 8 da 9 sun maimaita abin da aka faɗa a cikin Farawa 14: 3 kuma ta ci gaba da ba da labarin abin da ya faru lokacin da sarakuna suka taru don yaƙi.

suka juyo suka zo

Kalmar "su" na nufin sarakuna hudun da suka zo domin su kai farmaki a yankin Kan'ana. Sunayen kuwa Amrafel, Ariok, Kedorlawomar, da Tidal. AT: "suka juyo su ka je" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-go)

Amoriyawa waɗanda ke zama a Hazazon Tamar

Wannan maganar na bayana wani mutane Amoriyawa ne aka ci da yaƙi. Akwai waɗansu mutanen Amoriyawa da suka kasance a wasu wurare.

da sarkin Bela (da ake kira Zowar)

Birnin Bela ana iya kira Zowar. Ana iya faɗin wannan maganar a karshen jimla. "da sarkin Bela suka fati da shirin yaƙi. Bela kuma ana iya ce ita Zowar."

Genesis 14:10

ya cika da ramukan yaƙi

"na da ramukan yaƙi dayawa." Waɗannan ramuka ne a ƙasa da akwai kwalta a ciki.

sarakunan Sodom da Gomora

Anan sarakuna suna wakiltar kansu da sojojinsu. AT: "sarakunan Sodom da Gomora da rundunarsu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

suka faɗa cikinsu

Ma'ana mai yiwuwa 1) wasu sojojinsu su ka faɗa cikin ramukan kwalta, ko 2) sarakuna da kansu su ka faɗa a cikin ramukan da ke da kwalta. Tunda yaki 14:17 ya bayana cewa sarkin Sodom a je ya sami Ibram, to mai yiwuwa ma'ana na farko ne ke dai-dai. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Waɗanda su ka rage

Waɗanda ba su mutu ba waje yaƙi kuma basu faɗa a cikin ramukan ba"

maƙiya

Wannan na nufin sarki Kedorlawomar da sauran sarakuna da suke tare da kuma sojojinsu wadda suke tare a kai wa Sodom da Gomora farmaki.

kayayyakin Sodom da Gomora

"Sodom" da "Gomora" na nufin mutanen da su ka zama a waɗannan biranen. AT: "dukiyar mutanen Sodom da Gomora" ko " mallakar mutanen Sodom da Gomora" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

suka kame Lot, ɗan ɗan'uwan Ibram, wanda ke zama a Sodom tare da dukkan malakarsa

Wannan maganar "ɗan ɗan'uwan Ibram" da kuma "wanda ke zama a Saduma" na tunar da masu karatu game da abubuwan da aka rubuta game da Lot a baya. AT: "suka kuma ɗauki Lot da dukka mallakarsa. Lot ɗan ɗan'uwan Ibram ne kuma ya na zama a Sodom a wacan lokacin" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-distinguish)

Genesis 14:13

Wani da ya tsira ya zo

"Wani mutum da gudo daga yaƙin ya zo"

Ya na zama

"Ibram yana zama." Wannan yana gabatar da bayanan baya. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-background)

dukkan su abokan yaƙi ne na Ibram

"wanda sun kulla yarjejeniya da Ibram" ko "suna kulla zama salama da Ibram"

dangin sa

Wannan na nufin da Lot, yaron ɗan'uwan Ibram.

horarrun mazaje

:mazajen da suka horu wajen yaƙi"

mazaje waɗanda aka haifa a gidansa

"mazajen da aka haifa a cikin gidan Ibram." 'Ya'yan bayin Ibram ne.

bi su

"bi su a guje"

Genesis 14:15

Ya rarrraba mazajensa găba da su a wannan daren ya kai masu hari

Mai yiwuwa wannan na nufin dabarar yaƙi ne. "Ibram ya rarraba mazajen kashi-kashi, suka kuma kai ma maƙiyansu hari ta hanyoyi dabam-dabam" (UDB)

dukka mallakar

Wannan na nufin abubuwan da maƙiyan suka sato daga birnin Sodom da Gomora.

da kayansa

"da mallakar Lot wadda maƙiyan suka sato daga wurin Lot"

da mataye da sauran mutane.

"tare da mataye da sauran mutanen da sarakuna hudu su ka kama"

Genesis 14:17

ya dawo

Bayanin da aka nuna game da inda yake dawowa zai iya zama bayyane. AT: "an koma inda yake zaune" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Melkizedek, sarkin Salem

Wannan ne farkon da ambaci wannan sarki.

gurasa da ruwan inabi

Mutane sun saba cin gurasa da ruwan inabi. Duba yadda aka fassara "gurasa" a Farawa 3:17 da kuma "ruwan inabi" a Farawa 9:20.

Genesis 14:19

Ya albarkace shi

Sarki Melkizedek ya albarkace Ibram

Mai albarka ne Ibram ta wurin Allah Mafi Ɗaukaka, Mahallicin sama da duniya

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "Bari Allah Mafi Ɗaukaka, Mahallicin sama da duniya ya albarkace Ibram" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

Allah Mafi Ɗaukaka, wanda ya ba da

"Allah Mafi Ɗaukaka domin ya ba da." Maganar ya fara da "wanda ya ba da" ya na faɗa mana wani abu ne gae da Allah Mafi Ɗaukaka.

Albarka ta tabbata ga Allah Mafi Ɗaukaka

Wannan hanyar yi wa Allah yabo ne. Duba yadda aka fassara "albarka ta tabbata" a Farawa 9:26.

a hannunka

"a mulkin ka" ko "cikin ikon ka"

Genesis 14:21

Ka bani mutane

"Mutanen" na iya nufin mutanen Sodom wanda maƙiya su ka kama. Ibram ya cece su a sa'ad da ya cece Lot.

Na ɗaga hannunna

Wannan na nufi "Na ɗauki ranstuwa" ko "Na yi alkawari."

Ba zan ɗauki komai ba sai abin da matasan samarai su ka ci

"Iyakar abin da matasana samarai suka ci shi ne a karba a gare ka." Ibram ya ki ya karba komai domin kansa, amma ya amince cewa sojojinsa sun riga sun ci daga abin da ke akwai a sa'ad da suna dawowa Sodom daga yaƙi.

rabon mazajen da ke tare da ni

Ana iya ba da ma'anar wannan maganar a gamsashen bayani. AT: "rabo daga mallakar da ke na mazajen da suka taimaka mini samun su" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Aner, Eshkol, da Mamre

Waɗannan abokan yaƙi ne na Ibram (Duba Farawa 14:13). Domin su abokan yaƙin Ibram ne, su na zuwa yaƙi tare da shi. Ana iya ba da cikakiyar ma'anar wannan maganar haka. AT: "Abokai na Aner, Eshkol, da Mamre" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)