Genesis 13

Genesis 13:1

ya bar

"hagu" ko "tashi daga"

ya tafi cikin Negeb

Negeb wani hamada ne kudu da Kan'ana, a yammacin Masar. Ana iya ba da gamsashen bayana wannan. AT: "komo zuwa hamadan Negeb" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Ibram ya wadata sosai ta fannin dabobi da zinariya da azurfa

"Ibram na da dobbobi masu yawa, zinariya da azurfa masu yawa ƙwarai"

dabbobi

"dabbobin gida" fo "shanu"

Genesis 13:3

Ya ci gaba da tafiyarsa

Ibram da iyalinsa suna bin tafiyar daga wani wuri zuwa wani wuri. Ana iya ba da gamsashen bayani. AT: "Suka ci gaba da tafiyarsu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

zuwa wurin da ya kafa rumfarsa ta can baya

Masu fassarawa na iya ƙara ƙarin bayani na ɗan ƙasan da ke cewa "Duba Farawa 12:8." Lokacin tafiyarsa zai iya zama bayyane. AT: "zuwa wurin da kafa rumfarsa kafin ya tafi zuwa Masar" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

kiran sunan Yahweh

"sum yi addu'a a cikin sunan Yahweh" ko "sujada ga Yahweh." Duba yadda aka juya wannan a Farawa 12:8.

Genesis 13:5

Yanzu

Ana amfani da wannan kalman wajen nuna cewa bayanin da ke zuwa na ba da ƙarin haske ne, domin ya taimake masu karatu wajen fahimtar aukuwar da ke zuwa. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-background)

ƙasar kuma ta kasa musu

Babu isashen wurin kiwo da ruwa domin dukka dabbobin su.

mallakarsu

Wannan ya ƙunshi dabbobi ma, da suke bukatar wurin kiwo da kuma ruwa.

ba su iya tsayawa

"basu iya zama tare ba"

Kan'aniyawa da Feriziyawa na zama a wannan ƙasar a wancan lokacin

Wannan ma wani dalili ne da ya sa ƙasar ta kasa musu dukka.

Genesis 13:8

bai kamata a sami rashin jituwa tsakanina da kai ba

"kar muyi jayayya"

rashin jituwa

"takun saƙa" ko "hargitsi" ko "husuma"

ko kuma tsakanin makiyayan dabbobina da makiyayan dabbobinka

"mu kuma hana makiyayan dabbobin mu jayayya"

Fiye ma da haka mu dangi ne

"domin mu dangi ne"

ba fili ne nan gabanka ba?

Ana iya juya wannan tambayan a wata hanya mai kyau. AT: "dukka filin na nan domin ka." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

ka zaɓi duk inda ka ke so

Ibrahim na magana da Lot, yana kuma karfafa shi ya yi abin da zai taimake su tare. "Mu rabu."

in ka zaɓi dama ni sai in zaɓi hagu

Ma'ana mai yiwu 1) "In ka bi wani hanya, ni sai in bi ɗayan" 2) "In ka yi arewa, ni sai in yi kudu." Ibram ya bar Lot ya zaɓi iyakar fili da yake so, sai shi Ibram kuma ya ɗauki abin da ya rage.

Genesis 13:10

dukka yankin Urdun

Wannan na nufin iyakar yankin Kogin Urdun.

gan shi kore shar

"akwai ruwa sosai"

kamar lambun Yahweh kamar kuma ƙasar Masar

"kamar gonar Yahweh ko kamar ƙasar Masar." Waɗannan wurare dabam ne guda biyu.

kamar lambun Yahweh

Wannan wani suna na gonar Aidan.

Haka yake kafin a hallaka Sodom da Gomora

Wannan yana tsammanin wani abu da zai faru daga baya. Yana da mahimmanci a nan saboda ya bayyana dalilin da ya sa Lot ya zauna a yankin da daga baya ba ta da amfani.

dangin

"yan'uwa" ko "iyalan." Wannan na nufin Lot da Ibram da kuma gidajensu.

Genesis 13:12

zauna

"kasance" ko "tsaya"

ƙasar Kan'ana

"ƙasar Kan'anawa"

Ya kakkafa rumfunansa har zuwa Sodom

Ma'ana mai yuwa 1) "Ya kakkafa rumfunansa kusa da Sodom" (UDB) ko 2) "Ya matsar da rumfanansa zuwa wani wuri da ya kai har zuwa Sodom."

Genesis 13:14

bayan Lot ya rabu da shi

"bayan Lot ya bar Ibrahim"

Genesis 13:16

ka kewaya faɗin ƙasar da tsawonta

"ka kewaya dukka ƙasar"

Mamre

Wannan sunan mutumin da yake da itacen rimin. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Hebiron

Wannan sunan wuri ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

bagadi domin Yahweh

"badadin yi wa Yahweh sujada"