Genesis 12

Genesis 12:1

To yanzu

Ana amfani da wannan kalmar domin nuna alamar sabon sashin labari.

Ka tashi ka bar ƙasarka da danginka

"Ka tafi daga ƙasarka, daga iyalika"

zan maishe ka babbar al'umma

"ka" a nan na nufin Ibram ne, amma Ibram na wakiltar zuriyar sa. AT: "Zan fara babbar al'umma ta wurin ka" ko "Zan mai da zuriyarka babbar al'umma" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-synecdoche)

kuma sa sunanka ya yi girma

Kalmar "suna" tana wakiltar mutuncin mutum. AT: "kuma maishe ka shaharare" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

za ka zama albarka

An fahimci waɗannan kalmomin "zuwa wasu mutane." AT: "za ka zama albarka ga wasu mutane" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-ellipsis)

duk wanda ya rena ka, zan la'anta shi

"zan la'anta duk wanda ya rena ka" ko "idan wani ya mayar da kai abin banza, zan la'ance shi"

Ta wurin ka dukkan al'ummar duniya za ta sami albarka

Ana iya sanya wannan aiki. AT: "Zan albarkace al'umman duniya dukka ta wurin ka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

Ta wurin ka

""Saboda ka" ko "Domin na albarkace ka"

Genesis 12:4

mallaka

Wannan ya kunshi dabbobi da dukiya mara rai.

dukkan mutanen da su ka samu

Mai yiwuwa ana nufi 1) "bayin da suka tara" (UDB) ko 2) "mutanen da suka tara su kasance tare da su."

Genesis 12:6

Ibram ya wuce ƙasar

An kira Ibram ne kadai domin shine kan gidan. Allah ne ya bashi umurni ya tashi da iyalinsa su kuma tafi wurin. AT: "Sai Ibram da iyalinsa suka wuce cikin ƙasar" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

ƙasar

"ƙasar Kan'ana"

al'ul na Moreh

Mai yiwuwa "Moreh" sunan wani wuri. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Yahweh, wanda ya bayyana a gare shi

"Yahweh, domin ya bayyana a gare shi"

Genesis 12:8

ya kafa rumfarsa

Ibram na da mutane dayawa tare da shi sa'ad da yana tafiya. Mutanen da suke tafiya wurare dabam dabam na zama a rumfar ne. AT: "suka kafa rumfarsu"

kira bisa sunan Yahweh

"sun yi addu'a cikin sunan Yahweh" ko "yi wa Yahweh sujada"

Daga nan Abram ya ci gaba da tafiya

"Sai Ibram ya ɗauki rumfarsa ya kuma ci gaba da tafiya." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

zuwa wajen Negeb

"ta yankin Negeb" ko "ta wajen kudu" ko "kudu zuwa hamadan Negeb" (UDB)

Genesis 12:10

A kwai yunwa

Amfanin gona bai girma da kyau ba a wancan kakar. Ana iya ba wannan gamsashen bayani cewa. AT: "Ana ƙarancin abinci" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

cikin ƙasar

"cikin yankin" ko "a ƙasar da Ibram ke zama"

gangara zuwa

Mai yiwuwa ana nufin 1) "kara gaba zuwa kudu" (UDB) ko 2) "ya tafi daga Kan'anan zuwa." Zai fi kyau a juya wannan da kalmar da aka saba amfani da shi waje tafiya daga wuri mai tudu zuwa ƙasa.

za su kashe ni ... ki da rai

Ana iya ba gamsashen bayana game da dalilin da zai sa a kashi Ibram: "za su kashe ni domin su aure ki" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

don a bar ni in rayu sabo da ke

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: domin saboda ke, ba za su kashe ni ba" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

Genesis 12:14

Sai ya zamana cewa

Mai yiwuwa ana nufin 1) An yi amfani da wannan kalmomin a nan domin sa alamar inda aka fara abu, kuma idan harshenku na da hanyar yin wannan, ana iya yin yan ke shawarar amfani da shi a nan, ko 2) "haka kuma ya faru" (UDB).

'Ya'yan sarki suka gan ta

"Jami'an Fir'auna su ka ga Sarai" ko "ma'aikacin Fir'auna suka gan shi" (UDB)

yaba mata a gaban Fir'auna

AT: "Fir'auna ya ɗauke ta zuwa cikin gidansa" ko "Fir'auna da sojojinsa sun ɗauke ta zuwa cikin gidansa" (Dubi: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

Matar

Sarai

gidan Fir'auna

Mai yiwuwa ana nufin 1) "iyalin Fir'uan", wato a matsayin mata, ko 2) "gidan Fir'auna" ko "fadar Fir'auna," ana nufin Fir'auna ya maishe ta ɗaya a cikin matan shi. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-euphemism)

sabo da ita

"saboda Sarai" ko "saboda ita"

Genesis 12:17

saboda Sarai matar Ibram

Ana iya bayyana wannan a bayyane. AT: "domin Fir'auna na da nufin ɗaukan Sarai, matar Ibram, ta zama matar sa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Fir'auna ya kira Ibram

"Fir'auna ya kira Ibram" ko "Fir'auna ya umarci Ibram ya zo wurinsa"

me kenan ka yi mini?

Fir'auna yayi amfani da wannan tambaya ta zance don ya nuna fushin sa game da abin da Ibram ya yi masa. Hakanan za'a iya bayyana azaman tsawa. AT: "Kun yi min mummunan abu!" (Duba:: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

Sai Fir'auna ya ba da umarni game da shi

"Sai Fir'auna ya umarci ma'aikatan sa game da Ibram"

su ka sallame shi ya tafi, tare da matarsa da duk abin da ya ke da shi

"sai ma'aikatan suka sallame Ibram daga wurin Fir'auna, da matar sa da kuma dukka mallakarsa"