Genesis 11

Genesis 11:1

To Yanzu

Wannan kalmar na nuna cewa marubucin na shirin fara wani sabon sashi ne na labarin.

dukkan duniya

dukka mutanen duniya (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

sun yi magana da harshe ɗaya, kalmominsu kuma ɗaya ne

Waɗannan magana na nufin abu ɗaya ne, kuma na jadada cewa dukkan mutane sun yi magana da harshe ɗaya ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-parallelism)

tafiya

"ƙaura" ko "tafiya wurare"

a gabas

Mai yiwuwa ana nufi 1) "cikin gabas" ko 2) daga gabas" ko 3) "zuwa gabas". Zaɓin da aka fi so shi ne "a gabas" saboda Shinar yana gabas inda malamai ke gaskata jirgin ya tsaya.

zauna

daina tafiya daga wuri zuwa wuri aka kuma kasance a wuri ɗaya ana rayuwa

Genesis 11:3

Zo

Idan harshen ku na da yadda ake iza, ko umurtar mutane ga yin aiki kamar yadda Turanci ke amfani da "ku zo!", kuna iya amfani da shi a nan.

gasa su sosai

Mutane na yin tubali daga yinɓu sai a gasa su sosai domin su kasance da karfin gaske.

katsi ko kwalta

wani abu ne mai kauri, da ke mannewa, baƙi mai ruwa-ruwa da ke fitowa daga ƙasa

yinɓu

Wannan wani abu ne mai kauri da ake yin ta daga garin siminti, lãka, garin kasa da ruwa wanda ake amfani wajen hada tubali ko duwatsu waje gini.

mu yi wa kanmu suna

"mu yi wa kanmu martaba mai girma"

suna

"martaba"

zamu warwatsu

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "za mu rarrabu daga tsakanin mu kuma kasance a wurare dabam dabam" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

Genesis 11:5

zuriyar Adamu

"mutanen"

sauko ƙasa

Ana iya ba da gamsashen bayani game da inda ya sauko: "sauko daga sama." Wannan baya bayana yadda ya sauko ba. Yi amfani da kalmar gama gari ma'ana "ta sauko." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

suka gina

"a kiyaye" ko "a duba sosai"

sun fara yin wannan

Mai yiwuwa ana nufi 1) sun riga sun fara aikata wannan," manufar cewa sun fara gina hasumiya amma basu karasa ba, ko 2) "Wannan abu ne farko da suka yi," ko ma'anar shi ne nan gaba za su yi manyan abubuwa.

za su iya yin duk wani abin da su ka yi niyya

Ana iya bayyana wannan a cikin tsari mai kyau. AT: "kowani abin da suka yi niyyar aikatawa mai yiwuwa ne a gare su" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-doublenegatives)

mu sauka

Kalmar "mu" jam'i ne ko da yake yana nufin Allah ne. Wasu sun juya shi cewa "bari in sauka" ko "zan sauka." Idan an yi haka, ana iya tunanin sharihinta cewa wakilin sunan jam'i ce. Duba bayanin "Bari mu yi" a Farawa 1:26. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-pronouns)

rikirkitar da harshensu

Ma'anar wannan shi ne Yahweh zai sa mutanen dukka duniya su daina amfani da harshe ɗaya. AT: "jujjuya harshensu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

domin kada su fahimci juna

Wannan ne dalilin rikirkitar da harshensu. AT: "ta yadda ba za su iya fahimtar abin da juna ke faɗi ba" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Genesis 11:8

daga can

"daga birnin"

sunansa ya zama Babel, domin a can ne Yahweh ya rikirkitar

sunan Babel na kamar kalmar da ke nufin "rikirkita." Masu juya na iya sharihinta game da wannan.

rikirkitar da harshen dukka duniya

Ma'anar wannan shi ne Yahweh zai sa mutanen dukka duniya su daina amfani da harshe ɗaya. AT: "jujjuya harshen duniya gaba ɗaya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Genesis 11:10

Muhimmin Bayani:

Sauran suran nan na ba da jerin zuriyar Shem zuwa Ibram.

Waɗannan su ne zuriyar Shem

Wannan jimlar ya fara jerin zuriyar Shem.

ambaliya

Wannan ita ce rigyawa daga zamanin Nuhu lokacin da mutane suka zama mugaye har Allah ya aiko da ambaliyar duniya ta rufe duniya.

zama mahaifin Arfakshad

"samu ɗan sa Arfakshad " ko "aka haifi ɗansa Arfakshad"

Arfakshad

Wannan sunan namiji ne (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

ɗari ... biyu ... ɗari biyar

Masu juya na iya rubuta wannan cikin kalmomi ko adadi "100," "2," da "500." (ULB da UDB na amfani da kalmomi idan lamba na da kalma ɗaya ko biyu; sun amfani da adadi kuma idan lamba na kalmomi uku ko fiye. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers))

Genesis 11:12

ya zama mahaifin Shelah

"an haifi ɗan sa Shela"

Shela

Wannan sunan namiji ne (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Genesis 11:14

Muhimmin Bayani:

Abubuwan da aka rubuta a cikin Farawa 11:12-25 suna da tsari iri ɗaya. Duba yadda ka fassara su a cikin Farawa 11:12-13. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)

Genesis 11:16

Genesis 11:18

Genesis 11:20

Genesis 11:22

Genesis 11:24

Ibram, Nahor, da Haran

Ba mu san jerin haifuwar 'ya'yan sa ba.

Genesis 11:27

To waɗannan su ne zuriyar Tera

Wannan jimlar na gabatar da labarin zuriyar Tera. Farawa 11:27-25:11 na managa game da zuriyar Tera musamman ɗan sa Ibrahim. AT: "Wannan ne jerin asalin zuriyar Tera" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Haran ya mutu a fuskar mahaifinsa Tera

Wannan na nufin cewa Haran ya mutu yayin da mahaifinsa na nan da rai. AT: "Haran ya mutu yayin da mahaifinsa Tera, na tare da shi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Genesis 11:29

ɗauka mata

"aure mata"

Iskah

Wannan sunan mace ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

To yanzu

Ana amfani da wannan kalmar wajen gabatar da sabon bayani game da Sarai da zai zama da muhimminci a surori na gaba.

bakarariya

Wannan kalmar na bayana macen da ba ta iya haifuwa ba ko yin ciki ba. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-euphemism)

Genesis 11:31

ya

A nan kalmar "ya" na nufin Tera.

surukarsa Sarai matar ɗansa Ibram

"surukarsa Sarai, wanda itace matan ɗansa Ibram"

Haran ... Haran

Waɗannan sunaye biyu ne dabam dabam kuma ana rubuta su dabam dabam a Ibraniyanci. Ɗayan sunan mutum ne, ɗayan kuma sunan birni ne. Kuna iya rubuta su dabam dabam a harshen ku domin nuna wannan bambanci.