"Wannan shine asalin 'ya'yan Nuhu." Wannan jimlar na gabatar da asalin zuriyar Nuhu a Fara 10:1-11 :9.
"Ya'yan Yaban maza da zuriyar suka rabu, su ka je ƙasashe"
Wannan na nufin mutanen da suke zama a tsibiri.
"ƙasashensu na asali." Waɗannan wurare ne da mutane suka koma zama.
"Kowanne mutane suna furta harshensu" ko "Mutanen suka raba kansu zuwa harshensu"
Mizrayim ƙasar "Masar" ne a harshen Ibraniyanci.
Mai yiwuwa ana nufin 1) "babban mayaƙi" ko 2) "babban jarumi" ko 3) "ikon mulki."
Mai yiwuwa ana nufin 1) "a gaban Yahweh" ko 2) "da taimakon Yahweh"
Wannan na gabatar da karin magana. Mai yiwuwa harshenku na da yadda ku ke gabatar da karin magana ta wani hanya. AT: "Wannan shine dalilin da ya sa mutane su ke cewa (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-proverbs)
Mai yiwuwa ana nufin 1) wurin da fara mulkinsa, ko 2) muhimmin birane
"Nimron ya tafi zuwa Asiriya"
Jerin sunayen zuriyar Nuhu ya ci gaba.
Mizrayim ɗaya ne daga cikin 'ya'yan maza na Ham. Zuriyarsa ne suka zama mutanen Masar. Mizrayim kalmar Ibraniyanci ne na Masar.
Wannan sunayen na nufin babban taron mutanen zuriyar Kan'ana
"yankin ƙasa" ko "iyakar ƙasar su"
Idan ya kasance ana bukatar gamsashen bayani game da yankin kudu. AT: "daga arewacin birnin Sidon har zuwa kudunci garin Gaza, wanda ke kusa da Gerar" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)
Idan ya kasance ana bukatar gamsashen bayani game da yankin da ke fuskantar "gabas" ko "nesa daga teku." AT: "sai gabas wajejen garuruwan Sodom, Gomara, Adma, da Zeboyim har zuwa Lasha" (Duba: Assumed Knowledge da Implicit Information)
Kalmar "waɗannan" na nufin mutanen da jera sunayensu a Farawa 10:6.
"suka rabu bisa ga harsunansu dabam dabam"
"cikin ƙasashensu na asali"
Arfakshad ɗaya ne daga 'ya'yan Shem.
Masu fassara na iya ƙara bayanin takaice na rubutu da ke cewa: "ma'anar sunan Feleg kuwa shine 'rabuwa.'"
Ana iya sanya wannan aiki. AT: "mutanen duniya suka raba kansu" ko "mutanen duniya suka rabu daga tsakanin su" ko "Allah ya raba mutanen duniya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)
Yoktan ɗaya ne daga 'ya'yan Eber. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)
Anan "waɗannan" na nufin 'ya'ya maza na Yoktan.
"ƙasar da suke da iko akai" ko "ƙasar da suke zama"
Kalmar "waɗannan" na nufin zuriyar Shem (Farawa 10:21).
Wannan na nufin dukka jerin mutane da aka kira daga Farawa 10:1.
"jeri bisa"
"Daga waɗannan kabilun ne janhuroriyoyi suka rarrabu a ko'ina a duniya" ko "Waɗannan kabilun suka rarrabu a tsakaninsu suka zama janhuroriyoyi na duniya"
Ana iya bayana wannan a fili da gamsashen bayani. AT: "bayan ambaliyan ruwan ya hallakar da duniya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)