Genesis 9

Genesis 9:1

ku ruɓanɓanya, hayayyafa, ku wanzu a duniya

Wannan albarkan Allah ne. Ya ce wa Nuhu da 'ya'yan sa su haifar da wasu mutane kamar kansu, domin a su zama da yawa. Kalmar "ruɓanɓanya" na bayana yadda za su "hayayyafa." Dubi yadda aka fassarar wannan umarnin a Farawa 1:28. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-doublet da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

Tsoronku da tsoratawarku za ta zama a kan kowani dabba mai rai ... da kuma dukkan kifayen teku

Marubucin na maganar tsoro da tsoratarwa kamar wani abu ne da ke iya kasance a kan dabbobin. AT: "Kowani dabba mai rai ... da dukkan kifayen teku za su ji tsoron ka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

kowani dabba da ke duniya

Wannan ne farko jeri guda na dabbobi da marubucin ya rubuta, ba wai an takaita ambacin sauran dabbobin da aka ambaci su a nan gaba ba.

tsuntsu

Wannan suna ne na dukka abubuwa da suke tashi sama. Dubi yadda aka fassara wannan a Farawa 1:20.

a kan duk wani abu da ke motsi bisa ƙasa

Wannan ya haɗa kowani irin kananan dabbobi. Dubi yadda aka fassara wannan a Farawa 1:24.

An ba da su a hannunka

Hannun yana wakiltar sarrafawa. Ana iya sanya wannan aiki. AT: "An ba su su cikin ikonku" ko "Na sanya su ƙarƙashin ikonku" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

Genesis 9:3

Muhimmin Bayani:

Allah ya ci gaba da magana da Nuhu da 'ya'yansa.

rai ... jini

Masu fassara na iya ƙara alamun rubutu kamar haka: "Jini alama ce ta rayuwa." Wataƙila za su iya ƙara alamar ƙwallon ƙafa da ke faɗi abu kamar haka: "Allah yana umartar mutane kada su ci nama yayin da jini ke cikinsa. Dole ne su fara fitar da jinin da farko."

Genesis 9:5

Muhimmin Bayani:

Allah ya ci gaba da magana da Nuhu da 'ya'yansa.

Amma bisa jininka

Wannan na banbanta jinin mutum da jini dabbobi (Farawa 9:1).

bisa jininka, da ran da ke cikin jinin ka

Wannan na nuna cewa a zubar da jini. AT: "Idan wani ya sa jinika ya zuba" ko "Idan wani ya zubar da jinika" ko " Idan wani ya kashe ka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

rayuwa

Wannan na nufin rayuwa a zahiri

zan buƙata

Wannan biyan na nufin mutuwar mai kisa, ba kuɗi ba. AT:"zan buƙaci duk wanda ya kashe ka ya biya"

Daga hannun

A nan kalmar "hannun" na nufin wanda ya zama sanaɗin faruwar abin. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-synecdoche)

Daga dukkan dabbobi zan bukace ta

"zan buƙaci kowacce dabba da ta dauki ranka ta biya"

Daga hannun kowanne mutum, wato mutumin da ya yi kisan kai ga ɗan'uwansa, zan bukaci bada lissafi na wannan mutum

"Zan bukaci duk wanda ya ɗauki ran wani mutum ya biya"

daga hannun

Wannan na nufin mutum. AT:"daga wannan mutumin" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-synecdoche)

ɗan'uwansa

A nan an yi amfani da "dan uwa" a matsayin dangi, kamar yan ƙabila daya, dangi, or ƙungiya.

Duk wanda ya zubar da jinin mutum ta wurin mutum za a zubar da jininsa

Zubar da jini na nufin kisan wani. Wannan na nufi idan wani mutum ya kashe wani, to tilas ne wani mutum ya yi kisan sa. Duk da haka "jini" na da muhimminci a wannan yankin rubutun, in ya yiwu a yi amfani da kalmar a juyi. Fassarar "zubar da jini" da kalmar da zai nuna yawan jini da a ka rasa na sa mutuwa. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

domin cikin kammanin Allah aka hallici mutum

"domin Allah ya yi mutum ya zama kaman shi" ko "domin na yi mutum a cikin kamani na"

ku warwatsu a ko'ina a duniya, ku ruɓanɓanya

Wannan albarkar Allah ce. Ya ce wa Nuhu da iyalin sa su hayayyafa, don suyi yawa. Kalmar "ku ruɓanɓanya" ta bayyana yadda zasu zama da "albarka". Duba yadda aka fasara a Farawa 1:28. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-doublet da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

Genesis 9:8

Sai Allah ya yi magana da Nuhu da 'ya'yansa da ke tare da shi

Da ma tun can Allah na magana da su. Wannan maganar na ba da alamar cewa Allah zai canja abin da yake magana a kai. AT: Allah ya ci gaba da magana wa Nuhu da 'ya'yansa" ko "Sai Allah ya ci gaba da cewa"

Amma

An yi amfani da wannan jimlar da Turanci domin a nuna canzawa daga lokacin da Allah ke magana da Nuhu da 'ya'yan sa zasu yi zuwa abin da Allah zai yi

tabbatar da alkawarina da ku

"sa alkawari tsakanin na da kai." Fassarar wannan kamar Farawa 6:18.

Genesis 9:11

Muhimmin Bayani:

Allah ya ci gaba da magana da Nuhu da 'ya'yansa.

Na tabbatar da alƙawarina da ku

"Ta wurin faɗin wannan, Ina sa alƙawari tare da kai." Dubi yadda a juya kalmomi mai kamar wannan a cikin Farawa 6:18.

duk halittu

Mai yiwuwa ana nufin 1) dukka mutane ko 2) dukka rayayu da ake gani, da mutane da dabbobi. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

ba za a saken yin ruwan da zai hallaka duniya ba

"Ba za a ƙara hallakar da duniya da ambaliya ba." Za a yi ambaliya, amma ba zai hallakar da dukkan duniya.

alama

Wannan na tunashewa da abin da aka alkawatar.

alƙawari ... zamanin da ke zuwa

Alkawarin ya shafi Nuhu da iyalinsa har ma da dukkan tsararraki masu zuwa.

Genesis 9:14

Muhimmin Bayani:

Allah ya ci gaba da magana da Nuhu da 'ya'yansa.

Zai kuma zamana a lokacin

"kowani lokaci." Abu ne wanda zai ci gaba da faruwa loto loto.

aka ga bakangizo

Ba a bayana ko wanene zai ga bakangizo, amma tun da shike alƙawari na sakanin Yahweh ne da mutane, kuma in ya zama lalle a faɗa ko wanene da wanene za za su ga bakangizon, zai fi kyau a cewa Yahweh ne da mutane. Ana iya fassara wannan ta hanyar aiki. AT: "Ni da mutane za mu ga bakangizo" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

Zan tuna da alkawarina

Wannan bai nuna cewa Allah zai manta ba ne. AT: "Zan yi tunani game da alƙawarina"

ni da kai

Kalmar "kai" biyu ne. Allah na maganar Nuhu da 'ya'yansa.

kowani halitta

"kowani irin abu mai rai"

Genesis 9:16

Muhimmin Bayani:

Allah ya ci gaba da magana da Nuhu da 'ya'yansa.

domin in tuna

"saboda in tuna" ko "domin in yi tunani game"

tsakanin Allah da kowani halitta mai rai

Allah ke magana anan. AT: "tsakanin na da kowani halitta mai rai"

Sai Allah ya cewa Nuhu

Allah ya riga yana magana da Nuhu. Wannan magana na ba da alama ce na karshen sashin abin da Allah yake cewa. AT: "Allah ya gama magana da Nuhu" ko "Sai Allah ya ce wa Nuhu"

Genesis 9:18

Muhimmin Bayani:

Ayoyi 18-19 na gabatar da 'ya'yan Nuhu su uku, wanda suke da muhimminci a sashin labari da ke gaba.

mahaifi

Ham shi ne asalin mahaifin Kan'ana.

Genesis 9:20

manomi

"mai noma ƙasa"

ya bugu

"ya sha 'ya'yan inabin da yawa"

tsurara

Nassin bai fayyace nawa jikin Nuhu ya buya yayin da yake cikin maye ba. 'Ya'yansa maza halayen sun nuna mana cewa abin kunya ne.

Genesis 9:22

mahaifin sa

Wannan na nufin Nuhu ne.

Genesis 9:24

Muhimmin Bayani:

A cikin ayoyi 25-27 Nuhu ya la'anci ɗan Ham kuma ya albarkaci 'yan'uwan Ham. Abin da Nuhu ya faɗa game da su kuma ya shafi zuriyarsu, kamar yadda aka nuna a cikin UDB.

Muhimmin Bayani:

ULB yayi wannan tare da waƙoƙi a cikin la'anar Nuhu da albarka a cikin ayoyi 25-27. Wasu fassarar suna saita kowane layi na waƙa nesa da dama fiye da sauran rubutun don sauƙaƙe karatu.

ya tashi daga mayensa

"ya warware"

ɗansa ƙaramin

Wannan na nufin Ham ne. AT: "ƙaramin ɗansa, Ham"

Kan'ana zai zama la'annanne

"Na la'anci Kan'ana" ko "Bari mugayen abubuwa su faru ga Kan'ana"

Kan'ana

Wannan ɗaya ne daga 'ya'yan Ham. AT: "ɗan Ham, Kan'ana"

ya zama baran barorin 'yan'uwansa

"mafi ƙarancin bawan 'yan'uwansa" ko "mafi ƙanƙantar bawan' yan'uwansa"

'yan'uwansa

Wannan na iya nufin 'yan'uwan Kan'ana ko kuma danginsa gaba ɗaya.

Genesis 9:26

Muhimmin Bayani:

Idan za a iya sa waɗanan ayoyin kamar waka domin masu karatu su gane cewa waka ne.

Yahweh, Allah na Shem, ya zama da albarka

"Yabo ya tabbata ga Yahweh, Allahn Shem," ko "Yahweh, Allahn Shem, ya isa yabo" ko "Na yabe Yahweh, Allahn Shem" (UDB)

Kan'ana ya zama baransa

"Kan'ana kuma ya zama baran Shem." Wannan ya shafi zuriyar Kan'ana da zuriyar Shem.

Allah ya faɗaɗa abin mulkin Yafet

Mai yiwuwa ana nufin 1) "Allah ya sa ƙasar Yafet ya yi girma" (UDB) ko 2) "Allah ya sa Yafet ya sami zuriya mai yawa."

ya kuma sa gidansa a cikin rumfunan Shem

"ya kuma yi zaman salama da Shem." Wannan ya shafi zuriyar Yafet da zuriyar Shem.

Kan'ana kuma ya zama baransa

"bari Kan'ana kuma ya zama baransa." Wannan na nufin zuriyar Kan'ana da Yafet