Genesis 8

Genesis 8:1

la'akari

"tuna" ko "tunani game da"

jirgin

Wannan na nufin babban akwati da zai iya tafiya akan ruwa ko da bakin ƙwarya. "babban kwalekwale" ko " Babban Jirgin ruwa." juya wannan kamar a cikin Farawa 6:13.

Maɓuɓɓugai na ƙarƙas da tagogin sama aka rufe su

"Ruwan ya daina fitowa daga ƙasa, ruwan sama kuma ya daina faɗowa." Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "Allah ya rufe maɓuɓɓugai zurfafa da tagogin sama" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

maɓuɓɓugai zurfafa

"ruwa daga ƙarƙashin duniya." Dubi yadda aka fassarar wannan a cikin Farawa 7:11.

aka rufe tagogin sama

Wannan na nufin ruwan ya daina. Wannan na bayana sararin sama kamar rufi ne da ke hana ruwan da ke sama daga saukowa a duniya. A sa'ad da tagogi ko kofofin da sararin sama suka buɗe, sai ruwa ta sauko ta cikin su. AT: "sararin sama ta buɗe" ko "kofofin sama suka buɗe." Dubi yadda aka juya "tagogin sama" a cikin Farawa 7:11.

Genesis 8:4

ya sami sauka

"sauka akan doran ƙasa" ko "tsaya a doron ƙasa"

a ranar sha bakwai ga watan bakwai ... watan goma

Domin Musa ne ya rubuta wannan littafi, mai yiwuwa ana nufin watan bakwai da na goma na kalandar Ibraniyawa, amma ba tabbacin wannan. (Duba /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-hebrewmonths da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-ordinal)

A rana ta farko ga watan

"A rana ta farko ga watan goma"

bayyana

Ana iya bayana wannan a fili: "bayyana a bisa fuskar ruwan." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Genesis 8:6

Sai ya zamana

Ana amfani da wannan maganar domin sa alama a farkon wani sabon sashi labari. Idan harshenku na da wani hanya faɗin haka, ana iya yanke shawarar amfani da shi a nan. AT: "Ya kasance cewa"

Sai ya zama ... tagar jirgin ruwa da ya yi.

Maganar "da ya yi" na magana game da tagar. Wasu harsuna na iya bukaci a raba wannan maganar zuwa wani jimla: "Nuhu ya yi taga a jirgin ruwan. "sai ya zama bayan kwanaki arba'in sai ya buɗe tagar" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-distinguish)

hankaka

wani bakin tsuntsu ne da ya ke cin zanlar nama da dabbobin da sun mutu

ya yi ta kai da komowa

Wannan na nufin hankaka ya yi ta barin cikin jirgin ya je ya dawo.

har sai da ruwa ya tsanye daga duniya

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "sai da iska ya busher da ruwan" ko "har sai ruwan ya bushe" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

Genesis 8:8

ba ta sami wurin hutawa ba

"saukowa" ko " sauka." Ya na nufin sauka aka wani abu domin a huta daga shawagi a sama.

ƙafan ta ... ta dawo ... ta kawo

Marubucin na amfani da kalmar "kurciya" a matsayin mace. Ana iya juya waɗannan maganganu ta wannin wakilin sunan " ta ...ita ..." ko "shi ...ka ..." bisa ga yadda harshenku ke kiran kurciya.

shi

Idan ana amfani wakilin suna na maza wa "kurciya", za a bukaci a sa sunar Nuhu a nan domin a kauce wa rikicewa: "Nuhu ya aike kurciyar," Nuhu ya miƙar da hannunsa," etc.

Genesis 8:10

Duba

"Jawo hankalin" ko "Wannan na da muhimminci"

sabon ganye zaitun

"ganyen da ta tsinko daga itacen zaitun"

tsinko

"yanke daga abu"

Ya ƙara jira na waɗansu kwanaki bakwai

"Ya kuma jira na kwanaki bakwai"

ba ta sake komawa wurinsa ba

Ana iya bayana dalilin a fili idan mutane ba za su fahimta ba: "Ba ta sake komawa wurinsa ba domin ta sami wurin hutawa." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Genesis 8:13

Sai ya zamana

Ana amfani da wannan maganar domin ba da alama na farkon wani sabon sashin labarin. Idan harshenku na da wani hanya faɗin haka, ana iya yanke shawarar amfani da shi a nan.

a shekaru na ɗari shida da ɗaya

"sa'ad da Nuhu na shekara 601" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-ordinal)

a wata na farko, a ranar farko

Domin Musa ne ya rubuta wannan littafi, mai yiwuwa ana nufin watan farko na kalandar Ibraniyawa ne, amma ba tabbacin wannan. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-hebrewmonths da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-ordinal)

ruwa ta bushe daga ƙasa

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki AT: "ruwan da ya rufe ƙasa ya bushe" ko "iska ta busher da ruwan da ya rufe ƙasa" (Dubi: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive).

rufin jirgin ruwan

Wannan na nufin abin da aka sa domin hana ruwan sama shiga cikin jirgin.

ga shi

Kalmar "ga shi" na jawon hankalin mu ne ga muhimmin sakon da ke zuwa nan gaba.

A cikin wata na biyu, a ranar ashirin da bakwai

"rana ta ashirin da bakwai ga watan biyu." Wannan mai yiwuwa ana nufin wata na biyu na kalandar Ibraniyawa ne, amma ba tabbacin wannan. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-hebrewmonths da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-ordinal)

ƙasa ta bushe

"ƙasar ta bushe gaba ɗaya" (UDB)

Genesis 8:15

Fito ... kwaso waje

"bar ... ɗauki." Wasu fassarar an karanta "zo waje ... kawo" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-go)

kowancce halitta mai rai

"kowacce irin halitta mai rai." Duba yadda aka juya "kowacce halitta" a Farawa 6:11.

ku hayayyafa, ku kuwa ruɓaɓɓanya

Wannan karin magana ne. Duba yadda aka juya wannan a Farawa 1:28. Allah na so mutane da dabbobi su sake haifuwa, domin so kasance dayawa. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-doublet da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

Genesis 8:18

Nuhu ya fita

Wasu fassarar sun karanta "Nuhu ya fito." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-go)

bisa ga iyalinsu

"tare da irin su"

Genesis 8:20

gina bagadi ga Yahweh

"gina bagadi, ya keɓe wa Yahweh" ko "gina bagadin sujada ga Yahweh." Mai yiwuwa ya gina shi da duwatsu ne.

dabbobi ma su tsarki ... tsuntsaye ma su tsarki

"tsarki" a nan na nufin cewa Allah ya yarda a yi amfani da waɗannan dabbobin domin hadaya. Ba a amfani da wasu dabbbobi wajen miƙa hadaya, ana kiran su "mara tsarki."

miƙa hadaya ta ƙonawa

Nuhu ya kashe dabbobin, sai ya ƙona su kurmus a matsayin baiko ga Allah. AT: "ƙona dabbobin a matsayin baiko ga Yahweh"

ƙanshi mai gamsuwa

Wannan na nufin ƙanshi mai kyau daga gasashen nama.

nufe nufen mutum a zukatansu mugunta ne tun daga yarintakarsu

"tun daga farkon shekarunsu, sun kasnace da nufin aikata mugunta" ko "tun suna ƙuruciya, suna son aikata mugayen abubuwa"

Muddin duniya tana nan

"muddin jurewa duniya" ko "muddin kasancewa duniya"

lokacin shuka

"lokacin da ake yin shuki"

sanyi da zafi, damina da rani

Wannan maganar na nufin yanayi lokaci biyu da suke a shekara. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-merism)