Genesis 7

Genesis 7:1

Muhimmin Bayani:

Abubuwan da suka faru a wannan surar na bayan da Nuhu ya gina jirgin ruwan, ya tara abinci, ya kuma sa a cikin jirgin.

"Zo ...cikin jirgin ... kawo

"shiga ... cikin jirgin ... ɗauki." Yawancin fassara sun karanta "Ku tafi ... cikin jirgin ... ɗauki." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-go)

ka

kalmar "ka" na nufin Nuhu ne shi kadai. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-you)

gidanka

"iyalinka"

adali ne a gare ni

Wannan na nufin da cewa, Allah ya ga cewa Nuhu adali ne.

a wannan zamanin

Wannan na nufi dukkan mutane da suke a raye a waccan lokacin. AT: "a cikin dukka mutane da suke a raye yanzu"

dabba mai tsarki

Wannan dabba ne da Allah ya yaddar wa mutanen sa su ci, su kuma yi hadaya.

dabbobi marasa tsarki

Wannan dabbobi ne da Allah baya yaddar wa mutane sa su ci ba ko su yi hadaya da su.

domin adana irinsu

"domin su sami irinsu da zasu rayu" ko "domin bayan ambaliyan, dabbobi su ci gaba da rayuwa"

Genesis 7:4

kwana arba'in dare da rana

Wannan na nufin kwanaki arba'in. Ba wai kwanaki tamanin ba ne in a hada. AT: "yini da dare arba'in"

rayuwa

Wannan na nufin jiki mai rai.

Genesis 7:6

Muhimmin Bayani:

Ayoyi na 6-12 sun maimaita a karo na biyu kuma suna ba da ƙarin haske game da yadda Nuhu ya shiga cikin jirgi tare da iyalinsa da dabbobin a cikin Farawa 7: 1-5. Wannan ba sabon abu bane.

sauko bisa duniya

"faru" ko "zo a duniya"

domin ambaliyan ruwa

"domin ambaliyan ruwa da ke zuwa" ko "guje wa ambaliyan ruwan"

Genesis 7:8

Muhimmin Bayani:

Ayoyi na 6-12 sun maimaita a karo na biyu kuma suna ba da ƙarin haske game da yadda Nuhu ya shiga cikin jirgi tare da iyalinsa da dabbobin a cikin Farawa 7: 1-5. Wannan ba sabon abu bane.

dabbobi masu tsarki

Waɗannan dabbobi ne da Allah ya yaddar wa mutanen sa su ci, su kuma mika masa hadaya

dabbobi marasa tsarki

Wannan dabbobi ne da Allah baya yaddar wa mutane sa su ci ba ko su yi hadaya da su.

biyu-biyu

Dabbobin suka shiga jirgin biyu-biyu, na miji da ta mace.

Ya zama sa'ad da

Ana amfani da wannan maganar domin a ba da alama ne a cikin labarin: farin ambaliyan. Idan harshenku na da hanya yin wannan, ana iya yin amfani da shi a nan.

bayan kwanaki bakwan

"bayan kwanaki bakwai"

ambaliyan ruwan ya sauko bisa duniya

Bayyanin wannan maganar a fili shi ne, "aka fara ruwan sama" (UDB). AT: "aka fara ruwan sama, ambaliyan ruwan kuwa ya sauko bisa duniya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Genesis 7:11

Muhimmin Bayani:

Ayoyi 6-12 na maimaita sau na biyu ne da kuma ba da bayyani filla-filla game da yadda Nuhu ya shiga jirgin da iyalinsa da kuma dabbobin a cikin 7:1. Wannan ba sabon aukuwa ba ne.

a cikin shekara ta ɗari shida na rayuwar Nuhu

"A sa'd da Nuhu na shekaru 600" (UDB) (Dubi: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-ordinal)

A ranar sha bakwai ga watan biyu

Tun da shike Musa ne marubucin wannan littafi, ya yiwu yana nufin wata na biyu a kalanda Ibraniyawa, amma ba a tabbatar da wannan ba. (Dubi: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-hebrewmonths and /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-ordinal)

a wannan ranar

Wannan na nufin takamamen ranar da ruwan ta fara. Wannan maganar na nanata yadda waɗannan abubuwan suka faru nan da nan a sa'ad da lokaci ya kai.

maɓuɓɓugai na manyan zurfafa suka fashe

"ruwayen karkashin duniya suka gaggauto zuwa farfajiyar saman duniya"

manya zurfafa

Wannan na nufin teku da ake tsammanin na karkashin duniya.

tagogin sama suka buɗe

Wannan na nufin ruwan sama. Wannan na bayana sararin sama kamar rufi ne da ke hana ruwan da ke sama daga saukowa a duniya. A sa'ad da tagogi ko kofofin da sararin sama suka buɗe, sai ruwa ta sauko ta cikin su. AT: "sararin sama ta buɗe" ko "kofofin sama suka buɗe"

ruwan sama

Idan harshenku na da kalma wa ambaliyan ruwa, zai dace a nan.

Genesis 7:13

Muhimmin Bayani:

Ayoyi na 6-12 sun maimaita a karo na biyu kuma suna ba da ƙarin haske game da yadda Nuhu ya shiga cikin jirgi tare da iyalinsa da dabbobin a cikin Farawa 7: 1-5. Wannan ba sabon abu bane.

A wannan ranar

"a ainihin ranan nan." Wannan na nufin ranar da aka fara ruwan. Ayoyi 13-16 na faɗin abin da Nuhu ya yi nan da nan kafin ruwan ta fara.

dabbobin jeji ... dabbobin gida ... abubuwa masu rarrafe ... tsuntsaye

Waɗannan kungiyoyi huɗu na nuna cewa dukka dabbobi na ciki. Idan harshen ku na da wata hanyar kasa dabbobi a sashi sashi ana iya amfani da shi, ko a yi amfani da wannan kashi. dubi yadda aka juya wannan a Farawa 1:24.

abubuwa masu rarrafe

Wannan na nufin dabbobin da suke jan jiki a ƙasa kamar, jaba, ƙwaro, kaɗangare, da maciji.

da irin su

"domin kowace irin dabba ta iya haifar da irinta." Duba yadda aka fassara wannan a cikin Farawa 1:24.

Genesis 7:15

Muhimmin Bayani:

Ayoyi na 13-18 sun maimaita a karo na uku kuma sun ba da ƙarin haske game da yadda Nuhu ya shiga cikin jirgi tare da iyalinsa da dabbobi a cikin Farawa 7: 1-5. Wannan ba sabon abu bane.

biyu daga kowace nama

A nan "nama" a nufin dabbobi ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

wadda na da numfashin rai

A nan "numfashi" na nufin rai. AT: "da ke raye" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

zo wurin Nuhu

Ana iya fassarar kalmar "zo" kamar "tafi." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-go)

na dukkan halittu

A nan "halittu" na nufin dabbobi. AT: "na kowace irin dabba" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

bayan su

Cikakiyar ma'anar wannan na bayane a fili. AT: bayan suka shiga jirgin" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Genesis 7:17

Muhimmin Bayani:

Ayoyi na 13-18 sun maimaita a karo na uku kuma sun ba da ƙarin haske game da yadda Nuhu ya shiga cikin jirgi tare da iyalinsa da dabbobi a cikin Farawa 7: 1-5. Wannan ba sabon abu bane.

ruwan ya ƙaru

Wannan ya faru ne lokacin da ruwan ya cigaba da zuwa a kwanaki arba'in. "ruwan kuwa ya yi zurfi"

ya kuma ɗaga jirgin

"ya kuma sa jirgin yana lilo"

ya taso saman duniya

"sa jirgin ya taso a sama ya bar ƙasa" ko "jirgin na ta lilo a saman ruwan mai zurfi"

Genesis 7:19

Ruwan ya taso bisa duniyan sosai

"Ruwan ya mamaye duniyan gaba ɗaya"

Genesis 7:21

motsi bisa

"gantali" ko "yawo"

dukkan halittu da ke rayuwa a bisa duniya

Wannan na nufin dukka garkin dabbobi da suke yawo a ƙasa.

wanda ke da numfasa numfashin rai a hancinsu

A nan "hanci"na matsayin dukka dabbobi da mutane. AT: "kowa da kowa da ke numfashi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-synecdoche)

numfashin rai

Kalmomin nan "numfashi" da "rai" da matsayin ikon sa mutane da dabbobi su kasance a raye. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

mutu

Wannan na nufin mutuwa ta jiki.

Genesis 7:23

kowanne abu mai rai ... an shafe su

Idan ya cancanta, ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "kowane abu mai rai ... sun hallaka" ko "Ambaliyan ya hallakar da kowane abu mai rai gaba ɗaya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

dukkan su an hallakar da su

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "Allah ya hallakar da su dukka" (Dubi: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

daga duniya

"ba su nan kuma a duniya"

da dukka waɗanda suke tare da shi

"da mutanen da dabbobin da suke tare da shi"

su ka rage

"ragowa" ko "rayu" ko "rage da rai" (UDB)

ruwan ya maimaye duniyar

"Zurfin ruwan ya maimaye dukka duniya" ko " ruwan ya kasance a duniya" (UDB)