Genesis 6

Genesis 6:1

Sai ya zamana

An yi amfani da wannan maganar domin ba da alamar wani sabon sashi na labarin. Idan akwai yadda harshenku ke faɗin wannan, ana iya yanke shawaran amfani da shi anan.

suka haifi 'ya'ya mata

Wannan na iya zama mai aiki. AT: "matan suka haifi 'ya'ya mata" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

'ya'yan Allah

Masu juya wannan na iya sharihinta cewa: "Ba a bayana a fili ko wannan na nufi 'yan Adam ne ko halittu sama. Ko da wannene, duk dai Allah ne ya halicce su." Wasu sun gaskanta cewa waɗannan fadadun mala'iku ne da suka yi wa Allah tawaye, watu, mugayen ruhohi ko aljanu. Wasu na tunanin cewa ana nufin manya masu ikon mulki, wasu kuma suna tunani ana nufin da zuriyar Set ne.

Ruhuna

Anan Yahweh na magana game da kan shi da ruhunshi, wato Ruhun Allah.

jiki

Wannan na nufi da jikin mutum ne mai mutuwa.

kwanakin rayuwansu kuwa shekara 120 ne

Mai yiwuwa ana nufi 1) zaman rayuwan mutane zai ragu zuwa shekara 120. AT: "kwanakin su ba zai haye shekara 120" ko 2) cikin shekara 120 kowa za mutu. AT: "Iyakar kwanakin rayuwarsu she ni shekara 120" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)

Genesis 6:4

ƙarfafan mutane

manyan mutane, masu tsayi

Wannan ya faru ne sa'ad da

"An haifi manya manyan mutanen domin"

manyan mutanen dã can

"Wadannan ƙarfafan sune ƙarfafan da suka rayu dã can" ko "wadannan yaran ne suka girma suka zama mayaƙa da suka rayu dã can"

manyan mutanen

maza masu kwarin gwiywa da nasara cikin yaƙi

mutane masu jaruntaka

"shahararun mutane"

Genesis 6:5

son yi

"hali" ko "dabi'a"

tunanin zuciyarsu

Marubucin na maganar zuciya kamar shi ne yanki daga cikin mutum da yin tunani. Harsheku na iya amfani da wani yanki jiki da ke sa mutane tunani ba dole sai "zuciya" ba. AT: "cikin sirri tunaninsu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

abin ya ɓata masa zuciya

Marubucin na maganar zuciya kamar shi ne sashin jiki mutum da ke yin baƙin ciki.Harshenku na iya amfani da wani yanki jiki domin nuna yadda mutum ke ji. AT: "ya yi baƙin ciki kwarai da gaske game da haka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Genesis 6:7

Zan shafe mutum ... daga fuskar duniya

Marubucin na maganar yadda Allah zai hallakar da mutane kamar Allah na share datti daga kan shimfiɗaɗɗe abu. AT: "Zan hallakar da mutum ... ba za a sami ko mutum ɗaya ba a fuskar duniya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

Zan shafe mutum da na halitta

Wasu harsuna na iya bukacin a juya wannan a jimla biyu. AT: Na halicce mutum. Zan kuma shafe su" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-distinguish)

shafewa

"hallakar dukka." Ana maganar "shafewa" anan ta mumunar hanya, domin Allah na maganar hallakar da mutane domin zunuban su.

Nuhu ya sami tagomashi a idannun Yahweh

Nuhu ya sami alfarma a gaban Yahweh" ko "Yahweh ya ji daɗin Nuhu" (UDB)

a idannun Yahweh

"idannu" anan na matsayin gani ko tunani. AT: "A wurin Yahweh" ko "a zuciyar Yahweh" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Genesis 6:9

Muhimmin Bayani:

Wannan ne farkon labarin Nuhu, da ya ci gaba har zuwa sura 9.

Waɗannan sune abubuwa game da Nuhu

"Wannan shi ne labarin Nuhu"

tafiya tare da Allah

Juya wannan kamar yadda aka yi a cikin Farawa 5:21.

Nuhu ya zama mahaifin 'ya'ya uku

"Nuhu ya sami 'ya'ya uku" ko "matar Nuhu na da 'ya'ya uku"

Shem, Ham, da Yafet

Masu juya wannan na iya sharihinta cewa "ba a bisa girman 'ya'ya ne aka rubuta sunayen su ba."

Genesis 6:11

Duniya

Mai yiwuwa ana nufi 1) mutanen da suka kasance a duniya, ko 2) "ƙasan duniyar kanta." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

ta ƙazanta

An yi magana game da mutanen da suke aikata mugunta kamar abincin da ya ɓace. AT: "ya ɓace" ko "cika da mugunta" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

gaban Allah

Mai yiwuwa ana nufi 1) "a fuskar Allah" ko 2) "A fuskar Yahweh" kamar a cikin Farawa 4:16.

kuma cika da hargitsi

Marubucin na maganar mugunta kamar wani abu da ake iya zuba a cikin bokiti, duniya kuma kamar ita ce bokitin. AT: akwai kuma mugayen mutane cike a duniyan" ko "domin tana cike da mutanen da suka wa juna mugunta" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

ga shi

Kalmar "ga shi" na jawo hankalin mu ne domin sauraron abin mamaki da zai biyo.

duk mutane

Mai yiwuwa ana nufi 1) dukka 'yan Adam, ko 2) duk rayayu, mutane da dabbobi. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

sun ɓatar da hanyarsu

An yi magana game da yadda halin mutane yake kamar wani hanya. AT: "daina rayuwa yadda Allah yake so" ko "aikata hanyar mugunta" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

Genesis 6:13

duniyar na cike da mugunta a ko'ina

"dukka mutanen da suke a duniya mugaye ne"

Zan hallakar da su da duniyan

"Zan hallakar da su, har kuma da duniya" ko "Zan hallakar da su a sa'ad da ina hallakar da duniya"

jirgi

Wannan na nufin babban akwati da zai iya tafiya akan ruwa ko da bakin ƙwarya. "babban kwalekwale" ko "babban jirgin ruwa"

itace gofer

Mutane ba su san asalin ko wace irin itace ba ne wannan. "itacen da ake gina jirgin ruwa" ko "itace mai kyau"

dalaye ta da ƙaro

"yaɗa ƙaro a akai" ko "shafa kwalta akai." Ana iya bayana dalilin yin haka a fili cewa: "domin ya hana ruwa shiga" (UDB). (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

ƙaro

Wannan wani mai ne da kauri yana kuma mannewa, mutane na sa wa jirgin ruwa domin hana ruwa shiga tsakanin tazarar itacen.

kamu ko kafa

wannan ma auni ne da ya ka sa rabin mita. (Dubi: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-bdistance)

ƙafa ɗari huɗu da hamsin

"mita ɗari da talatin da takwas." Ana iya amfani da yadda Ibraniyawa suke awo a ULB ko tsarin awo a UDB, ko kuma in harshenku na da yadda ku ke auna abu kuma za iya kwatantawa da tsarin awo. Ana iya sharihinta cewa: "kafa ɗari huɗu na kusan mita ɗari da talatin da takwas." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-bdistance)

ƙafa saba'in da biyar

"mita ashirin da uku" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-bdistance)

ƙafa arba'in da biyar

"mita goma sha huɗu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-bdistance)

Genesis 6:16

rufe wa jirgin

Wannan na iya yiwuwa shimfiɗaɗɗe jinka ko mikakke. An yi haka ne domin hana ruwa shigan jirgin daga kowani hanya.

na ƙasa, na biyu, da na uku

"hawa na ƙasa, na tsakiya, da na sama" ko "hawa uku a ciki" (UDB)

bene

"kan ɗaki" ko "hawa"

Ka saurara

Allah ya faɗi haka domin ya jadada cewa zai aikata abin da so faɗa. "saurara" ko "ka ji abin da nake faɗi"

Zan kawo ambaliyan ruwa

"Ina shirin kawo ambaliyan ruwa" ko "Ina shirin in sa ambaliya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-go)

dukkan fata

Wannan na matsayin dukka rayayu, da mutane da dabbokin

mai numfashin rai

Anan "numfashi" na matsayin rai. AT: "da ke rayaye" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Genesis 6:18

kafa alƙawarina da kai

sa alƙawari tsakaninka da ni"

da kai

da Nuhu

Za ka shiga cikin jirgin

"Zaka shiga jirgi." Wasu fassarar sun ce "Za ku shiga cikin jirgi."

da kowane irin main rai kuma za ka shigar da biyu biyu a cikin jirgin

"Lalle ne ka shigar da kowane irin halitta mai rai cikin jirgin, su biyu biyu"

halitta

dabban da Allah ya halitta

Genesis 6:20

bisa ga irinsu

"na kowani iri"

abubuwa masu rarrafe a ƙasa

Wannan na nufin 'yan kananan dabbobin da suke motsi a ƙasa (UDB).

biyu biyu na kowani iri

Wannan na nufin biyu biyu a cikin kowani irin tsuntsaye da dabbobi.

domin su rayu

"domin ka rayar da su" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-ellipsis)

ga kai ... kanka ... ka

Waɗannan na nufin Nuhu ne shi kadai. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-you)

abinci da ake ci

"abincin da mutane da dabbobi suke ci"

Nuhu ya yi wannan bisa ga dukka abin da Allah ya umurce shi

Waɗannan jimla biyun na nufin abu ɗaya ne. na farkon na kara bayana na biyu da kuma jadada cewa Nuhu ya yi biyayya da Allah. Ana iya mayar da wannan jimla ta wata hanya. AT: "Nuhu kuwa ya yi dukka abin da Allah ya umurce shi ya yi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-parallelism)