Genesis 5

Genesis 5:1

Muhimmin Bayani:

Wannan shi ne farin jerin zuriyar Adamu

a cikin kamaninsa

Wannan jimlar na nufin Allah ya yi mutum ya zama kamar shi. Wannan ayan bai faɗa ko ta wace hanya ne mutane suke kama da Allah ba. Ba a nufin cewa muna kamar shi a jiki domin Allah ba shi da jiki. AT: "kasance cikin gaskiyar kamanin mu." Duba yadda aka juya "cikin kamaninmu" a Farawa 1:26. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-pronouns)

da halicce su

Ana iya sanya wannan aiki. AT: "sa'ad da ya halicce su" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

Genesis 5:3

130 ... ɗari takwas

Masu juyi na iya rubuta lamba "130" da "800" ko kuma a cikin kalma "ɗari da talatin" da "ɗari takwas." (ULB da UDB sun yi amfani da lamba in da adadin na da kalmomi da suka kai uku ko fiye; suka kuma yi amfani da kalmomi in da lamba na da kalmomi ɗaya ko biyu kawai.) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)

ya zama mahaifin ɗa

"yana da ɗa"

cikin kamaninsa da kuma siffar sa

Waɗannan kalmomi na nufin abu ɗaya ne. An yi amfani da su ne domin a tunin cewa Allah ya yi mutum cikin siffarsa. Duba yadda aka juya irin wannan maganar a Farawa 1:26.

Ya zama mahaifin 'ya'ya maza da mata

"Ya sami 'ya'ya maza da mata"

sanan ya mutu

za a yi ta maimaita wannan maganar a cikin wannan surar. Yi amfani da kalmar da aka fi sanin "mutuwa."

Adamu ya yi rayuwa har shekaru 930

Mutane na da tsawon shekaru a wancan lokacin. Yi amfani da kalmar da aka saba wa "shekaru." AT: "Iyakar rayuwa Adamu shi ne shekara 930" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)

Genesis 5:6

sai ya haifi Enosh

"Mahaifi" anan na nufin asalin mahaifinsa, ba kakanshi ba. AT: "Ya sami ɗansa Enosh."

ya zama mahaifin 'ya'ya maza da mata da yawa

"ya kuma kara samin 'ya'ya maza da mata"

Set ya rayu har shekaru 912

"Iyakar rayuwar Set shi ne shekara 912" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)

daga nan ya mutu

Za a yi ta maimaita wannan maganar a cikin wannan surar. Yi amfani da kalmar da aka fi sanin "mutuwa."

Genesis 5:9

Muhimmin Bayani:

Abubuwan da aka rubuta a cikin Farawa 5: 6-27 suna da tsari iri ɗaya. Fassara su gwargwadon bayanan da ke cikin Farawa 5: 6 (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)

Genesis 5:12

Muhimmin Bayani:

Abubuwan da aka rubuta a cikin Farawa 5: 6-27 suna da tsari iri ɗaya. Fassara su gwargwadon bayanan da ke cikin Farawa 5: 6 (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)

Genesis 5:15

Muhimmin Bayani:

Abubuwan da aka rubuta a cikin Farawa 5: 6-27 suna da tsari iri ɗaya. Fassara su gwargwadon bayanan da ke cikin Farawa 5: 6 (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)

Genesis 5:18

Muhimmin Bayani:

Abubuwan da aka rubuta a cikin Farawa 5: 6-27 suna da tsari iri ɗaya. Fassara su gwargwadon bayanan da ke cikin Farawa 5: 6 (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)

Genesis 5:21

sai ya haifi Metusela

"ya sami ɗansa Metusela"

Metusela

Wannan sunan na miji ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Enok ya yi tafiya da Allah

Yin tafiya tare da wani na bayana kusancewar dangantakar su tare. AT: "Enok ya kusance Allah" ko "Enok ya yi zama zumunta da Allah" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

Ya kuma haifi waɗansu 'ya'ya maza da mata

"Ya kara samun 'ya'ya maza da mata"

Enok ya rayu shekara 365"

"Iyakar rayuwar Enok shi ne shekara 365" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)

sanan ya tafi

Kalmar "ya" na nufin Enok. Ba ya nan a duniya kuma.

Allah kuwa ya ɗauke shi

Wannan na nufin cewa Allah ya ɗauke Enok zuwa wurin sa (Allah).

Genesis 5:25

Munimmin Bayani:

Abubuwan da aka rubuta a cikin Farawa 5: 6-27 suna da tsari iri ɗaya. Fassara su gwargwadon bayanan da ke cikin Farawa 5: 6 (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers).

Genesis 5:28

sai ya haifi ɗa

"ya sami ɗa"

Nuhu

Masu juya wannan na iya sharihinta cewa "Wannan sunan na kamar kalmar da ke nufi "hutu" a Ibraniyanci." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names).

daga aikinmu da wahalar hannuwanmu

Lamek ya maimaita wannan domin ya jadada irin wahalar aikin. AT: "daga aiki wahala da hunnuwanmu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-doublet da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-synecdoche)

Genesis 5:30

Lamek ya rayu shekara 777

"Iyakar rayuwar Lamek shi ne shekara 777" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)

Genesis 5:32

ya zama mahaifin

"ya sami 'ya'yansa maza." Wannan bai bayana mana ko an haife 'ya'yan a rana ɗaya ne ko shekaru dabam dabam.

Shem, Ham, Yafet

Ba lalle ne wai an jera sunayen 'ya'ya bisa ga haifuwarsa ba. Akwai bambancin ra'ayi game da wanene babba. A kauce wa juya wannan ta hanyar da zai nuna kamar jerin na bisa shekaran su.