Genesis 4

Genesis 4:1

Na mijin

"mutumin" ko "Adamu" (UDB)

kwana da

Harshen ku na iya samun wata hanyar faɗin wannancikin ɗa'a. Wasu tsohon juyi sun amfani da "sani." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-euphemism)

Na haifi ɗa namiji

Kalmar "miji" na bayana mutum da ya yi girma, ba ɗan jariri ko yaro ba. Idan juya wannan haka zai kawo rikicewa, ana iya juya shi haka "yaro na miji" ko "yaro" "jariri na miji" ko "ɗa."

Kayinu

Masu juya na iya sharihinta cewa "sunar Kayinu na kamar kalmar da ke nufi a 'haifar' a harshen Ibraniyanci. Hauwa ta bashi sunar Kayinu domin ta haife shi ne." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Sanan ta haifi

Bamu da cikakiyar sanin sawon lokacin da ke tsakanin haifuwar Kayinu da Habila. Suna iya kasance tagwaye ne, ko kuma an haifi Habila bayan Hauwa'u ta sake ɗaukan ciki. In zai yiwu, a amfani da maganar da ba zai ba da takamamen tsawon lokaci ba tsakaninsu.

noma

Wannan na nufin cewa yana yin duk abin da ake bukatar yi domin amfanin gona ta girma da kyau.

Genesis 4:3

Sai ya

Wannan jimlar na sa alama ce wa farkon sashi na labarin. Idan harshen ku na da yadda ku ke faɗin wannan, kuna iya yin amfani da shi anan.

zamana wata rana

Mai yiwuwa ana nufin 1) "bayan tsawon wani lokaci" ko 2) "a dai-dai lokacin"

amfanin gona

Wannan na nufin abinci da tsire-tsiren gonar ta haifar. AT: "girbi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

wasu ƙosassu

Wannan na nufi da sashin namar rago kitse ko ƙiba da ya kashe, bangare ne ma fi kyau a dabba. AT: "bangare mai ƙiba" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

karɓa

"kula" ko "ya gamsu da"

ya husata ƙwarai

Wasu harsuna na da yadda suke bayana wannan kamar "zafi/ƙona" ko "ƙonewa da hushi."

tsikar jikinsa ta tashi

Wannan na bayana yadda fuskar sa ya nuna hushinsa da kishi. Wasu harsuna na da yadda suke bayana fuskar wanda ya ke hushi. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

Genesis 4:6

Me ya sa ka husata, kuma ya sa har tsikar jikinka ta tashi

Allah ya yi amfani da wannan tambayoyi domin ya nuna wa Kayinu cewa ba dai-dai ba ne ya husata ya kuma sa tsikar jikinsa ta tashi. Mai yiwuwa kuma suna ba wa Kayinu zarafi ne ya furta cewa ya yi laifi ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

In ka ... da ba za a karɓe ka ba?

Allah ya yi amfani da wannan tambaya domin ya tunashe Kayinu game da abin da yakamata a ce ya sani. AT: "Ka san cewa in da ka aikata abin da ya ke daidai, ai da na karɓe ka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

Amma idan ba ka ... tilas ne ka mallake shi

Allah na magana game da zunubi kamar wani mutum ne. AT: "Amma idan ba ka bidar aikata abin da ke dai-dai, to za ka bida ka aikata zunubi, kuma za ka yi abin da ke na zunubi. Tilas ne ka ki yin biyayya da shi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-personification)

Zunubi na fako ... ya mallake ka

Ana magana game da zunubi anan kamar wani mugun dabba jeji ne da fakon kai hari wa Kayinu. AT: "Za ka cika da hushi har za ka gagara kin aikata zunubi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

zunubi

Harsuna da ba su da suna da ke bayana "zunubi" na iya juya wannan kamar "sha'awar aikata zunubi" ko "mumunar abubuwan da ka ke so ka yi."

tilas ne ka mallake shi

Yahweh na magana game da sha'awar aikata zunubi da Kayinu ke yi kamar wani mutum ne da Kayinu zai yi mulkin shi. AT: "dole ka mallake shi domin kar ka yi zunubi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-personification)

Genesis 4:8

Kayinu ya ce wa ɗan'uwansa Habila

Wasu harsuna na iya bukatar takamamen bayanin abin da Kayinu ya ce wa ɗan'uwansa game da tafiyarsu ciki saura. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

ɗan'uwa

Habila ƙanin Kayinu ne. Wasu harsuna za su bukaci amfani da kalmar "ƙani." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

ya tasar wa

"kai hari" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

Ina Habila ɗan'uwanka

Allah ya san cewa Kayinu ka kashi Habila, amma ya tambayeshi domin ya amsa. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

Ni makiyayin ɗan'uwana ne?

Kayinu ya yi amfani da tambaya domin ya guje wa faɗin gaskiya. AT: "Ni ba makiyayin ɗan'uwana ba ne!" ko "Aikina ba kiwon ɗan'uwana bane!" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

Genesis 4:10

Me ke nan ka yi?

Allah ya yi amfani tambaya domin ya tsauta wa Kayinu. AT: "Ka aikata mumunar abu!" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

Muryar jinin ɗan'uwanka tana yi mini kuka

Jinin Habila na matsayin mutuwar sa, kamar mutum ne na kiran Allah ya horar da Kayinu. AT: "Jinin ɗan'uwanka na kira kamar mutum ne da ya ke so in horar da mutumin da ya kashe shi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Yanzu fa, kai la'ananne ne daga cikin ƙasar

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "Ina la'ance ka, ba za ka iya nomar abinci daga ƙasa ba" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

da ta buɗe baki ta karɓi jinin ɗan'uwanka

Allah na magana game da ƙasar kamar wani mutum ne da zai iya shan jinin Habila. AT: "da ke jike da jinin ɗan'uwanka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-personification)

daga hannunka

Allah na magana game da hannun Kayinu kamar hannun ya zuba jinin Habila a "bakin" ƙasa. AT: "da ya zub a sa'ad da ka kashe shi" ko "daga gare ka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-synecdoche)

nome

Wannan na nufin yin duk abin da ake bukata domin amfanin gona ta girma da kyau.

ba za ta ƙara ba ka cikakken amfaninta

An yi maganar ƙasa kamar mutum ne da karfinsa na kasawa. AT: "ƙasar ba za ta ba ka abinci ba" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-personification)

Mai yawo barkatai mai kai da kawowa kuma

Ana iya haɗa waɗannan kalmomin tare. AT: "Mai yawo barkatai mara gida" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-hendiadys)

Genesis 4:13

zan ɓoye daga fuskarka

Kalmar "fuskarka" na nuna gaban Allah. AT: "ba zan iya magana da kai ba" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

za a rama masa har sau bakwai

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "zan ɗau ramako akan shi sau bakwai" ko "Zan hukunta mutumin sau bakwai fiye da hukuncin ka" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

ba zai kai masa hari ba

"ba zai kashe Kayinu ba"

Genesis 4:16

ya tafi daga fuskar Yahweh

Koda yake Yahweh yana ko'ina, wannan maganar na nuna kamar cewa Kayinu ya tafi wani wuri mai nisa. AT: "tafi daga inda Yahweh yayi masa magana" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

Nod

Mai juya wannan na iya sharihinta cewa "Kalmar Nod na nufin "yawo barkatai."

kwana da

Harshen ku na iya samun wata hanyar faɗin wannancikin ɗa'a. Wasu tsohon juyi sun amfani da "sani." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-euphemism)

Ya gina birni

"Kayinu ya gina birni"

Genesis 4:18

Ga Enok sai aka haifa masa Irad

Wannan na nuna cewa Enok ya girma kuma ya aure wata mace. AT: "Enok ya girma kuma ya yi aure, sanan ya haifi ɗa wanda ya kuma kira shi Irad" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Irad ya zama mahaifin Mehuyawel

"Irad ya haifi ɗa ya kuma kira shi Mehuyawel" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Ada ... Zulla

Waɗannan sunayen mata ne (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Genesis 4:20

Shi ne mahaifin masu zama a cikin rumfuna

Mai yiwuwa ana nufi 1) "Shi ya zama na farko da ke zama a cikin rumfuna" ko 2) " Shi da zuriyarsa sun zauna a cikin rumfuna."

zama a cikin rumfuna waɗanda ke da dabbobi

mutanen da suke zama cikin alfarwa suna kuma kiwon dabbobi

Shi ne mahaifin makaɗan molo da algaita

Mai yiwuwa ana nufi 1) "shi ne ya zama na farkon zama makaɗin molo da algaita" ko 2) "Shi da zuriyarsa ne suka zama makaɗan molo da algaita."

Tubal-Kayinu, shi ne asalin maƙeran tagulla da ƙarfe

"Tubal-Kayinu. Shi ne maƙeran tagulla da kayayyakin ƙarfe" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

ƙarfe

Wannan wani ƙarfe ne mai karfi wanda ake amfani wajen yin kayayyakin ƙarfe, da makamai.

Genesis 4:23

saurari murya na ... ji abin da nake faɗi

Lamek ya faɗa wannan sau biyu domin ya jadada abin da ya ce. Muryar na nufin shi gaba ɗaya. AT: "saurare ni a hankali" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-parallelism da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

mutum ... saurayi

Lamek ya kashe mutum ɗaya. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-doublet)

ya yi mini rauni ... ya buge ni

"domin ya yi mini rauni ... ya kuma buge ni" ko "domin ya ji mini ciwo" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-doublet)

Idan an rama wa Kayinu sau bakwai, hakika na Lamek

Lamek ya san cewa Allah zai rama wa Kayinu sau bakwai. AT: "Da shike Allah zai hukunta sau bakwai duk wanda ya kashe Kayinu, Lamek" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

hakika na Lamek sau saba'in da bakwai za a rama

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "Allah zai hukunta sau saba'in da bakwai, duk wanda ya kashe ni" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

saba'in da bakwai

"77" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)

Genesis 4:25

kwana da

Harshen ku na iya samun wata hanyar faɗin wannancikin ɗa'a. Wasu tsohon juyi sun amfani da "sani." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-euphemism)

ta kuwa ce, "Allah ya kara bani wani ɗan

Wannan shi ne dalilin da ya sa ta kira sunansa Set. AT: "ta kuma bayana cewa "Allah ya sake ba ni ɗa." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Set

Masu juya na iya sharihinta cewa "Wannan sunan na kamar kalmar da ke nufi "an bayar" a harshen Ibraniyanci." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Aka haifa wa Set ɗa

Ana iya bayyana wannan a bayyane. AT: "matar Set kuwa ta haifar masa ɗa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

kira bisa sunan Yahweh

A wannan lokacin ne mutane suka fara kiran Allah da sunan Yahweh. Ana iya sa wannan a sarari cewa. AT: "yi wa Allah sujada ta wurin kiran sa Yahweh" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)