Genesis 3

Genesis 3:1

Yanzu

Marubucin na fara wani sabon sashin labari.

mafi wayo

"fi wayo" (UDB) ko "mai kaifin baki domin ya sanu abun ya ke so, ta wurin faɗin karya"

Ko Allah ya ce, 'Ku ... gona'?

Macijin na wayancewa yana mamaki wai Allah ya ba da wannan doka. Ana iya fassara wannan tambayar ta lafazi a matsayin sanarwa. AT: "Ina makaki wai Allah ya ce, "Ku ... gona'" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

Ba za ku ci ba

Kalmar "ku" na nufin namijin da ta macen. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-you)

muna iya ci

"muna da izinin ci" ko "an yarda mana mu ci"

Ba za ku ... ko za ku ... za ku mutu

Kalmar "ku" na nufin namijin da ta macen. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-you)

Ba za ku iya ci ba

"Ba za ku ci ba" ko "kada ku ci"

kuma ba za ku taɓa shi ba

"ba za ku kuma taɓa shi ba" ko "kuma kada ku taɓa"

Genesis 3:4

Ku ... ku ... na ku ... ku

Wannan na nufin namijin da ta mace su biyu. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-you)

idanunku za su buɗe

"idanunku zai buɗe." Wannan karin magana na nufin cewa "za ku san abubuwa" ko "za ku fahimci sabobin abubuwa." Ana iya bayana wannan a fili. AT: "Zai kasance kamar cewa idanunku sun buɗe" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

sanin nagarta da mugunta

Anan "nagarta da mugunta" karin magana ne da ke nufi sanin farko da iyakar abu da komai da ke cikin abun. Dubi yadda aka juya "sanin nagarta da mugunta" a Farawa 2:9. AT: "sanin komai, na nagari da na mugunta" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-merism)

na da kyau ga idanu

"itacen na da kyau a duban idanu" ko "na da sha'awan kallo" ko "na da kyau ƙwarai" (UDB)

kuma da cewa abun marmari ne domin ba da hikima

"ta kuma so 'ya'yan itacen domin ya na iya ba wa mutum hikima" ko "ta kuma so 'ya'yan domin 'ya'yan na iya sa ta fahimci abin da ke dai-dai da mumunar abu kamar yadda Allah ya sani"

Genesis 3:7

sai idanunsu biyun suka buɗe

"Sai idanunsu suka buɗe" ko "Suka sani" ko "Sun fahimta." Dubi yadda aka juya "idanunku za su buɗe" a cikin Farawa 3:4.

ɗinka

"lazimta" ko "ƙulle"

ganyayen ɓaure

Idan mutane ba su san kamanin ganyayen ɓaure ba, ana iya juya wannan haka "manyan ganyayen daga itacen ɓaure" ko kuwa "manyan ganyaye." kawai

suka yi wa kansu sutura

Sun yi haka domin su na kunya. Ana iya mayar da wannan magana a cikin sauki, idan ana bukata yin haka kamar a cikin UDB. AT: "suka kuma yi wa kansu sutura domin suna kunya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

a cikin sanyin ranar

"a lokacin iska mai sanyi na ranar"

daga fuskar Allah Yahweh

"daga fuskar Allah Yahweh" ko "don kada Allah Yahweh ya iya ganin su" (UDB) ko "daga Allah Yahweh"

Genesis 3:9

Ina ka ke?

"Me ya sa ka na ɓuya daga gare ni?" (UDB). Allah ya san inda mutumin ya ke. Da mutumin ya amsa, ba ya faɗa inda ya ke ba daidai dalilin da da ya sa ya ɓuya.

ka

A aya 9 da 11, Allah na magana da mutumin ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-you)

Na ji ka

"Na ji motsin zuwar ka"

Wa ya ce ma ka

Allah ya san amsar wannan tambayan. Ya yi tambayan domin ya tilasta Adamu ya furta rashin biyayyar sa ga Allah. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

ka ci ... daga?

Kuma, Allah ya san cewa haka ya faru. A juya wannan ta hanyar da zai nuna cewa Allah na dora wa Adamu laifin rashin biyayya. AT: "haƙika ka ci ... daga." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

Genesis 3:12

Mene ne wannan da kika yi?

Allah ya riga ya san abin da macen ta aikata. Da yake tambayan nan, yana ba ta damar ta faɗa masa da kuma yana nuna rashin jin dadi abin da ta aikata. Harsuna da yawa na morar tambaya domin tsautawa. In akwai yadda za a nuna rashi jin dadin a yi amfani da shi. Ana iya fassara wannan tambayar ta lafazi a matsayin sanarwa. AT: "Kin aikata mummunar abu." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

Genesis 3:14

kai kaɗai la'ana za ta bi

"kai kaɗai aka la'anta." Kalman "la'anta" ya fito a farkon maganar a harshen Ibraniyanci domin jadada bambancin albarkan da Allah ya sa wa dabbobin da wannan la'anta da ke akan macijin. Haka aka "saba la'anta", ko yadda ake faɗin kalmar la'antawa. Ta ambacin wannan la'ananci, Allah ya sa haka ya faru.

dukkan dabbobin gida da na jeji

"duk dabbobin da ake kiwo a gida da na jeji"

rubda ciki za ka yi tafiya

"da ciki za ka dinga tafiya a ƙasa." Maganar "da cikin ka" ya zo a farkon maganar domin a jadada bambanci tsakanin yadda sauran dabbobi za su yi tafiya da kafafunsu amma macijin kuwa rub da ciki zai yi. Wannan na yadda a ka saba la'anta ne.

turɓaya za ka ci

"ƙura za ka ci." "Turɓaya ne" ya zo a farkon maganar domin nuna bambancin tsire-tsire da sauran dabbobi za su ci da kuma datti da ƙurar da ke ƙasa da macijin zai ci. Wannan ma na yadda aka saba la'anan ne.

ƙiyayya tsakaninka da matar

Wannan na nufin cewa macijin da macen za su zama abokan gãba.

zuriya

Kalmar "zuriya" na nufin abin da na miji ya ke sa a cikin mace domin yaro ya girma a cikin ta. yadda kalmar yake, ya na iya nufin mutum ɗaya ne ko fiye. A nemi kalmar da zai iya bayana zuriya na iya zama ɗaya ko fiye ɗaya.

shi zai ƙuje ... diddigensa

Kalmar "shi" da "sa" na nufin zuriyar matar. Idan kalmar "zuriya" na jam'i ne, ana iya juya shi haka "za su ƙuje ... diddigensu"; in ya kasance haka, ana iya sharihinta cewa "su" wakilin suna ne da nufin mutum ɗaya. (Dubai: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-pronouns)

ƙuje

"murkushe" ko "boga" ko "farmaki"

Genesis 3:16

Zan ninka shan wuyarki sosai

"Zan ƙara zafin nuƙudarki" ko "Zan sa zafin naƙudarki ya zama da tsanani"

a samun 'ya'ya

"ta haifan 'ya'ya" ko "a sa'ad da ki ke haifan 'ya'ya" (UDB)

muradinki zai koma ga mijinki

"za ki kasance da matukar sha'awa ga mijinki." Mai yiwuwa ana nufi 1) "Za ki bukaci dayawa a gare mijinki" ko 2) "Za ki so ki sarrafa mijinki"

zai kuwa mallake ki

"zai kasance uban gidan ki" ko "zai yi sarrafa ki"

Genesis 3:17

Adamu

Adamu da "na miji" na da kalma ɗaya ne a harshen Ibraniyanci. Wasu juya na amfani da "Adamu" wasu kuma "na mijin." Ana iya amfani da kowane domin ana nufin mutum ɗaya ne.

ka kasa kunne ga muryar matarka

Wannan ƙarin magana ne. AT: "ka yi biyayya da abin da matar ka ta faɗa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

ka ci daga itacen

Ana iya faɗin abin da suka ci. AT: "ci daga 'ya'yan itacen" ko "ci daga wasu 'ya'yan itace" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

a la'antar da ƙasa

Kalmar "la'anta" na zuwa a farkon maganar domin a jadada cewa, ƙasar da Allah ya ce na kyau a baya, na karkashin la'ana yanzu. AT: "Ina la'antar ƙasa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

ta wahalar aiki

"ta wurin aiki tuƙuru"

za ka ci daga cikinta

Kalmar "ta" na nufin ƙasa ne, kuma yana bayana sashin amfanin gona da ke girma a cikin ƙasa da mutane ke ci. AT: "za ka ci daga abin da ya girma a cikinta" (Dubi: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

tsire-tsiren jeji

Mai yiwuwa ana nufi 1) "tsire-tsiren da ka ke nomar ta a gonar ka" ko 2) "tsire-tsiren da ke girma a filin jeji."

Da zuffar fuskar ka

"Za ka yi zuffa da aiki tuƙuru"

za ka ci gurasa

Anan "gurasa" na nufi kowani irin abinci. AT: "za ka ci abinci" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-synecdoche)

har ka koma ƙasa

"har mutuwarka, a kuma sa jikin ka a cikin ƙasa." Wasu al'adu na sa jikin wanda suka mutu a rami a cikin ƙasa. Wahalar aikin mutum ba ta karewa har sai lokacin mutuwarsa da biso.

gama turɓaya ka ke, kuma turɓaya za ka koma

"Da turɓaya ne na yi ka, haka kuma jikin ka zai zama turɓaya."

Genesis 3:20

Mutumin

Wasu juyi sun ce "Adamu."

kira matarsa suna Hauwa

"ba wa matarsa suna Hauwa" ko "sa wa matarsa suna Hauwa" (UDB)

Hauwa

Masu juya wannan na iya sharihinta cewa "sunar Hauwa na kamar kalmar Ibraniyanci da ki nufi 'rayuwa.'"

dukka rayayyu

Kalmar "rayayyu" na nufin mutane ne. AT: "dukka mutanen" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-nominaladj)

tufafi na fata

"kayansawa daga fatar dabbobi"

Genesis 3:22

Mutumin

Mai yiwuwa ana nufi 1) Allah magana game da mutum ɗaya ne, na mijin, ko 2) Allah na magana game da mutane dukka, wato na miji da matan shi. Ko da mutum ɗaya ne Allah ke magana da, abin da ya faɗa ya shafe su dukka biyu.

kamar ɗayan mu

"kamar mu." Wakilin sunan nan "mu" jam'i ce. Duba yadda aka juya "Bari mu yi" a Farawa 1:26.

sanin nagarta da mugunta

Anan "nagarta da mugunta" ƙarin magana ne da ke nufin iyakar farko da karshen kowani abu da duk abin da ke tsakani. Dubi yadda aka juya "sanin nagarta da mugunta" a cikin Farawa 2:9. AT: "sanin komai, da nagarta da mugunta" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-merism)

kada a yarda mi shi

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "ba zan yarda mi shi ba" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

itacen rai

"itace da ke ba da rai."

ƙasar, inda aka ɗauko shi

"ƙura, dommin daga ƙura ya fito." Wannan baya nufin wani takamamen ƙasa ne da Allah a ɗauko mutumin.

domin haka Allah ya fisshe shi daga cikin gonar

"Allah ya tilasta mutumin ya bar cikin gonar." Wannan na bayana abin da ya faru a Farawa 3:22, inda ya ce " Allah Yahweh ya kori mutumin daga gonar Aidan." Ba wai Allah ya kori mutumin na biyu ba ne.

ya nome

Wannan na nufin yin aikin da a ake bukata domin amfanin gona ta girma da kyau. juya wannan kamar a 2:4.

domin tsare hanya zuwa itacen rai

"domin ya tsayad da mutane daga zuwa itacen rai"

takobi mai harshen wuta

Mai yiwuwa ana nufi 1) takobi da ke da harshen wuta akai, ko 2) harshen wuta da kamar siffar takobi. harsuna da ba su da takobi na iya amfani da makami kamar mashi.