"sararin"
"da dukkan abubuwa da yawa masu rai da ke cikin su" ko "da duk taron rayayyu da ke cikin su"
Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "Allah ya gama halittar su" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)
Allah ba ya yi kowani aiki ba a kwana na bakwai
Wannan karin magana ne. AT: "ya gama" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)
"ba ya yi aiki ba a wannan ranar"
Mai yiwuwa ana nufi 1) Allah ya sarrafe kwana na bakwai da sakamako mai kyau, ko 2) Allah ya ce kwana na bakwan na da kyau.
"ya kuma keɓe shi" ko "ya kuma kira ranar na shi"
"a cikinsa bai yi aiki ba"
Sauran Farawa sura biyun na magana game da yadda Allah ya halicci mutane a cikin kwana na shida.
"Wannan shi ne tarihin sama da duniya" ko "Wannan shi ne labari game da sama da duniya." Mai yiwuwa ana nufi 1) wannan taƙaitaciyar labari ne da aka bayar a Farawa 1:1-2:3 ko 2) Na gabatar da abin da ke faruwa a Farawa 2. in mai yiwuwa ne, juya a hanyar da mutane za su fahimce dukka.
"Allah Yahweh ya halicce su." A sura 1 marubucin na ambatar Allah da sunar sa "Allah", amma a sura 2 yana kiran shi "Allah Yahweh."
"a sa'ad da Allah Yahweh ya halicci." Kalmar "rana" na nufin iyakar lokacin halitta, ba wani kwana ɗaya ba.
Wannan shi ne sunar da Allah ya bayyanar wa mutanen sa a cikin Tsohon Alkawari. Duba translationWord domin sanin yadda aka juya kalmar Yahweh.
ba tsire-tsiren da ke girma a jeji domin dabbbobi su ci
ba shuka masu ganyayyeki kamar kayan lambu da mutane da dabbobi za su iya ci
a yi duk abin da ake bukatan yi domin shuka ta yi girma da kyau
Mai yiwuwa ana nufi 1) wani abu kamar hazo, ko 2) bubbugowar ruwa daga rafi.
duniya dukka
"shafi" ko "kera" ko "halicce"
"ɗan adam mai rai ... ɗan adam" ko " mutum ... mutumin" ba lalle na miji ba
"hancinsa"
"numfashin da ke sa abubuwa su rayu." Anan "rai" na nufin kasance rayyaye a duniya.
Wannan na iya zama gonar itatuwa masu 'ya'ya ko wani wuri da ke da kowani irin itatuwa.
"a gabas"
"itace da ke ba mutane rai"
Wannan na nufi "rai madawwami" ko rai mara iyaka.
"itacen da ke ba mutane ikon fahimtar nagarta da mugunta" ko "itace da ke sa mutune su san abubuwa masu kyau da mugayen abubuwa idan an ci 'ya'yan ta"
Wannan karin magana ne da ke nufi sanin farko da iyakar abu da komai da cikin abun. AT: "komai, na nagari da mugunta" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-merism)
"a tsakiyar gonar." Mai yiwuwa Itatuwa biyun ba a tsakiyar gonar suke ba.
Gonar na Aidan. Kogin ya ci gaba da malalowa har wa jen Aidan. AT: "Wani kogi ya malalo a cikin Aidan ya shayar da gonar."
Anan kadai ne aka ambaci wannan kogin a Littafi Mai Tsarki. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names).
"iyakar ƙasar da a kira Hawila." Yana nan ne a wani wuri a Hamadar Larabawa. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names).
Wannan maganar na ba da bayani ne gama da Hawila. Wasu harsuna na iya sa shi a wani jimla dabam. AT: "Akwai zinariya a Hawila" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-distinguish)
Kalmar "akwai" na farkon jimlar domin jadada maganar. AT: "Anan ne kuma mutane ke iya samun duwatsu masu daraja"
Wani abu ne mai da ƙamshi da ke fitowa a wani irin itace. Yana mannewa kuma yana iya konewa. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-unknown)
"duwatsu masu daraja." Wani wani irn dutse ne mai kyau. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-unknown)
Anan kadai ne aka ambaci wannan kogin a Littafi Mai Tsarki. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)
Kogin bai rufe ƙasar gaba daya ba, amma ya kewaye wurare dayawa a ƙasar.
"iyakar ƙasar da ake kira Kush"
"wanda yake malala a cikin ƙasar da ke gabashin birnin Assurh" KoginTigiris na malala daga arewa zuwa kudu. Kalmomin "wanda ke malala gabashin Asshur" na bayana inda Kogin Tigiris ya ke. wasu harsuna za su wannan a wani jimla dabam. AT: "kuma yana malala gabashin Asshur" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-distinguish)
"gonar da ke a cikin Aidan"
"ya nome ta." Wannan na nufin cewa ya yi duk abun da ake bukata domin tsire-tsiren su yi girma da kyau.
ya kiyaye gonar daga kowace muguwar abu da ke so ya faru a cikin ta
" 'ya'yan kowance itace da ke a gonar"
Wannan wakilin suna ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-you)
A wasu harsu a akan fara irin wannan maganar da ambacin wanda ba a so mutum ya aikata kamin wanda zai iya aikatawa.
"na iya ci ba tare da hani ba"
itacen da ke ba mutane ikon fahimtar nagarta da mugunta" ko "itace da ke sa mutune su san abubuwa masu kyau da mugayen abubuwa idan an ci 'ya'yan ta."
"ba zan ba ka izinin ci ba" (UDB) ko "ba za ka ci ba"
"Zan yi masa mai taimakon da ke dai-dai masa"
Maganganu nan "ta filin ƙasa" da kuma "na sararin sama" na faɗin inda ake samun dabbobi da tsuntsu ne. AT: "dukka irin dabbobi da tsuntsaye."
"dukka dabbobin da mutane ke kiwon su"
Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: " babu abokin hira da ya dace da shi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)
"sa mutumin yin barci mai zurfi." ba a iya ta da mai zurfi barci a cikin sauki ba.
"daga haƙarƙarin ... ya kera mace." Haƙarƙarin ne abun da Allah ya yi macen da shi.
"A karshe dai, ƙasusuwan wannan kamar nawa ne, naman ta kuwa kamar nama na." Bayan neman abokin zama daga dabbobin bai kuma samu ba, yanzu dai a karshe ya ga wani mai kama da shi kuma na iya zama abokinsa. Mai yiwuwa mutumin na nuna gamsuwarsa da murna.
Wannan na nufi jikin mutum kamar fata da tsoka.
Mai juya wannan na iya sharihinta cewa "kalmar "mace' na kusa da kalmar 'miji' a Ibraniyanci.
Sauran magana daga marubucin littafin ne ba mutumin da aka halitta ba.
"Don wannan ne"
"mutum zai rabu da gidan mahaifinsa da mahaifiyarsa." Wannan maganar ga maza ne dukka. Ba wa wani takamamen mutum a wani lokaci ba.
Wannan ƙarin maganar na bayana cewa jikinsu da ke tare a jima'i na zama jiki ɗaya ne. AT: "jikinsu biyun zasu zama ɗaya" (Dubi: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)
Kalmar "su" na nufin na mijin da ta macen da Allah ya hilitta.
"ba tare da sa tufafi ba"
"ba su jin kunyar kasancewa a tsiraice" (UDB)